Sunday, February 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Na yi mamaki da naji Kwankwaso ya bayyana ni a matsayin makiyinsa>>Inji Ganduje

Na yi mamaki da naji Kwankwaso ya bayyana ni a matsayin makiyinsa>>Inji Ganduje

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, yayi mamaki da ya ji Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyanashi a matsayin makiyinsa. Yace, shi baya kallon Kwankwaso a matsayin makiyi. Yace ya kamata ace sun wuce wannan wurin, Yace a yanzu hadin kai a Kano na da matukar Muhimmanci. Yace yana kiran Kwankwaso ya hakura da siyasa ya sanyawa zuciyarsa ruwan sanyi. Ganduje ya kuma yiwa Abba maraba da zuwa jam'iyyar APC.
Babu Wani dadi da ake ji a matsayin matar Gwamna Sai Wahala>>Inji Matar Tsohon gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai

Babu Wani dadi da ake ji a matsayin matar Gwamna Sai Wahala>>Inji Matar Tsohon gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai

Duk Labarai
Matar tsohon gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai ta bayyana amincewa da kalaman gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda. Dikko ya bayyana cewa babu wani jin dadi a zama gwamna, mutane na ganin kamar jin dadi suke amma a zahiri wahala suke sha. Ya kara da cewa ko da kasashen waje da suke zuwa, saidai ai ta taruka ba shakatawa suke zuwa yi ba. Hajiya Hadiza da take martani akan kalaman na Gwamnan Katsina, ta bayyana cewa, shima mukamin matar Gwamna haka yake. https://twitter.com/i/status/2010824002781028737
Kusan duk manyan ma’aikatun da ake samun kudaden shiga a Najeriya Bayerabene shugabansu inji Hamma

Kusan duk manyan ma’aikatun da ake samun kudaden shiga a Najeriya Bayerabene shugabansu inji Hamma

Duk Labarai
Me sharhi akan Al'amuran yau da kullun, Hamma, ya yi zargin cewa, kusan duk manyan ma'aikatun da ake samun kudaden shiga, Bayerabene ke shugabantarsu. Ya zano ma'aikatun kamar haka, CBN, NRS, Customs, NNPC da sauransu inda yace duka Yarbawa ne shuwagabanninsu. Ya bayyana cewa, a kowace kabila a Najeriya akwai kwararru, me yasa sai Yarbawa kawai ake baiwa mukami? https://twitter.com/i/status/2010977805069107473 i