Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Wani Matashi yaje zance wajen budurwa yayanta ya fito da gora ya bùgà masa a ka Ya ràsù a Kano

Wani Matashi yaje zance wajen budurwa yayanta ya fito da gora ya bùgà masa a ka Ya ràsù a Kano

Duk Labarai
Wani Matashi yaje zance wajen budurwa yayanta ya fito da gora ya buga masa a ka Ya rasu. Cikin wani sako da mai magana da yawun randunar SP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa yace “Matashi yaje zance wajen budurwa, yayanta ya fito da gora ya buga masa a ka. Ya rasu, shi kuma yana hannun Yan Sanda. Daga karshe Kiyawa yace nan gaba kadan zasu fitar da cikakken bayani.
Zan halarci taro kan tsaro da majalisa ta Shirya>>Ministan Tsaro Badaru

Zan halarci taro kan tsaro da majalisa ta Shirya>>Ministan Tsaro Badaru

Duk Labarai
Ministan tsaro, Muhammadu Badaru ya bayyana cewa, zai halarci taron tsaro da majalisa ta shirya. Ya bayyana hakane a ranar Lahadi ga manema labarai. Badaru a baya yace canja tsarin tsaro ne zai fi kawo ci gaban matsalar tsaro a taron ba. Saidai a yanzu yace shawarwarin da za'a bayar a wajan taron zasu taimaka wajan aiwatar dasu a aikata dan kawar da matsalar tsaron.
DA ƊUMI-ƊUMINSA: Hùkumar Hisba Ta Haramta Çàça, Dara Da Wasan Ĺìdo Da Ake Bugawa A Wayoyin Hannu A Garin Dutsin-ma Na Jihar Katsina

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Hùkumar Hisba Ta Haramta Çàça, Dara Da Wasan Ĺìdo Da Ake Bugawa A Wayoyin Hannu A Garin Dutsin-ma Na Jihar Katsina

Duk Labarai
Hùkumar Hisba Ta Haramta Çàça, Dara Da Wasan Ĺìdo Da Ake Bugawa A Wayoyin Hannu A Garin Dutsin-ma Na Jihar Katsina Daga Comr Nura Siniya Hukumar Hisbah reshen karamar hukumar Dutsin-ma a jihar Katsina ta saka dokar hana caca da wasan lido a majalissun gari da sauran wuraren masha'a domin yaki da ayyukan badala a karamar hukumar ta Dutsin-ma da ma jihar Katsina baki ɗaya. Haka zalika Hisba ta haramta dara da wasan karta da aka fi sani da “Whot wanda ake bugawa a wayoyin hannu da kasuwanni. Hukumar ta gargadi jama'a da su kiyaye idan ba haka ba za su fuskanci fushin hukuma.
Allah ya min Wahayin mutane 3 da su kadai ne zasu iya kayar da Tinubu zaben 2027>>Inji Malamin Kirista Primate Elijah Ayodele

Allah ya min Wahayin mutane 3 da su kadai ne zasu iya kayar da Tinubu zaben 2027>>Inji Malamin Kirista Primate Elijah Ayodele

Duk Labarai
Babban malamin Kirista, Primate Elijah Ayodele ya bayyana cewa Allah ya masa Wahayin mutane 3 wanda su kadaine idan daya daga cikinsu ya fito takarar shugaban kasa to zai iya kayar da Tinubu. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Tribune. Yace amma ko da za'a kafa mishi Bindiga ba zai fadi sunayen mutanen ba amma idan dayansu ya fito takara, zai ce Eh Shine. Yace ko da Atiku ko Peter Obi ne suka ci zabe babu abinda zai canja daga halin da 'yan Najeriya ke ciki.
An ceto ƴar shekara biyu da aka sàyàr kan 100,000 a Abuja

