Thursday, March 26
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Gwamnatin sojin Nijar ta hana sojoji yin ritaya

Gwamnatin sojin Nijar ta hana sojoji yin ritaya

Duk Labarai
Gwamnatin sojin Nijar ta hana sojoji yin ritaya A jamhuriyar Nijar, gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta ce ta ɗauki matakin hana jami’an tsaro yin ritaya a wannan shekara ta 2025 ko da kuwa shekarunsu sun kai na ajiye aikin. Wannan matakin na ƙunshe ne cikin wata takarda da ministan tsaro na Nijar, Janar Salifu Modu, ya aike wa hafsan hafsoshin sojin ƙasar, inda ya buƙaci a riƙe ɗaukacin sojojin da shekarunsu suka kai su yi ritaya daga aikin tsaro bisa la'akari da ɗimbin ayyuka da kuma alƙawuran da ke gaban sojojin a duka fadin ƙasar. Hukumomin tsaron ƙasar sun ce sun ɗauki wannan mataki ne saboda buƙatar da ke da akwai ta ƙarin sojoji a fagen daga musamman yadda ƙasar ke ci gaba da fuskantar hare-hare daga kungiyoyi masu ɗauke da makamai a yankunan ƙasar da dama. Shugaban ƙung...
Zulum zai mayar da ‘yan gudun hijira 6,000 gidajensu saboda ‘ƙaruwar karuwanci’ a sansanoni

Zulum zai mayar da ‘yan gudun hijira 6,000 gidajensu saboda ‘ƙaruwar karuwanci’ a sansanoni

Duk Labarai
Gwamnan jihar Borno a arewacin Najeriya ya bayyana shirinsa na mayar da iyalai 6,000 da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu sakamakon abin da ya bayyana da "ƙaruwar karuwanci" a sansanonin 'yan gudun hijira. Yawancin mutanen sun ftio ne daga ƙananan hukumomin Dikwa da Mafa, kamar yadda Gwamna Babagana Zlumu ya bayyana a sansanin 'yan gudun hijira na Muna da ke Maiduguri. A cewarsa, dole ne mutane su koma gidajensu domin su ci gaba da neman abin dogaro da kansu. "Mun lura cewa a sansanin 'yan gudun hijira akwai ƙaruwar karuwanci, da yawaitar 'yandaba, da cin zarafin yara, da kuma aikata laifuka iri-iri," in ji shi cikin wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar. Ya kara da cewa tuni aka mayar da kashi 75 cikin 100 na mazauna sansanin gidajensu. Gwamnan ya kuma ce kowane ma...
Ji Dalilai bakwai da ke ta’azzara talauci a yankunan karkarar Najeriya>>Inji Bankin Duniya

Ji Dalilai bakwai da ke ta’azzara talauci a yankunan karkarar Najeriya>>Inji Bankin Duniya

Duk Labarai
Wani sabon rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna yadda talauci ƙaruwa a yankunan karkara a Najeriya, inda alaƙluma ke nuna ya ƙaru zuwa kashi 75 cikin 100 a watan Afrilu. Rahoton da bankin ya fitar na watan Afrlun 2025, ya nuna cewa talaucin dai ya ƙaru a ɓangren karkara idan aka kwatanta da yadda yake a biranen ƙasar. Rahoton ya yi nazari kan girman talauci a ƙasashen duniya, yana mai bayyana kashi 30.9 cikin 100 na 'yan Najeriya na rayuwa ne kasa da dala biyu a kowacce rana a shekara ta 2018/2019 - kafin annobar korona. Haka kuma, rahoton ya nuna cewar 'wasu alkaluma da aka fitar na 2018/2019 ya nuna cewar akwai karin mutum miliyan 42 da suka sake faɗawa cikin talauci a Najeriya, wanda hakan ke nuni da fiye da rabin al'ummar ƙasar wato kashi 54% da aka yi ƙiyasin na fama da t...
Goodluck Jonathan, da Bukola Saraki sun yiwa Tsohon Shugaban kasa, Marigayi Umar Musa ‘Yaradua addu’a

Goodluck Jonathan, da Bukola Saraki sun yiwa Tsohon Shugaban kasa, Marigayi Umar Musa ‘Yaradua addu’a

Duk Labarai
A yayin da tsohon shugaban kasa, Marigayi, Umar Musa 'Yaradua ya cika shekaru 15 da rasuwa, Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya masa addu'a. Yace 'yaradua ya sashi ya kara fahimtar aikin gwamnati da kyau. Yace bai cika yawan magana ba, kuma idan yayi magana babu siyasa a ciki zaka ji ta me ma'ana ce. Yace bashi da girman kai, yana da kankan da kai. Inda a karshe yayi mai fatan Allah ya ci gaba da sakashi ciki mutane na gari a Aljannah Firdausi. Shima Bukola Saraki a nasa sakon cewa yayi, Muna girmama tsohon shugaban mu da bashi da girman kai ga hangen nesa . Yace manyan abubuwan da ake tuna tsohon shugaban kasar dasu sune, hadin Kan Najeriya, Sulhu da 'yan Naija Delta, zaman lafiya da gyaran Zabe. Yayi fatan Allah ya ci gaba da yi masa Rahama.
Tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Dr. Dalhatu Bafarawa ya koka da rashin kishin kasa na ‘yan siyasa

Tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Dr. Dalhatu Bafarawa ya koka da rashin kishin kasa na ‘yan siyasa

