Thursday, December 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Mummunan hàrì yayi sanadiyyar salwantar rayuka 10 a jihar Filato

Mummunan hàrì yayi sanadiyyar salwantar rayuka 10 a jihar Filato

Duk Labarai
Aƙalla mutum 10 ne aka kashe tare da sace shanu a wani sabon rikici da ya ɓarke a yankin ƙaramar hukumar Riyom a jihar Plateau. Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata amfanin gona da sace shanu da kashe wasu dabbobin, kamar yadda Gidan Talbijin na Channels a ƙasar ya ruwaito. Cikin wata sanarwa da rundunar soji ta 'Operation Safe Haven' ta fitar ta ce rikicin ya fara ne tun a ranar Litinin 12 ga watan Mayun da muke ciki, a lokacin da aka zargi wasu fusatattun matasa da kashe wasu shanu da suka yi zargin sun shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan da ke ƙaramar hukumar ta Riyom. A ranar 13 ga watan ne kuma aka zargi wasu makiyaya da kai hari ƙauyen Danchindo domin ramuwar gayya, tare da kashe mutum huɗu kafin su tsare bayan zuwan jami'an tsaro. Haka kuma a ranar 14 aka zargi wasu mah...
Sai Talaka ya Dara: Na sha Alwashin karya farashin shinkafa warwas>>Inji BUA

Sai Talaka ya Dara: Na sha Alwashin karya farashin shinkafa warwas>>Inji BUA

Duk Labarai
Shugaban rukunin kamfanonin kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya alƙawarta sake rage farashin shinkafa da sauran kayan abinci, wanda ya ce tun shekarar da ta gabata yake ta sauka. Abdul Samad Rabiu ya bayyana haka ne ranar Alhamis jim kaɗan bayan ganawarsa ta Tinubu a fadar shugaban ƙasar. Shugaban na BUA ya yaba wa Tinubu kan bayara da damar shigo da wasu kayan abinci da ya yi, yana mai bayyana matakin da 'kyakkyawa'' da ya ce ya taimaka wajen karyewar farashin kayan abinci a ƙasar. A watan Yulin 2024 ne gwamnatin Shugaba Tinubu ta bayayna dakatar da karɓar kudin fito na shigo da kayan abinci a wani mataki na magance hauwarar farashin kayayyaki. BUA ya zargi masu sayen kayyaki domin ɓoyewa da haddasa tashin farashin. Ya ce da zarar lokacin girbe amfanin gona ya yi, sai wasu ...
Ba ma fatan Najeriya ta zama ƙasa mai bin tafarkin jam’iyya ɗaya – APC

Ba ma fatan Najeriya ta zama ƙasa mai bin tafarkin jam’iyya ɗaya – APC

Duk Labarai
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC, Felix Morka, ya bayyana cewa duk da ƙaruwar mutane da ke sauya sheka zuwa jam’iyyar, jam’iyyar mai mulki ba ta da niyyar mayar da Najeriya ƙasa mai jam'iyya ɗaya tak. Ya bayyana cewa a lokacin da Jam’iyyar PDP, ke mulki, ta rike fiye da jihohi 28 ba ba a zarge ta da ƙoƙarin mayar da ƙasar ta zama ƙasa mai jam'iyya ɗaya ba. Morka ya ce babu wani laifi ga mambobin jam'iyyun PDP da LP da ke sauya sheka zuwa APC idan suna son su haɗa kai da tsarin jam’iyyar mai mulki. Ya ce, “Da yawa daga cikin waɗannan mutane na shigowa a cewarsu don zama a ɓangaren da ke kan tsari. “A ƙasar mu, duka a cikin ƙundin tsari dokar zaɓe, da kuma sauran dokoki da dama, akwai tsarin da ya tabbatar da cewa Najeriya ƙasa ce mai jam’iyyun siyasa da dama kuma al’umma ...
Tinubu zai halarci bikin rantsar da sabon fafaroma

