Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Pastor Umo Eno ya bayyanawa kwamishinoninsa cewa zai koma jam'iyyar APC.
Yace bai kamata hakan ya zowa mutanen nasa da mamaki ba inda yace duk wanda ya ga ba zai iya binsa zuwa APC ba sai ya ajiye mukamin da ya bashi.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana mamaki kan yanda aka kama mutum daya da gidaje guda 750 na sata.
Shugaban ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka yi dashi.
https://twitter.com/NigeriaStories/status/1925602986862026869?t=qws3dWF2gX9hlD6h8_cn_Q&s=19
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Emefiele ne aka kama da wadannan gidaje wanda tuni an kwace za'a sayar dasu.
Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnati ta ceto ƴan ƙasar da ke maƙale a Saudiyya.
Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta ceto ƴanƙasar da ke maƙale a Saudiyya sakamakon sabbin sauye-sauyen dokokin ayyukan ƙwadogo da hukumomin Saudiyya suka bijiro da su.
Dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Hon. Muhammad Bello Shehu ne ya gabatar da udurin a yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
A baya-bayan nan ne dai hukumomin Saudiyya suka bijiro da wasu sauye-sauye kan dokokin da suka shafi ayyukan baƙi a ƙasar, ciki har da daina sabunta takardun izinin aiki a ƙasar ga wasu mutanen.
Hon. Muhammad Shehu ya ce sauye-sauyen sun tilasta wa wasu ƴan Najeriya da dame da ke zaune a Saudiyya rasa ayyukansu, yayin da wasu ke fuskantar tsadar kuɗin sabunta takardun...
Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Jigawa, ta ce ta ceto wata tsohuwa mai shekara 80 da aka yi garkuwa da ita daga gidanta da ke ƙaramar hukumar Minjibir a jihar Kano.
Kakakin Rundunar ƴansandan jihar SP Lawan Adam Shiisu Adam ya ce mutanen da suka yi garkuwa da tsohuwar sun ɓoye ta a cikin wani daji na jihar Jigawa mai makwabtaka.
''Bayan sace tsohuwar, barayin sun tafi da ita wasu dazuka da ke tsakanin ƙananan hukumomin Garki da Sule Tankarkar, daga nan ne jami'ansu tare da haɗin gwiwar ƴanbijilanti da na ƙungiyar ƴanbulala suka far wa maharan, bayan ɗauki-b-daɗi kuma suka samu nasarar ceto ta''
SP Shiisu ya ce jami'ansu sun yi nasarar kama wasu manyan ƴanfashin daji biyar da aka jima ana nema ruwa-a-jallo.
''Daga ciki akwai wanda ma har yana tsallakawa jamhuriyar Nijar ya k...
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da taron ƙoli, karo na farko gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.
Mahalarta taron, wanda ke gudana a yau Alhamis su ne Shugaban ƙasar, Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da kuma shugabannin Majalisar Dattaijai da Wakilai da mataimakansu.
Haka nan gwamnonin jam'iyyar masu ci da kuma tsofaffi suna cikin waɗanda aka gayyata domin halartar taron.
Wannan na zuwa ne gabanin cikar shugaban na Najeriya shekara biyu da kama mulki, daidai lokacin da ake ganin jam'iyyar na ƙara samun tagomashi sanadiyyar tuɗaɗar ƴan adawa zuwa cikin jam'iyyar daga sauran jam'iyyu.
Jam'iyyun adawar ƙasar da dama na fama da rikicin cikin gida, ciki har da babbar jam'iyyar adawa ta ƙasar - PDP, wadda ake kyautata zaton ɗan takararta na shugab...
Ƙungiyar siyasa ta Northern Democrats, ƙarƙashin jagorancin Malam Ibrahim Shekarau ta ce za ta shiga sabuwar haɗakar ƴan hamayya ta National Coalition Group ƙarƙashin tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata David Mark domin tunkarar zaɓen 2027.
A wata sanarwar bayan taron da ƙungiyar ta yi ranar Alhamis, ND ta ce duk da amincewar da ta yi na shiga haɗaka, amma za su ci gaba da bayar da gudunmawa wajen tattaunawa yiwuwar kafa sabuwar jam'iyya ko kuma shiga wata jam'iyyar domin yin tafiya tare.
Harwayau, ƙungiyar ta Northern Democrats ta ƙara da cewa sun amince da matsa wa gwamnati lamba musamman jagorancin majalisar dokoki wajen ganin an tabbatar da bin tsarin mulkin ƙasar sau da ƙafa.
Daga ƙarshe ƙungiyar ta ce mambobinta sun amince su tattauna da jihohin arewacin ƙasa...
Makusantan matashiyar nan da ta yi suna bayan jan hankalin gwamnatin jihar Sokoto kan matsalar tsaro sun tabbatar wa BBC cewa an tsince ta a wani daji na jihar Zamfara bayan batan-dabon da ta yi.
Tun ranar Talata ne aka bayar da rahoton ɓatan Hamdiyya Sidi Sharif, bayan ta fita domin zuwa kasuwa, lamarin da ya sanya ta kasa bayyana a zaman kotu kan shari'ar da ake mata a ranar Laraba a Sokoto.
A watannin baya ne dai gwamnatin jihar Sokoto ta shigar da matashiyar ƙara a gaban kotu, bisa zargin ta da aikata laifin tunzura tayar da zaune tsaye, shari'ar da har yanzu ake gudanar da ita.
A tattaunawarsa da BBC, lauyan da ke kare Hamdiyya, Abba Hikima ya ce yanzu haka tana wani asibiti da ke ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara "cikin mummunan yanayi."
Ya ce ''wasu mutane ne sanye ...
Mun Gama Ýanke Shawarar Mayar Da Tinubu Jihar Legas A Zaben 2027, Domin Za Mu Dakatar Da Shi Daga Zarcewa A Mulki Karo Na Biyu, Inji El-Rufai.
Daga Comr Nura Siniya
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa akwai wani muhimmin yunkuri na kafa hadaka da nufin ganin an dakatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga sake samun mulki a karo na biyu.
Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana hakan ne a yayin taron baje kolin fasaha da ƙirƙira na “Arewa TechFest da aka gudanar a jihar Katsina ranar Laraba 21 ga watan Mayu 2025.
A cewarsa, “Jiya da karfe 8 na dare, mun gudanar da wani muhimmin taro na hadakar da muke kokarin kafa wa domin tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya koma Legas.”
Duk da wannan yunkuri, El-Rufai ya jaddada cewa akwai ministocin da suke ganin sun...
Gwamnonin APC Da Jiga-Jiganta Sun Amince Tinubu Ya Sake Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A 2027
Sun bayyana hakan ne a yayin da taron da suka gudanar a Abuja a yau Alhamis.
Me za ku ce?
Wannan matashiyar ta bayyana cewa, bayan ta kammala karatu na tsawon shekaru 5 yanzu tana bukatar aure.
https://twitter.com/mariyaalqibty/status/1925151480564039902?t=rgC1OREd5-EsZfyIh2U0EQ&s=19
Da yawa sun tayata Murna.