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Dr. Dalhatu Bafarawa yace 'yan siyasar yanzu basu da kishin kasa wanda yace hakan barazanane ga ci gaban Najeriya. Yace yanda ake shirin mayar da mulkin Najeriya babu 'yan adawa abin damuwa ne musamman yanda 'yan adawar ke komawa jam'iyya me mulki saboda abinda zasu samu ba dan kishin masa ba. Yace hakan baranane ga Dimokradiyyar Najeriya. Yace idan aka bar abubuwa suka ci gaba da lalace wa hakan ba karamar illanzai wa Najeriya da al'ummarta ba. Ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi a kafar BBCHausa.
EFCC ta kama matashi bayan da yayi Bidiyo yana wulakanta Naira a Kaduna

EFCC ta kama matashi bayan da yayi Bidiyo yana wulakanta Naira a Kaduna

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Hukumar yaki da rashawa da ci hanci EFCC ta kama matashin da yayi Bidiyo yana wulakanta Naira yana talata inda kuma ya nemi ida EFCC din sun isa su kamashi. Matashin me amnfani da sunan @youngcee0066 a Tiktok tuni ya shiga hannu. Hukumar tace ta kama matashin me suna Muhamad Kabir Sa'a a unguwar Tudun Wada dake Kaduna. Tace nan gaba zata gurfanar dashi a gaban kotu dan a yanke masa hukunci.
JIYA BA YAU BA: Farashin Kaya A Lokacin Mulkin Marigayi ‘Yar’Adua

JIYA BA YAU BA: Farashin Kaya A Lokacin Mulkin Marigayi ‘Yar’Adua

Duk Labarai
JIYA BA YAU BA: Farashin Kaya A Lokacin Mulkin Marigayi 'Yar'Adua Litar Fetur = Naira 65Gas = Naira 112Shinkafa = Naira 3,500Siminti = Naira 750Taki = Naira 2500Buhun Siga= Naira 7,000.Buhun Fulawa = Naira 6,050 Da sauran farashin kaya, duk babu tsada a lokacin sa, kuma ya dauko hanyoyin gyara kasa, Allah Ya dauki ransa. A yau ne dai marigayi tsohon shugaban kasan ke cika shekaru 15 da rasuwa. Gaskiya Nijeria mun yi rashin Adalin Shugaban Kasa, Ya Allah Ka haskaka kabarin Umar Musa Yar'Adua, Ka sa shi a aljannar Firdausi, Don Alfarmar Sayyidina Rasulillah. Daga Rashida Bala Suleja
Hukumar raba arziƙin ƙasa ta nemi sake duba ƴancin kashe kuɗin ƙananan hukumomi a Najeriya

Hukumar raba arziƙin ƙasa ta nemi sake duba ƴancin kashe kuɗin ƙananan hukumomi a Najeriya

Duk Labarai
Hukumar rarraba arziƙin ƙasa (RMAFC) ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba ƴancin kashe kuɗin ƙananan hukumomi 774 da yadda ake aiwatar da sabuwar dokar man fetur (PIA). Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ɗauke da sa hannun shugaban hukumar, Dr. Muhammed Shehu, da Sakatarenta, Injiniya Joseph Okechukwu Nwazeb. hukumar ta fitar da sanarwar ne bayan taron horarwar kwana uku da aka gudanar a Uyo, Jihar Akwa Ibom inda taron ya mayar da hankali kan inganta tsarin kuɗi da rarraba albarkatu a Najeriya. Sanarwar ta ce "Ya zama dole a riƙa biyan kuɗaɗen kananan hukumomi kai tsaye daga asusun tarayya ba tare da tsoma bakin gwamnatocin jihohi ba." Haka kuma, hukumar ta buƙaci a sauya Sashe na 162(2) na kundin tsarin mulki domin sanya lokaci na musamman da s...
DA DUMIDUMINSA: An Gwangwaje Mawaki Rarara Da Matarsa Aisha Humaira Da Kyautar Motoci Biyu A Katsina

DA DUMIDUMINSA: An Gwangwaje Mawaki Rarara Da Matarsa Aisha Humaira Da Kyautar Motoci Biyu A Katsina

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} DA DUMIDUMINSA: An Gwangwaje Mawaki Rarara Da Matarsa Aisha Humaira Da Kyautar Motoci Biyu A Katsina Daga Comr Nura Siniya Uwar marayun kasar Kaita Dr. Amina Musa Kaita ta baiwa Mawakin siyasa Dauda Adamu Rarara da kyautar babbar mota Coaster mai ɗaukar mutum 35, yayin da yake wake Ɗan nata Dr. Haruna Maiwada a wajen taron walimar taya murnar nadinsa a Katsina Kazalika Dr. Amina ta gwangwaje amaryarsa Aisha Humaira da mota ƙirar RAV 4 New model domin tasha amarci. A cewar D...
Gwamnonin Zamfara da Benue sun ƙalubalanci gayyatar kwamitin majalisar wakilai

Gwamnonin Zamfara da Benue sun ƙalubalanci gayyatar kwamitin majalisar wakilai

Duk Labarai
Gwamnonin jihohin Zamfara da Benue, Dauda Lawal da Hyacinth Alia, sun ƙi amincewa da gayyatar da Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafe na Majalisar Wakilai ta Tarayya ya aike musu, inda suka bayyana shakku kan halaccin gayyatar. An gayyaci gwamnonin da majalisun dokokin jihohinsu ne domin su bayyana a gaban kwamitin bisa zargin karya ƙundin tsarin mulki da kuma gazawa wajen gudanar da mulki. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na kwamitin, Chooks Oko, ya fitar Sanarwar ta bayyana cewa an tsara zaman sauraron bayanansu ne a ranar 8 ga watan Maris, inda ake sa ran za su bayar da ƙarin haske kan wasu muhimman al’amura. Daga cikin matsalolin da ake son jin bayani a kansu har da dakatar da wasu 'yan majalisar jiha da kuma taɓarɓarewar tsaro a jihohin biy...