Kalli Bidiyon: Ni a wajena babu Musulmi makiyin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ko da wanda basa Maulidi, Basu Fahimceshi bane amma suna da hanyar da suke bi wajan daraja Annabi>>Inji Dr. Murtala Abubakar Argungun
Malamin Addinin Musulunci, Dan Darika, Dr. Murtala Abubakar Argungun ya bayyana cewa, shi a wajensa babu Musulmi makiyin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).
Malam yace ko da wadanda basa Maulidi baya daukarsu a matsayin makiyan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) kawai dai akwai sabanin fahimta ne kan yanda ya kamata a girmama Annabi.
Wannan kalamai nasa sun jawo masa yabo sosai inda mutane ke cewa haka ya kamata a rika wa'azi.
https://www.tiktok.com/@drmurtalaabubakarargungu/video/7552325369139973394?_t=ZS-9061J3L3XIP&_r=1