An ceto ƴar shekara biyu da aka sàyàr kan 100,000 a Abuja

Duk Labarai
Hukumar da ke yaƙi da fataucin mutane a Najeriya, NAPTIP ta ce ta ceto wata yarinya ƴar shekara biyu da aka yi safararta zuwa jihar Abia daga Abuja. Wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Juma'a, ta ce hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ne suka kama wanda ya yi safararta, inda ake zargin ya sayar da da ita kan naira 100,000. "Mun samu nasarar ceto Chiamaka Favor, bayan safararta daga Abuja zuwa Aba a watan Febrairun 2025. "Ana zargin wanda ya yi safararta ya yi aiki da wasu ƙungiyoyin safarar mutane uku a Abuja - sannan ya sayar da ita ga wani kan naira 100,000. Muna ci gaba da bincike," in ji NAPTIP. Hukumar ta kuma yi kira ga iyayen yarinyar ko ƴan uwanta da su hanzarta su tuntuɓe ta domin karɓar ƴarsu.
Atiku ya soki EFCC kan tsare Hon Gudaji Kazaure

Atiku ya soki EFCC kan tsare Hon Gudaji Kazaure

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya soki hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC kan tsare tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Muhammad Gudaji Kazaure. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya kwatanta kama Kazaure da kuma tsare shi a matsayin saɓa wa doka. "EFCC ta sake aikata abin da ta saba na take doka, ta hanyar kamawa da kuma tsare ƴan ƙasa da ba su aikata laifin komai ba," in ji Atiku. Ya yi misali da labarin fitattcen ɗan gwagwarmayar nan Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da Verydarkman wanda EFCC ta kama amma ta sake shi bayan matsin lamba daga wajen ƴan ƙasar. "Yanzu kuma hukumar ta koma kan Gudaji Kazaure. Sun kama shi ba tare yin wani bayani na laifi da suke tuhumarsa da aikatawa ba. "An ɗauke shi daga Kano zuwa ...
Hukumar NIMC ta kara kudin yin katin zama dan kasa, an kuma kara kudin canja shekarun haihuwa zuwa Naira N28,574

Hukumar NIMC ta kara kudin yin katin zama dan kasa, an kuma kara kudin canja shekarun haihuwa zuwa Naira N28,574

Duk Labarai
Hukumar yin rijistar katin zama dan kasa ta NIMC ta kara farashin yin katin zama dan kasan. Tun a ranar 1 ga watan Mayu ne dai hukumar ta NIMC ta sanar da cewa, zata kara farashin yin katin zama dan kasar. A sanarwar data fitar Ranar Asabar, Hukumar tace ta kara farashin canja ranar Haihuwa daga Naira N16,340 da ake biya a baya, zuwa Naira N28,574 a yanzu. Hakan na nufin an yi karin kaso 74.87 a cikin kudin. Farashin canja sauran bayanai kamar suna da adreshin gidan zama shima ya tashi zuwa Naira N2,000 daga Naira N1,522 da ake biya a baya. Hakan na nufin an samu karin kaso 31.41 cikin 100 akan farashin da aka saba biya. Bada katin zama dan kasar da rijista duk kyauta ne amma idan ya bace, an canja farashin baiwa mutum sabo daga Naira 500 zuwa 600.
Kalli Bidiyo: Dan gidan Ministan Abuja, Wike ya wallafa irin rayuwa kece rainin da yake yi

Kalli Bidiyo: Dan gidan Ministan Abuja, Wike ya wallafa irin rayuwa kece rainin da yake yi

Duk Labarai
Daya daga cikin 'ya'yan Ministan Abuja, Nyesom Wike ya wallafa Bidiyon rayuwar kece Raini da yake. Bidiyon ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta inda aka ganshi a cikin jirgin sama da kasashen waje da sauran gurare na alfarma. https://twitter.com/GossipMillNaija/status/1921517476505878616?t=XiTAWxRUilQ20N2Hp3eV6Q&s=19 Wasu dai sun bayyana cewa, wannan kudin al'ummar Najeriya ne.
Taron Coci ya watse a Karu Abuja bayan da aka zargi Faston cocin da dirkawa daya daga cikin mabiyansa ciki

Taron Coci ya watse a Karu Abuja bayan da aka zargi Faston cocin da dirkawa daya daga cikin mabiyansa ciki

Duk Labarai
Wata hatsaniya ta faru a Cocin Redeem church dake Karu a babban birnin tarayya, Abuja bayan da aka zargi faston cocin da dirkawa daya daga cikin membobinsa ciki. Rahoton yace faston ya zubar da cikin bayan da ya ga Asirinsa zai tonu. Sannan ya bayar da Naira miliyan 3 toshiyar baki dan kada a tona masa asiri amma duk da haka ana tsaka da taron Lahadi a cocin wani ya masa tonon silili.