Tuesday, December 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ku daina sauraren karairayin kafafen sada zumunta ku goyi bayan shugaba Tinubu>>Wike ya gayawa Mutanen Abuja

Ku daina sauraren karairayin kafafen sada zumunta ku goyi bayan shugaba Tinubu>>Wike ya gayawa Mutanen Abuja

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya nemi mutanen Abuja da su daina sauraren karairayin da ake musu a kafafen sada zumunta. Hakanan yace su daina sauraren 'yan Adawa wadanda kansu ba a hade yake ba. Ya bayyana hakane a wajan kaddamar da wani titi a Apo. Inda yace a baya karairayi kawai ake musu amma a yanzu gashi ana fada da cikawa. Wike ya jawo hankalinsu da su goyi bayan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dan shine ya musu aiki na zahiri.
Da Duminsa: Bayan da aka yi Allah wadai da lamarin, Ma’aikatar noma ta Najeriya ta dakatar da Shirin yin Azumi dan neman sa’ar wadatar abinci a Najeriya

Da Duminsa: Bayan da aka yi Allah wadai da lamarin, Ma’aikatar noma ta Najeriya ta dakatar da Shirin yin Azumi dan neman sa’ar wadatar abinci a Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni daga ma'aikatar noma ta Najeriya ta sanar da dakatar da shirinta na tursasa ma'aikatan ta yin azumin kwanaki 3 dan neman sa'a wajan wadata Najeriya da abinci. Takardar umarnin daukar azumin ta bayyana inda aka ga cewa an bukaci ma'aikatan hukumar da su tashi da azumi nan da ranar Litinin. Saidai bayan da Allah wadai yayi yawa, ma'aikatar ta noma ta dakatar da wannan shiri inda tace sai abinda hali yayi .
Kalli Hotuna: Ana zargin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka Agogon Naira Miliyan dari da Tamanin

Kalli Hotuna: Ana zargin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka Agogon Naira Miliyan dari da Tamanin

Duk Labarai
Ana zargin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da saka Agogon Naira Miliyan 180,000,000. An ga Agogon a hannun shugaban kasar ne a yayin da kwanin Wsan Chess ya kai masa ziyara. An samu wasu suka yi binciken Kwakwaf dan gano kudin Agogon Inda aka ga ana sayar da ita akan dala $114,495 kwatankwacin sama da Naira Miliyan 180 kenan. Wasu dai na ganin ba lallai shugaban kasar ne ya siyasa da kansa ba watakila bashi aka yi kyauta.
Kalli Bidiyon:Sheikh Lawan Triumph yayi Allah ya isa ga abinda tawagar Sarki Sanusi II suka yi a kofar gidan Aminu Dogo Dantata

Kalli Bidiyon:Sheikh Lawan Triumph yayi Allah ya isa ga abinda tawagar Sarki Sanusi II suka yi a kofar gidan Aminu Dogo Dantata

Duk Labarai
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Lawan Triumph yayi Allah ya isa kan abinda 'yan Bindiga na tawagar hawan Sallahn Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II suka yi a kofar gidan Aminu Dantata. An zargi 'yan bindigar da buga Bindiga a kofar gidan Aminu Dogo Dantata inda aka ji suna cewa ku buga mai ya mutu. Saidai wasu na ganin wannan ba wani Abu bane saboda al'adace wadda kuma ko lokacin tsohon sarki ana yinta. https://www.tiktok.com/@arewaupdatesng/video/7515560323517041925?_t=ZM-8xCFtxmLMEH&_r=1 Sheikh Lawan yayi Allah ya Isa ga wadanda suka saka 'yan Bindigar suka yi wannan abu wanda ya kira da rashin da'a.
Kalli Bidiyo yanda wata baturiya ta lalata Talabijin dinta saboda bata ji dadin harin da Israyla ta kaiwa kasar Ìràn ba

Kalli Bidiyo yanda wata baturiya ta lalata Talabijin dinta saboda bata ji dadin harin da Israyla ta kaiwa kasar Ìràn ba

Duk Labarai
Wata baturiya ta lalata Talabijin dinta saboda bata ji dadin harin da kasar Israyla ta kaiwa kasar Ìràn ba. A wani Bidiyo data wallafa, An ganta tana jefawa Talabijin dinta abubuwa har Talabijin din ta fashe. https://www.tiktok.com/@mommasam/video/7515277840095448362?_t=ZM-8xCEFCwk1Ek&_r=1 A jiya ne dai kasar Israyla ta Afkawa Iran da yaki bisa kokarin hanata mallakar makamin kare dangi wanda tace barazanane ga kasantuwarta. Saidai Iran ta mayar da martani.
Ma’aikatar Noma tace ma’aikatanta su dauki azumin kwana 3 dan yin Addu’a a samu wadataccen Abinci a Najeriya

