DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bada gurbin talkafin karatu na ƙasashen waje ga ɗalibai 9 da su ka gama da sakamako mafi girma a jami’ar kimiyya da fasaha ta Dangote da ke Wudil
Gwamnan ya sanar da wannan tallafi ne yayin da ya ke jawabi a bikin yaye ɗalibai karo na 5 a jami'ar da ke gudana a yanzu haka.
Daliban dai sun samu sakamako mafi kyau a fannoni daban-daban.








