Monday, February 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Yanda Zanga-zangar “Takalmin Annabi ya fi kowa” ta barke a Katsina

Kalli Yanda Zanga-zangar “Takalmin Annabi ya fi kowa” ta barke a Katsina

Duk Labarai
Daga Auwal Isa Musa Kamar yadda wakilin Jaridar Taskar Labarai taskar labarai ya aiko mana, cincirindon jama'a ne suka yi farin-dango wajen fitowa tare da bazama a kan manyan Titunan birnin Katsina da hantsin yau Asabar, domin gudanar da zanga-zanga maintaken "Takalmin Annabi ya fi kowa" Bangarorin al'ummar musulmi a jihar ta katsina, an shaida shigarsu wannan zanga-zanga wadda yanzu haka take gudana a tsanake, a yain da mahalartanta ke rera wakokin yabo ga fiyayyen halitta, musamman Takalminsa (S) da suka fito zanga-zangar nuna daraja da fifikonsa. Zanga-zangar ta taso ne taso ne daga filin Polo/kofar 'yandaka, inda ta ta nufo cikin gari.
Na Yafe Duk Wata Rashin Fahimta Da Ta Shiga Tsakanina Da Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi, Inji Gwamna Bala Mohammed yayin da yaje ta’aziyyar malamin

Na Yafe Duk Wata Rashin Fahimta Da Ta Shiga Tsakanina Da Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi, Inji Gwamna Bala Mohammed yayin da yaje ta’aziyyar malamin

Duk Labarai
Na Yafe Duk Wata Rashin Fahimta Da Ta Shiga Tsakanina Da Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi, Inji Gwamna Bala Mohammed …Malami ne mara tsoro da ya sadaukar da rayuwarsa wajen karantar da mušùĺùnçìn, wanda jihar Bauchi za ta yi kewarsa …ya ku mallakawa Almajiransa filin game village Daga Rariya A yammacin yau Abasar ne Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya kai ziyarar ta'aziyyar rasuwar Sheik Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ga iyalansa da mabiyansa, wanda ya rasu a daren Juma'ar da ta gabata. Gwamna Bala wanda ya jagoranci tawagar mukarraban gwamnati, ya kai ziyarar ta'aziyyar ne a madadin kansa, iyalansa, gwamnati da kuma daukacin al'ummar jihar Bauchi. Gwamnan ya bayyana marigayi Shehin Malamin a matsayin malamin mara tsoro wanda ya sadaukar da kansa waj...
Bashin da ake bin Najeriya ya karu sosai

Bashin da ake bin Najeriya ya karu sosai

Duk Labarai
Bashin da ake bin Nijeriya ya haura zuwa tiriliyan N144.67 a 2024 - Rahoton DMO Ofishin kula da basussuka na Nijeriya ya ce bashin da ake bin Najeriya ya karu da naira tiriliyan N47.32tn, wanda ya nuna karuwar kashi 48.58 cikin 100 daga Disamba 2023 zuwa Disamba 2024. Sabon rahoton da aka fitar a wannan Juma’a, ya nuna cewa an samu karuwar cin bashi daga kasashen waje da kuma cikin gida, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
An min Wahayi cewa nan gaba a saman wata da kuke gani a sama zamu je mu yi zaman taro>>Inji Pastor Enoch Adeboye

An min Wahayi cewa nan gaba a saman wata da kuke gani a sama zamu je mu yi zaman taro>>Inji Pastor Enoch Adeboye

Duk Labarai
Babban Malamin kirista, Pastor Enoch Adeboye ya bayyana cewa, an masa wahayi cewa, nan gaba a saman wata za'a je a gudanar da taron cocinsa. Faston ya bayyanawa mabiyansa hakane yayin da yake musu wa'azi. Saidai yace lamarin Allah akwai ban mamaki amma ba lalai bane sai mutane sun yarda ba. Lamarin dai ya baiwa mutane da yawa, ciki hadda kiristoci mamaki.
Kalli matashi me digiri na 3 watau Ph. D da ke aikin goge-goge ana biyanshi Albashin Naira Dubu 70