Ma’aikatar Noma tace ma’aikatanta su dauki azumin kwana 3 dan yin Addu’a a samu wadataccen Abinci a Najeriya

Duk Labarai
Ma'aikatar Noma ta Najeriya ta yi kiran da a dauki Azumi a tsakanin ma'aikatan hukumar dan neman Allah ya wadata kasa da Abinci. Sanarwar hakan na kunshene a cikin sanarwa wadda wakilin ma'aikatar, Adedayo Modupe ya fitar inda yace ana bukatar addu'ar domin taimakawa kokarin Gwamnati na wadata kasa da abinci. Yace ana tsammanin duka ma'aikatan hukumar zasu fara wannan Azumi dan neman taimakon Allah. Sanarwar ta bukaci kowane ma'aikacin hukumar ya dauki azumi ranar Litinin ya je dashi wajan aiki.
Hukumar kula da birnin tarayya Abuja zata sake gina sabuwar Hukumar zabe me zaman kanta INEC, ‘yan Najeriya da yawa sun ce wata hanyar bata kudi ce

Hukumar kula da birnin tarayya Abuja zata sake gina sabuwar Hukumar zabe me zaman kanta INEC, ‘yan Najeriya da yawa sun ce wata hanyar bata kudi ce

Duk Labarai
Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, FCTA ta sanar da shirin sake gina sabuwar Hukumar zabe me zaman kanta, INEC. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne zai kaddamar da fara ginin na INEC wanda na daga cikin bikin cikarsa shekara 2 akan mulki. Ba dai a bayyana ainahin nawaye kudin da za'a yi amfani dasu wajan sake gina sabuwar hukumar INEC din ba amma an ce zasu kai Biliyoyin Naira. Da aka binciki cewa, me yasa FCTA zata gina INEC saboda lura da INEC hukuma ce me zaman kanta, wata majiya daga hukumar ta FCTA tace ai sune suka gina hukumomi da yawa a Abuja hadda ma majalisar tarayya. Sannan sake ginin bashi da wata alaka da kokarin nuna iko da hukumar ta INEC.
Naira Biliyan N39bn d aka kashe wajan gyaran babban dakin taro na Abuja wanda aka sakawa sunan shugaban Tinubu, kudin zasu iya gina Asibitoci 312 da Ajujuwan makarantu 1,200

Naira Biliyan N39bn d aka kashe wajan gyaran babban dakin taro na Abuja wanda aka sakawa sunan shugaban Tinubu, kudin zasu iya gina Asibitoci 312 da Ajujuwan makarantu 1,200

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya, Abuja ya gyara babban dakin taro na kasa da kasa dake Abuja wanda ya sakawa sunan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Lamarin ya jawo cece-kuce inda masu suka ke cewa, a zamanin tsohon shugaban kasa janar IBB ne aka gina dakin kuma sunansa ya kamata a saka. Saidai wani abu da ya kara daukar hankula shine maganar kudin da aka kashe wajan gyaran inda Ministan yace sun kashe Naira Biliyan 39 wajan yin wannan gyara. Masu bin diddigi sun ce Naira Biliyan 39 dinnan zata iya gina Asibitoci 312 da Ajujuwan Karatu 1,200. Hakan dai na nuna rashin muhimmanci da shuwagabanni basu baia bukatar talakawa, ko kuma ace rashin saka kudi inda aka fi bukatarsu.
An zargi cewa An fifota baiwa Adam A. Zango kulawa fiye da sauran wadanda suka yi Hadari tare a Asibiti inda aka bar su duk da sun fi shi jin jiki, har daya ta rasu daga ciki

An zargi cewa An fifota baiwa Adam A. Zango kulawa fiye da sauran wadanda suka yi Hadari tare a Asibiti inda aka bar su duk da sun fi shi jin jiki, har daya ta rasu daga ciki

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Bayan da kafar Hutudole ta wallafa labarin wata matashiya me suna Natasha wadda ta koka kan yanda mutane ke baiwa Adam A. Zango fifikon Addu'a fiye da sauran wadanda suka yi hadari tare, Wani da yayi ikirarin cewa yana asibitin da aka kai su Adam A. Zango me suna Ibrahim Kalil yace ko a Asibiti haka aka fi baiwa Adam A. Zango fifiko fiye da sauran wadanda suka yi hadarin tare. Ga abinda ya fada kamar haka: "Wallahi gaskiya ta faɗi ko a asibitin da aka kawo su ana zuwa kan Adam Za...