Thursday, April 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon yanda aikin gyaran wutar lantarkin Arewa ke gudana

Kalli Bidiyon yanda aikin gyaran wutar lantarkin Arewa ke gudana

Duk Labarai
Bidiyo ya bayyana da ya nuna yanda ake ta kokarin gyara wutar lantarkin Arewa data lalace. Yau Kwanaki 10 kenan cif ba wutar lantarki a Arewa bayan da wasu bata gari suka lalata wutar. Lamarin ya jefa jihohi da yawa a yankin cikin duhu sannan ya sanya mutane da yawa tafka asara ta miliyoyin kudade a wasu Rahotannin ma har rayuwa an rasa. https://twitter.com/DOlusegun/status/1851505945152549093?t=hQXXb7qapmDDPO_IyFYxAw&s=19 Hukumar TCN dai tace ranar Lahadi 3 ga watan Nuwamba za'a kammala gyaran wutar lantarkin.
Kotu ta hana CBN baiwa jihar Rivers rabonta na kudaden shiga daga gwamnatin tarayya

Kotu ta hana CBN baiwa jihar Rivers rabonta na kudaden shiga daga gwamnatin tarayya

Duk Labarai
Babbar Kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta hana babban bankin Najeriya, CBN ci gaba da turawa jihar Rivers kudadenta na shiga da gwamnatin tarayya ke aikawa kowace jiha. Mai Shari'a, Joyce Abdulmalik ce ta yanke wannan hukunci bisa dalilin cewa gwamnan jihar Sim Fubara baya bin doka wajan kashe kudaden da ake turawa jihar. Dan hakane tace kada a sake turawa jihar wadannan kudade. Wasu masu sharhi da yawa dai sun bayyana wannan mataki da cewa ba ya rasa nasaba da rashin jituwa dake tsakanin Gwamna Sim Fubara da Nyesome Wike.
Majalisar tarayya ta fara tantance sabbin ministoci

Majalisar tarayya ta fara tantance sabbin ministoci

Duk Labarai
Majalisar tarayya ta dakatar da duk wani aikin da take a ranar Laraba inda ta fara tantance sabbin ministocin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mika mata sunayensu. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya aikewa da majalisar sunayen sabbin ministocin da ya nada bayan da yawa majalisarsa ta zartaswa garanbawul, inda ya hade wasu ma'aikatun sannan ya kirkiri wasu ya kuma kori wasu ministoci sannan ya nada wasu sabbi. Senator Opeyemi Bamidele ne ya gabatar da fara tantance ministocin sannan sanata Abba Moro ya goya masa baya. Daga nan ne sai aka karanto sunayen sabbin ministocin da za'a tantance wanda ciki akwai Dr. Nentewa Yilwatda a matsayin ministan jin kai da rage talauci, Sai kuma Muhammad Maigari Dingyadi a matsayin ministan ayyuka da kwadago, Sai kuma Bianca Odinaka Odume...
Muna ci gaba da kokarin gyara wutar lantarkin Arewa data lalace kuma zuwa yanzu mun kashe Naira Biliyan 29 a wajan gyaran>>Gwamnatin Tarayya

Muna ci gaba da kokarin gyara wutar lantarkin Arewa data lalace kuma zuwa yanzu mun kashe Naira Biliyan 29 a wajan gyaran>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta hannun kamfanin samar da wutar lantarki na kasa, TCN ta bayyana cewa zuwa yanzu ta kashe Naira Biliyan 29.3 a wajan gyaran wutar Lantarkin data lalace. Karafunan wutar lantarkin 266 ne aka lalata a duka fadin Najeriya. Ciki hadda wanda ya faru kwanannan wanda ya shafi wasu jihohin Arewa. Rahotanni dai sun bayyana cewa, Najeriya na tafka asarar Dala Biliyan 26 duk shekara saboda matsalar lalacewar wutar lantarki. A baya dai irin wannan matsala ta faru a jihohin Abuja, Lagos, Kano, Enugu, Bauchi, Port Harcourt, da yankin Benin.
Darajar Naira ta dan farfado a kasuwar Canji

Darajar Naira ta dan farfado a kasuwar Canji

Duk Labarai
Darajar Naira ta dan farfado a kasuwar canji ranar Talata. An sayi dala akan Naira 1,725 ranar Talata, idan aka kwatanta da Yanda aka sayi Dalar akan Naira 1,730 ranar Litinin, za'a iya ganin cewa darajar Nairar ta dan farfado da Naira 5. Hauhawar farashin dala dai na daga cikin abubuwan dake kara tsadar kayan abinci a Najeriya.
‘Yan ta’adda sun kwace iko da sansanin horas da soji mafi girma a Najeriya

‘Yan ta’adda sun kwace iko da sansanin horas da soji mafi girma a Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan Bindiga sun kwace iko da sansanin horas da soji na Nagwamase Military Cantonment dake karamar hukumar Kwantagora a jihar Naija. Hakanan aun kuma kori mutanen kauyukan dake kusa da sansanin. Majalisar jihar Naija ce ta bayyana hakan inda ta ti kira ga gwamnati data ta kawo karshen ayyukan 'yan ta'addan. Jimullar Kauyuka 23 ne dai 'yan Bindigar suka kwace iko dasu. Dan majalisar jihar dake wakiltar Kwantagora, Abdullahi Isah ne ya kai maganar zauren majalisar ranar Talata inda yace sansanin horas da sojin dake da girma wanda yake a cikin karamar hukumar Kwantagora har zuwa karamar hukumar Mariga a yanzu yana hannun 'yan Bindigar. Ya bayyana cewa kasancewar 'yan Bindigar a cikin sansanin yana a matsayin wata barazanane ga jama'ar yankin inda yac...
A karshe dai Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar da zara gyara wutar lantarkin Arewa

A karshe dai Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar da zara gyara wutar lantarkin Arewa

Duk Labarai
Kamfanin TCN ya bayyana ranar Lahadi, 3 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da zai gyara wutar lantarkin Arewa. Kamfanin yace yana yin dukkan mai yiyuwa dan ganin ya dawo da wutar zuwa yankin Arewa. Wakilin Kamfanin, Sule Abdulaziz ne ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a babban birnin tarayya, Abuja ranar Talata. Tun ranar 22 ga watan October ne dai aka fara samun matsalar wutar. Ya kara da cewa suna kokarin dawo da wutar ne bisa kokarin basu tsaro da sojojin Najeriya ke yi.
Da Duminsa: Gwamnati ta kara farashin man fetur

Da Duminsa: Gwamnati ta kara farashin man fetur

Duk Labarai
Rahotanni da muke samu na cewa Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya kara kudin man fetur. Rahotan yace a yanzu sabon farashin man ya kai Naira 1060 akan kowace lita a Abuja inda kuma a Legas ake sayansa akan Naira 1025 akan kowace lita. Makonni 3 da suka gabata ne dai kamfanin na NNPCL ya kara farashin man fetur din zuwa 1030 akan kowace lita. Hakan na zuwane bayan da shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya baiwa 'yan Najeriya zabin sayen man fetur akan Naira 1000 ko su koma amfani da CNG wanda ake saye akan Naira 200 kan kowace lita.