Hukumar alhazan Najeriya ta saka ranar fara kai maniyyata Saudiyya
Hukumar Alhazai ta Ƙasa a Najeriya ta sanar da kammala shirye-shirye domin soma jigilar maniyyata aikin Hajjin bana zuwa kasar Saudiyya ranar 9 ga watan Mayu.
Hukumar ta Nahcon ta sanar da hakan ne bayan wata ganawa da shugabanta da wakilan majalisar gudanarwa suka yi da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.
Mataimakin shugaban kasar ne ya gayyaci shugaban hukumar Farfesa Abdullah Saleh Usman da wakilan sashen gudanarwa zuwa ganawar a ofishinsa domin sanar da shi inda aka kwana game da shirye-shiryen aikin hajjin.
"Mun yi masa bayani game da shirye-shiryenmu a Makkah da Madina da Arafa kuma ya gamsu, har ma ya ba mu umarnin yadda za mu haɗa kanmu mu yi aikin har zuwa ƙarshensa," kamar yadda Farfesa Saleh ya shaida wa BBC.
Kazalika, shugaban ya ce suna sa ran kammala aikin k...