Tinubu zai halarci bikin rantsar da sabon fafaroma

Duk Labarai
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai halarci bikin rantsar da sabon fafaroma, Leo XIV da za a gudanar a birnin Rome na asar Italiya. Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce Tinubu zai tafi Rome a ranar Asabar domin halartar bikin, bisa gayyatar da sabon fafarman ya aike masa. Sanarwar ta ce Tinubu zai yi bulaguron ne tare da manyan jagororin ɗariar Katolika na Najeriya domin shaida bikin rantsar da sabon fafaroman wanda shi ne na 267. Fadar shugaban ƙasar ta ce cikin takardar gayyatar sabon fafaroman ya bayyana alaƙar ƙashin kai da Najeriya, yana mai cewa ''ƙasarka mai girma na da mutuƙar muhimmanci a gareni, saboda na yi aiki a majami'ar Apostolic Nunciature da ke birnin Lagos a shekarun 1980''.
Rashin tsaro: Tinubu na ganawa da shugabannin hukumomin tsaro na ƙasa

Rashin tsaro: Tinubu na ganawa da shugabannin hukumomin tsaro na ƙasa

Duk Labarai
A halin yanzu shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na wata ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro da kuma babban sufeton ƴansanda na kasa (IGP) a fadar shugaban kasa da ke Abuja. DAILY TRUST ta rawaito cewa wadanda su ka halarci ganawar sun hada da babban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa; Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede; Hafsan Hafsoshin Sojan Sama, Air Marshal Hassan Abubakar; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla; da Sufeto Janar na ƴansanda, Kayode Egbetokun. Ko da ya ke ba a fayyace cikakken bayanin taron ba har zuwa lokacin da Trust ta buga labarin, amma tattaunawar ba za ta rasa nasaba da sabbin hare-haren ƴan ta'adda a wasu sassan kasar ba.
An kama ‘yan Arewa 89 a Kudu da sunan Wai Mahara ne, saidai ‘yansanda sunce ma’aikatan kamfanin Dangote ne

An kama ‘yan Arewa 89 a Kudu da sunan Wai Mahara ne, saidai ‘yansanda sunce ma’aikatan kamfanin Dangote ne

Duk Labarai
Wasu 'yan Arewa 89 da aka kama a Legas da zargin cewa mahara ne, hukumar 'yansandan Najeriya ta fito tace ba mahara bane, ma'aikatan kamfanin Dangote ne. Hukumar 'yansandan Legas sun ce ma'aikatane aka kawo daga Katsina zasu yi aiki a matatar man fetur ta Dangote. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1923264289097281970?t=Ig44GRbIaAHgCrswQluiSg&s=19 Kakakin 'yansandan jihar Legas, CSP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da cewa sun gudanar da bincike kuma sun gano ma'aikatan matatar man Dangote daga Katsina ba mahara ba.
BUA ya yabawa Tinubu kan karyewar farashin kayan abinci

BUA ya yabawa Tinubu kan karyewar farashin kayan abinci

Duk Labarai
BUA ya yabawa Tinubu kan karyewar farashin kayan abinci Shugaban Kamfanin BUA , Abdulsamad Isyaku Rabiu, ya ce hangen nesa da shugaba Bola Tinubu ya yi wajen samar da rangwamen haraji kan muhimman kayan abinci a bara ya taimaka wajen karya farashin kayan abinci a Najeriya. Rabiu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawa da Shugaban Kasa a jiya Alhamis. “Farashin abinci yana raguwa a Najeriya kuma muna kokarin tallafawa wannan yunkuri. “Za ku tuna cewa mai girma Shugaban Kasa ya bayar da rangwamen haraji a bara domin a shigo da wasu kayan abinci kamar shinkafa, masara, alkama da dawa cikin ƙasa. “A lokacin, farashin abinci ya yi matuƙar tsada; farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 a bara ya kai kusan Naira 1...