Thursday, May 7
Shadow

Author: Bashir Ahmed

An kama matar da ake zargi da kashe jinjirin kishiyarta da guba

An kama matar da ake zargi da kashe jinjirin kishiyarta da guba

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce ta kama da tsare wata mata mai suna Zaliha Shu'aibu bisa zargin kashe ɗan kishiyarta ɗan wata uku da haihuwa da maganin ƙwari. A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar ta Kaduna, DSP Mansur Hassan ya fitar, al'amarin ya faru ne a ranar 13 ga watan nan na Mayu a gidansu da ke ƙauyen Malari a ƙaramar hukumar Soba. Sanarwar ta ce shaidu sun ce uwar yaron dai ta fita daga ɗakinta domin shiga banɗaki lokacin da kishiyar tata ta shigar mata ɗaki kuma bayan ta koma ɗakin ne ta ga kishiryar rungume da ɗan nata. Bayan ta miƙa mata jaririn ne sai uwar ɗan ta fahimci yadda kumfa ke fita daga bakin yaron nata sannan kuma akwai rauni a wuyansa, inda yaron ya kece da kuka. Bayan bincike, rundunar ƴansandan ta ce matar ta tabbatar da cewa ta aik...
A yayin da Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke cewa zai kayar da Tinubu a 2027, dansa Bello El-Rufai yace Tinubu ne zabinsa a 2027

A yayin da Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke cewa zai kayar da Tinubu a 2027, dansa Bello El-Rufai yace Tinubu ne zabinsa a 2027

Duk Labarai
Dan tsohon Gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai ya bayyana goyon bayansa ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027. Hakan na zuwane yayin da mahaifinsa, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke jam'iyyar SDP da kuma shan Alwashin sai ya kayar da Tinubu daga kan Mulki. Bello Wanda dan majalisar wakilai ne me wakiltar Kaduna ta kudu, na daga cikin wanda suka halarci babban taron jam'iyyar APC inda jam'iyyar ta bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin dan takararta na shekarar 2027. A watan Maris da ya gabata ne dai El-Rufai ya bayyana cewa ya fice daga jam'iyyar APC saboda a cewarsa ta bar turbar da aka kafata akai. Reno Omokri da yake mayar da martani kan lamarin yace idan har El-Rufai ba zai iya jawi hankalin dansa ya bar Tinubu ba ta yaya zai iya jawo hankalin 'yan Najeriy...

Taya zan fara sana’a

Duk Labarai
Fara Sana'a abu ne me sauki sosai, musamman a wannan zamanin da muke na yanar gizo da kafafen sada zumunta. A yanzu ba lallai sai kina ko kana da jari ba sannan zaka fara sana'a ba. Kamin ka fara sana'a, yana da kyau kasan sana'ar kuma kasan ba a dare daya da fara wannan sana'a zaka yi nasara ba, akwai kalibale. Yana da kyau amma ba lallai bane ya zama kana ko kina son sana'ar da kike, ko kake. Mana'ana, zai iya zama ka tsani sana'a amma tana kawo kudi, kaga kuwa bai kamata kawai dan ka tsaneta ka daina ba. Ita sana'a yawanci yana da kyau a fara koyanta kamar yanda muka bayyana. Kuma akwai hanyoyin koyo da yawa, wata kila tana bukatar ka je makaranta irin ta watanni 3 ko watanni shida dinnan wanda ake koya saka, dinki, da sauransu. Ba lallai sai kin ko ka je irin wadannan...

Me ake nufi da kwaila

Sha'awa, Soyayya
Kwaila na Nufin mace sabuwar Balaga amma wadda bata gama mallakar hankalin kanta ba. Kwailanci na farawa ne daga shekaru 15 har zuwa 18 ko 19. A tsakanin wadannan shekaru kwaila bata iya magana ba, ko saurayi ta yi, saidai yayi hakuri da ita yayi ta dorata a hanya har ta zama ta fahimci rayuwa. Duk da dai akwai kwailaye da basu da yawa masu hankali. Hakanan a tsakanin wadannan shekaru, Kwaila na da kaguwa akan abubuwa, musamman ma soyayya, takan bayar da zuciyarta gaba daya idan ta samu saurayi me sonta. To shiyasa a daidai wannan lokaci idan aka samu mara Imani ya gudu ya barta, zata ji kamar ta yi hauka, zata yi kunci sosai da kuka me tsanani. Yawanci kwaila bata damu da kudi ba, ko nawa ka bata zata gode maka, abinda ta fi damuwa dashi shine, wannan kulawar da kake bata d...
Kalli Bidiyon yanda magidanci ya kama matarsa na cin amanarsa, Ta kwantar da diyarsu a kasa

Kalli Bidiyon yanda magidanci ya kama matarsa na cin amanarsa, Ta kwantar da diyarsu a kasa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Wani magidanci a kasar Amurka ya dawo gida ya tarar da matarsa na cin amanarsa inda ta kwantar da diyarsu a kasa. Saidai rashin dukan kwarton yasa mutane su kai ta mamakin hakurinsa. https://twitter.com/vdmempire/status/1925813109328925127?t=Hyez368bocIo46W7dEQ2DQ&s=19 Lamarin ya bayar da mamaki sannan Mijin ya sha Yabo.
Ba ma so a miƙa Hamdiyya ga jami’an ƴansanda – Amnesty

Ba ma so a miƙa Hamdiyya ga jami’an ƴansanda – Amnesty

Duk Labarai
Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International a Najeriya ta soki matakin da hukumomi ke shirin ɗauka na miƙa matashiyar nan da aka gano a jihar Zamfara, Hamdiyya Sharif ga jami’an ƴansanda. Shugaban ƙungiyar Mallam Isa Sanusi ya shaida wa BBC cewa bayanan da suke samu shi ne kwamishinan ƴansanda jihar Zamfara ya nace sai an mayar da Hamdiyya Sharif ga hukumar ƴansandan Sokoto, maimakon ba ta kulawar likitoci, wanda a cewarsa shi ta fi buƙata a halin yanzu. ''Mu yanzu abin da muka fahimta a taƙaice shi ne kenan an kamata, ko kuma sun riƙe ta'', in ji shi. Mallam Isa Sanusi ya yi kira ga hukumomin Najeriya su bai wa matashiyar kariya saboda yadda rayuwarta ke cikin ''barazana''. A yammacin ranar Laraba ne aka gano Hamdiyya Sherif a wani ƙauye cikin jihar Zamfara, bayan ...
Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙarar Sanata Natasha kan zargin ƙage

Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙarar Sanata Natasha kan zargin ƙage

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙarar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, saboda zargin ɓata suna da ta yi a gidan talabijin kai-tsaye. Gwamnatin na zargin dakatacciyar ƴarmajalisar, da ''yin ƙage, duka kuwa da ta san cewa hakan zai shafi ƙimar mutum'', tana mai kafa hujja da cewa yin hakan laifi ne da ke ɗauke da hukunci ƙarƙarshin sashe na 392 na kundin tsarin mulkin ƙasar. Daga cikin jerin mutanen da gwamnatin da sanya a matsayin shaidun da za su tabbatar d zargin, har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello. Ɗaya ɗaga cikin tuhume-tuhumen da gamnatin ke yi wa Sanata Natasha shi ne inda ta zargi Godswill Akpabio da Yahaya Bello da yunƙurin kitsa kasheta. A farkon watan Maris ne da Majalisar Dattawan...