Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ganduje zai dawo jam’iyyar mu ta PDP>>Inji Sule Lamido

Ganduje zai dawo jam’iyyar mu ta PDP>>Inji Sule Lamido

Duk Labarai
Jigo a jam'iyyar PDP tsohon gwamnan jihar Jigawa Alh.Sule Lamiɗo, ya yi hasashen cewa za a samu ɓarkewar rikici mai girma a jam'iyyar APC, inda ya ce nan da ɗa wani lokaci kaɗan jiga-jigai a Jam'iyyar APC, ciki har da shugaban jam'iyya na ƙasa, Dr.Abdullahi Umar Ganduje za su iya komowa cikin jam'iyyar PDP. Lamiɗo ya bayyana haka ne ya yin gangamin taron da aka gudanar a filin taro na Aminu kano Triangle a babban birinin jiha Dutse a lokacin zaɓan shuwagabannin jam'iyyar a matakin jiha. Ya ce "Na tabbatar da cewa waɗanda suka bar jam'iyyar PDP za su dawo, domin APC a cike take da rigima kuma nan ba da daɗewa ba gayyar za ta watse" ~Sule Lamiɗo Ya ƙara da cewa "Ku rubuta ku a jiy, nan da watanni shida da yawa daga cikin waɗanda suka koma j'iyyar APC za su dawo PDP, kuma idan suka y...
Karanta Jadawalin wanda suka halarci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP

Karanta Jadawalin wanda suka halarci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP

Duk Labarai
Ministan Tinubu na Abuja Nyesom Wike ya halarci taron jiga-jigan jam'iyyar PDP na Nijeriya da a ka gudanar a daren Lahadin a Abuja Taron wanda Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya kira da nufin Dinke Barakar da Jami’iyar PDP ke fama da ita ta samu halartar tsoffi da gwamnonin jam'iyyar PDP Da Shuwagabanin kamarMembers na National Working Committee (NWC) a jagoran Shugaban Riko Ambassador Iliya Damagum. GovernorH.E. Senator Bala Abdulkadir Mohammed (Bauchi State) - Chairman H.E Dr. Agbu Kefas ( Taraba State) - Member H.E. Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa State) - Member H.E. Dr. Dauda Lawal (Zamfara State) - Member H.E. Senator Ademola Adeleke, (Osun State) - Member H.E. Pastor Umo Eno Ph.D (Akwa Ibom State) - Member H.E. Dr. Peter Mbah (Enugu State) - Member H.E. B...
Nuna banbancin Addini ne da Muslim-Muslim da APC ta yi suka sa Peter Obi ya samu suna amma ba wai wani tsari me kyau gareshi ba>>Inji Omoyele Sowore

Nuna banbancin Addini ne da Muslim-Muslim da APC ta yi suka sa Peter Obi ya samu suna amma ba wai wani tsari me kyau gareshi ba>>Inji Omoyele Sowore

Duk Labarai
Mawallafin Jaridar Sahara Reporters kuma tsohon da takarar shugaban kasa a jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore yace Peter Obi ya samu daukaka ne saboda nuna banbancin Addini. Ya bayyana cewa saboda APC ta tsayar da duka 'yan takara musulmai shiyasa Kirista su kuma suka zabi Peter Obi. Yace amma Peter Obi ba wani tsari ne gareshi da zai kawowa Najeriya ci gaba ba wanda za'a ce shine yasa shi ya samu daukaka.
Gwamnatin Tarayya ta dauki manyan Lauyoyi dan karawa da Gwamnonin PDP a kotu game da dakatar da Gwamnan Jihar Rivers

Gwamnatin Tarayya ta dauki manyan Lauyoyi dan karawa da Gwamnonin PDP a kotu game da dakatar da Gwamnan Jihar Rivers

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta dauki manyan lauyoyi ciki hadda tsohon ministan shari'a kuma babban lauyan Gwamnati, Chief Akin Olujinmi (SAN) dan su kareta game da karar da Gwamnonin PDP 11 suka shigar da ita suna kalubalantar dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya wa Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara. Sauran lauyiyin da gwamnatin tarayya ta dauka sun hada da Prof Kanyinsola Ajayi, Jelili Owonikoko, Kehinde Ogunwumiju, Tijani Gazali, Babatunde Obama , Olawale Fapohunda, Olumide Olujinmi, Akinyemi Olujinmi da Ademola Abimbola. Sauran sune, Akinsola Olujinmi, Oluwole Ilori, Abdulwahab Abayomi, Mojeed Balogun, Jideuche Ezi sai Ramat Tijani. Gwamnonin jihohin Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Plateau, Delta, Taraba, Zamfara, da Bayelsa ne suka shigar da gwamnatin kara s...
Dangote ya nanata cewa, yana da man fetur din dake iya wadatar da Najeriya duk da ‘yan kasuwar man sun ce ba gaskiya bane

Dangote ya nanata cewa, yana da man fetur din dake iya wadatar da Najeriya duk da ‘yan kasuwar man sun ce ba gaskiya bane

Duk Labarai
Matatar fetur ta Dangote ta nanata cewa, tana samar da isashshen man fetur din dake iya wadatar da Najeriya. Hakan na zuwane bayan da 'yan kasuwa masu Depot din sayar da man fetur din suka ce sune ke wadatar da sauran sassan Najeriya dan har yanzu Matatar man ta Dangote bata iya wadatar da dukan Najeriya da man fetur din da take da dashi. Shugaban 'yan kasuwar, Olufemi Adewole ne ya bayyana hakan inda yace duk da yawan man fetur din da 'yan Najeriya ke sha ya ragu, har a haka ma Matatar ta Dangote bata iya wadatar da Dukan Najeriya da mai. Yace sune ke kokarin yin hakan. A bangare guda kuma, Wata majiya daga matatar man fetur din ta Dangote ta bayyanawa kafar Punchng cewa, Matatar tasu na wadatar da Najeriya har ma ta fitar da Man fetur din zuwa kasashen waje.
An gudanar da taron masu ruwa da tsaki na PDP dan shawo kan matsalar masu ficewa daga jam’iyyar zuwa APC, kuma Wike ma ya halarci wajan

An gudanar da taron masu ruwa da tsaki na PDP dan shawo kan matsalar masu ficewa daga jam’iyyar zuwa APC, kuma Wike ma ya halarci wajan

Duk Labarai
An gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a Abuja. An gudanar da taronne a gidan Gwamnatin jihar Bauchi dake Asokoro A Abuja. Manyan 'yan jam'iyyar da yawa da suka hada da Ahmad Makarfi, Seriake Dickson, Gwamna Bala Muhammad, Gwamna Agbu Kefas, Gwamna Ahmadu Fintiri, Gwamna Dauda Lawal Dare, Gwamna Ademola Adeleke, Gwamna Caleb Muftwang, Da Dai Sauransu. Wani abin ba zata shine, Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ma ya halarci taron