Ba gaskiya bane, Ban sha komai ba, Matukin jirgin saman Air Peace ya karyata binciken da yace ya sha miyagun Qayoyi da Giyya a lokacin da yake tuka mutane 103
Matukin jirgin saman air peeace ya musanta sakamakon da aka fitar wanda yace ya sha giya da miyagun kwayoyi a lokacin da jirgin saman da yake tukawa me dauke da mutane 103 yayi hadari.
Matukin a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV yace shi bai sha komai ba.
Yace sun san irin kudade masu yawa da suka kashe a makarantar horas da tukin jirgin sama, babu yadda za'a yi a rana daya su batawa kansu suna.
Yace Asibitin da aka kai jininsu aka yi gwajin hukumar jirgin sama bata amince da ingancinsa ba.
https://twitter.com/ARISEtv/status/1966654676750811647?t=65NG7VksvJlfKm8zwcr29Q&s=19
Jirgin dai yayi hadari ne ya sauka daga kan titinsa a filin jirgib sama na fatakwal duk da yake dai ba'a samu asarar rayuka ba








