INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Umar Salisu Dan Reno Danbatta, Cikon Na Biyar Daga Cikin 'Yan Gida Daya Su Hudu Da Suka Ràsù Sakàmakon Hadari Shi Ma Ya Rasu Daga Baya
Allah Ya gafarta musu.
“
Babu ƙanshin gaskiya a cewar da ake yi ƴan ta'adda na da makaman da su ka fi na jami'an tsaron Nijeriya” Inji Ministan Tsaron Nijeriya Muhammad Badaru Abubakar.
A Cikin Shekaru Biyu Na Gwamnatin Tinubu An Sami Cìkakken Tsaro Akan Hanyar Abuja Zuwa Kaduna, Wanda A Baya Ya Taɓa Kasancewa Tungar Masu Ģarkuwa Da Mutane, Inji Ministan Tsaro, Badaru
"Daga watan Mayun 2023 zuwa yanzu mun yi nasarar murƙushe ƴan ta'adda har 13,000, kazalika an kawar da shugabannin Boko Haram sama da 300
"A Maiduguri, a baya da an ce Gambaru, Bama, ka san an ambaci hanya mai hatsarin gaske, amma a yanzu hakan ya zama tarihi, duk wannan ya faru ne a cikin shekaru 2 na wannan gwamnatin".
Sojojin Nijeriya Sun Cancanci Lambar Yabo Fiye Da Wanda Ake Yi Musu A Yanzu, Duba Da Yadda Suke Yin Nasara Àka...
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban sojojin Najeriya, General OO Oluyede ya koma jihar Borno da zama dan kula da yanda sojoji ke aikin magance matsalar tsaro.
A 'yan Kwanakinnan dai Hare-haren kungiyar Bòkò Hàràm sun yawaita inda aka gansu da makamai na zamani.
Majalisar tarayya ma ta bayyana cewa, 'Yan Bòkò Hàràm din sun fi sojojin Najeriya makamai masu kyau.
Wasu na ganin komawar shugaban sojojin zuwa jihar Borno zai taimaka matuka wajan magance matsalar tsaron jihar da makwabciyarta Yobe.
DAGA ZAUREN MAJALISA :
Sanata Kawu Sumaila (Kano ta Kudu) ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC a zaman majalisar dattawa na yau. Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar sauya shekar tasa.
Inside Bauchi State07-05-2025
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi karin haske kan sana’ar da zai fara bayan ya kammala wa’adin mulkinsa zango na biyu.
Gwamna Sule yace zai koma sana’ar da ya fara yi tun kafin fara mulkin jihar Nasarawa wato sana,ar walda, da zarar ya kammala wa’adin mulkinsa a shekarar 2027.
Yace akwai alkairi a cikin Sana’ar ta walda sosai ,Inda ya nemi matasa da su dage da Sana’a
Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron tattaunawa da hukumar samar da wutar lantarki ta karkara ta shirya tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Nasarawa.
Ya kuma yi amfani da damar wajen tabbatarwa da masu sha’awar zuba jari cewa jihar Nasarawa na da ƙwararrun ma’aikata, inda ya nuna cewa jihar na da ɗimbin matasa masu horo da shaidar ƙwarewa da za su iya tallafawa mas...
Wata budurwa ta dauki hankula a kafafen sada zumunta bayan da ta gayawa Saurayinta cewa yana talaucewa zata rabu dashi.
Suna tafiya a motane ta musu Bidiyon inda take gayawa Saurayin nata hakan.
https://www.youtube.com/watch?v=w-e8AYYBals?si=m_PIp1ggJ-UcJBVQ
Sau da yawa akan zargi mata da yin soyayya ba dan Allah ba.
'Yan majakisar Wakilai musamman wadanda suka fito daga jihohin da matsalar tsaro ta yi kamari sun gayawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dauki mataki akan lokaci ko kuma mutane na Daf da giwa Gwamnatin sa Bore.
'Yan majalisar sun bayyana takaici kan kasa magance marsalar tsaro a kasar nan duk da kashe makudan kudaden da suka kai Naira Tiriliyan 19.7 akan tsaron a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2019.
An fara tattaunawar ne biyo bayan korafin harin da aka kai kan Giwa Barak a jihar ta Borno da kuma kashe-kashen da ake yi a Jihohin Borno da Yobe.
Dan majalisa, Ahmed Satomi ya fara yin maganar a zaman majalisar inda sauran 'yan majalisar da yawa suka nuna damuwa sa alhini.
Kakakin majalisar, Godswill Akpabio yace ya kamata a bar maganar siyasa a dakatar da wannan matsalar tsarom
FATIMA DAHIRU: Mace Mai Horar Da Maza Kwallon Kafa A Kano.
'Yar asalin jihar Kano ce, wacce kuma ta zamo mace daya tilo a Nijeriya dake horas da 'yan wasan kwallon kafa, bayan zamowa kocin kungiyar kwallon kafa ta Manya United.
Kwamishina ya mayar da Naira miliyan 301 ragowar kuɗin ciyarwar azumi a Jigawa.
Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Auwalu Danladi Sankara, ya mayarwa baitul malin jihar Naira miliyan 301 da su ka yi ragowa bayan kammala shirin ciyarwa na watan Ramadan bana.
Sankara ya sanar da mayar da kudaden ne a yayin taron majalisar zartarwa na jiha wanda gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranta.
Kudin sun yi ragowa ne biyo bayan ware naira biliyan 4.8 da gwamnatin jihar Jigawa ta baiwa ma’aikatar don shirin ciyar da abinci, wanda ya kunshi dukkanin kananan hukumomi 27 da kuma cibiyoyi kusan 700 na ciyarwa.
An ba da rahoton cewa, shirin wanda wani kwamiti ya jagoranta, ya ciyar da mutane sama da 5,550 a kullum a tsawon kwanaki 29 na azumi.
Majalisar zartaswar jihar ta yaba ...