Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana aniyar gwamnatinsa na kammala gina titin jirgin kasa daga Kano, zuwa Jigawa zuwa Katsina zuwa Maradi.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya bayyana haka a yayin da ya kaddamar da wasu ayyuka a jihar ta Katsina da gwamnatin Jihar ta aiwatar.
Shugaban kasar yace idan aka kammala wannan aiki zai taimaka wajan saukaka tafiyar mutane da safarar kaya wanda yace hakan zai rage amfani da Titi.
Hakanan shugaban kasar yace sun bayar da aikin gyaran titunan da suka hada Marabar Kankara -Dutsinma -Katsina da kuma wadanda suka hada garuruwan Zaria -Hunkuyi -Dabai da kuma wadanda suka hada garuruwan.
Hakanan shugaban kasar yace suna aiki akan titin Kano zuwa Katsina.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Anya Baffa Bichi na da hankali kuwa?
Yayi wannan tambayar ne game da ikirarin Baffa na cewa ana turawa Kwankwaso Naira Biliyan 2 duk wata.
https://twitter.com/HonAbdullahiM12/status/1919049059119014034?t=cOh5tIQ0hOwP_0-gIyNDoQ&s=19
Wannan magana dai ta jawo cece-kuce sosai a kafafen sadarwa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai gana da kamfanonin wutar lantarki dan magance matsalar bashin da kamfanonin wutar ke bi.
Ana sa ran Shugaban zai gana da kamfanonin ne inda za'a biya wani sashe na bashin da suke bi sannan sauran bashin za'a biyashi a hankali nan da watanni 6.
Hakan na zuwane bayan ganawar kamfanonin wutar da ministan wuta, Adebayo Adelabu.
Me magana da yawun Ministan, Bolaji Tunji ne ya tabbatar wa da manema labarai hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Kamfanonin wutar na fuskantar matsalar karancin kudi wanda kuma suke bin bashin Naira Tiriliyan 4.
Wannan wani dan kasada ne da ya baiwa mutane mamaki inda aka ganshi yana tsallaka Titi yayin da tawagar motocin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke wucewa.
Lamarin ya baiwa mutane mamaki inda akai ta masa Allah wadai.
https://twitter.com/abdullahayofel/status/1918913317881491890?t=Wca6Hk9N0w2YDDllnbS4lA&s=19
Wasu dai sun ce kamar baya son rayuwarsa ne.
Wani ɗan asalin jihar kano, mazaunin Faransa ya kafa sabon tarihi a fannin kimiyya.
Dr. Mubark Mahmud PhD, mai bincike kan muhalli ya ƙirƙiri sabuwar hanyar auna tsawon bishiya wanda duniyar kimiyya ta karba ta kuma raɗa wa binciken suna "Mahmud Method".
An saka a manhajar M-Tree da jami'o'i a Faransa ke amfani da ita wajen auna tsayi da kauri na bishiyoyi.
Tuni dai aka ƙaddamar a jami'ar da ya ke karatu, université Paris-Saclay a ranar 30 ga watan Afrilu.
Tuni dai aka wallafa wannan bincike a wata mujallar noma mai suna Smart Agricultural Technology Kuma za a saka shi a manhajojin koyarwa a makarantu da cibiyoyi da dama.
Hakazalika an baiyana cewa akwai shirin za a bunƙasa binciken ta hanyar saka shi a ƙirkirarriyar fasaha wato Artificial Intelligence, AI.
Zargin Biliyan biyu ga Kwankwaso: Babu hankali da lissafi a maganar Baffa Bichi - Abba Gida-Gida.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Baffa Bichi martani bisa zarge-zargen da ya fada akan gwamnatin.
A wata hira da manema labarai da ta karade kafafen watsa labarai, an jiyo Baffa Bichi, wanda aka cire shi daga muƙamin sakataren gwamnatin, na cewa an ɗauki matakin ne don ya ki amincewa da ya sahale a rika diban Naira biliyan 2 duk wata ana saka wa a asusun Rabi'u Musa Kwankwaso, jagoran Kwankwasiyya.
A wani taro da kansilolin mazaɓu 484 na jihar a yau Lahadi, gwamna Abba ya ce maganganun da Bichi ya yi "babu hankali da lissafi da aiki da ƙwaƙwalwa a wannan maganar."
A cewar gwamna Abba, babu hankali a ce gwamnatin sa da ko shekaru bi...
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatin sa ba wajen zaman ɓarayi ba ce sabo da jajircewa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.
Da ya ke jawabi a wajen taro da kansilolin mazaɓu 484 da ke gudana yanzu haka a gidan gwamnati, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatin sa ba za ta lamunci satar kudin al'umma ba.
A cewar sa, ya na jagorantar gwamnati mai tsafta da kaffa-kaffa wajen sace kudin al'umma, inda ya jaddada cewa "ɓarawo ba ya zama a gwamnatin mu,"
Ya ce wannan kokarin yaki da din hanci ne ya sanya gwamnatin ke samun makudan kuɗaɗen da ta ke ta bijiro da aiyuka domin jin dadin al'ummar Kano.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Gwamna Yusuf ya fadi hakan ne bayan da a kwanan nan tsohon sakataren gwamnatin, Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya ke zargin badakala da wawure kuɗaɗen al'...
Bayan da 'yar jarida Dr. Sandra Duru ta yiwa Sanata Natasha Akpoti Tonon Silili, inda tace sun yi waya kuma ta nadi maganar da suka yi inda Sanata Natasha Akpoti ta mata tayin Miliyan Naira 200 dan ta kalawa Sanata Godswill Akpabio sharrin cewa yana safarar sassan jikin mutane, Sanata Natasha Akpoti ta karyatata.
Natasha tace bata ma san 'yar Jaridar ba.
Saidai daga baya da aka dameta da tambaya, ta amsa cewa lambar wayar da 'yar Jaridar ta nuna sun yi magana da ita, tatace.
Watau kalaman da ake zarginta da furtawa ta furtasu.
Ko da dai Sanata Natasha Akpoti ta nace akan cewa bata furta wadancan kalamai ba, to lallai bai kamata mutane su ci gaba da yadda da maganganunta ba.
Hukumar da ke sanya ido kan farashi da kare haƙƙin masu sayen kaya ta Najeriya (FCCPC), ta ce barazanar da kamfanin Meta ya yi na ficewa daga ƙasar, ba zai hana a hukunta shi ba.
Hukumar ta ce ba za a janye shari'ar da ake yi da Meta ba duk da barazanar da ya yi.
FCCPC ta ce kamfanin ya yi barazanar ficewa daga Najeriya ne domin a ji tausayinsa, da kuma matsawa hukumar canza matakin da ya ɗauka na cin tarar kamfanin.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da darektan hukumar, Ondaje Ijagwu ya fitar ranar Asabar.
Hakan kuma na zuwa ne bayan wani gargaɗi da Meta ya yi da farko cewa "za a tilasta masa rufe shafukan Facebook da Instagram a Najeriya don kauce wa barazanar fuskantar hukunci".
Hukumar ta zargi Meta da yi wa bayanan ƴan ƙasar kutse, ciki har da aika bayanan ba tare d...