Wani matashi da ya kàshè mutane wajen ƙwacen waya ya kai kan sa wajen ƴansanda a Kano
Wani matashi mai shekaru 20 da ya amsa da bakin da cewa ya kashe mutane wajen ƙwacen waya a gurare daban-daban ya miƙa kansa da kansa ga rundunar ‘yansanda ta jihar Kano.
Wanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa da Umar Auwal, mai lakabi da ‘Abba Dujal,’ mazaunin karamar hukumar Wudil a jihar Kano, ya amsa cewa yana da hannu a laifukan kisan kai, fashi da makami da kuma sata, musamman na babura da wayoyin hannu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, SP Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa miƙa kansa da Auwal ya yi ya biyo bayan zurfafa samame da rundunar ke yi a maboyar ‘yan ta’adda a jihar.
Kiyawa ya ce wannan mataki yana daga cikin kokarin da rundunar ke yi na dawo da doka da oda da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Auwal ya amsa cewa ya daba wa wani...