Kalli matashi me digiri na 3 watau Ph. D da ke aikin goge-goge ana biyanshi Albashin Naira Dubu 70

Duk Labarai
Wannan wani mutum ne a jami'ar jihar Ebonyi me suna Dr. Enyi onyebuchi Paul wanda a shekarar 2007 ya samu aikin goge-goge a makarantar. Saidai ya jajirce inda ya ci gaba da karatu har ya samu Digiri na daya zuwa na 3 a makarantar. Saidai duk da wannan kokari da yayi, ba'a mayar dashi malami me koyarwa ba a jami'ar. An ci gaba da barinsa a matsayin me goge-goge inda ake biyansa Albashin Naira Dubu 70. An dai yi zargin saboda bashi da kafa ne shiyasa ya kasa samun aikin koyarwa a makarantar.
Matashi Ba Taliya Ko Ƴan Kuɗi Yake Buƙata Daga Wajen Ƴan Siyasa Ba Face A Gina Rayuwarsa-Inji Sanata Ahmad Babba Kaita

Matashi Ba Taliya Ko Ƴan Kuɗi Yake Buƙata Daga Wajen Ƴan Siyasa Ba Face A Gina Rayuwarsa-Inji Sanata Ahmad Babba Kaita

Duk Labarai
Daga Comr Nura Siniya Tsohon Sanata mai wakiltar shiyyar Daura a jihar Katsina Sen. Ahmad Babba Kaita, ya bayyana cewa matashin Najeriya ba Taliya ko 'yan kudi yake bukata daga wajen 'yan siyasa face a gina rayuwarsa don gobensa ta yi kyau. A cewar sa, Sanata Kaita rayuwar matasa a Najeriya ba za ta inganta da taliya ko kyautar naira daga hannun ‘yan siyasa ba. Ya kuma ce abubuwan da matasa ke buƙata da gaske sune: tsaro mai kyau, ingantaccen ilimi da kuma samun aikin yi ko sana'ar dogaro da kai. Sanatan ya jaddada cewa waɗannan ginshiƙai su ne tushen da ya gina siyasarsa a kai, kuma yana fatan ci gaba da bin wannan hanya don ganin rayuwar matasa A ƙarshe ya ce Ina siyasa ne don a gina rayuwar matasa. Ba wai domin jama’a su sa ni a dama da su ba. Ina fatan ganin matasan Najeriy...
An gayyaci Sanata Shehu Sani ya shiga cikin wadanda zasu yi Alkalancin budurwar da zata lashe sarauniyar kyau a Najeriya amma yace baya so dan ko tsakanin matansa bai iya yin alkalancin wadda tafi kyau ba

An gayyaci Sanata Shehu Sani ya shiga cikin wadanda zasu yi Alkalancin budurwar da zata lashe sarauniyar kyau a Najeriya amma yace baya so dan ko tsakanin matansa bai iya yin alkalancin wadda tafi kyau ba

Duk Labarai
An gayyaci tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya shiga cikin Alkalan da zasu yanke hukunci kan wadda zata lashe gasar Sarauniyar kyau ta Najeriya amma yace baya so. Tsohon sanata, Ben Bruce ne ya shirya wannan lamari wanda zai wakana a Otal din Federal Palace Hotel dake Legas. Sannan ya gayyaci Sanata Shehu Sani ya zama cikin Alkalai. Saidai a sanarwar da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta, Sanata Shehu Sani yace baya son wannan gayyata kuma ba zai iya ba. Yace matansa ba zasu ji dadi ba idan yayi wannan alkalanci saboda ko a tsakaninsu bai iya fitar da wadda ta fi wata kyau ba dan haka ba zai iya alkalanci akan matan da bai sani ba. Saidai yace ya gode da wannan gayyata da aka masa.
Ministan ilimin Najeriya na so a faɗaɗa shirin NYSC zuwa shekara biyu

Ministan ilimin Najeriya na so a faɗaɗa shirin NYSC zuwa shekara biyu

Duk Labarai
Ministan ilimi na Najeriya, Olatunji Alausa ya yi kira da a faɗaɗa shirin yi wa ƙasa hidima, NYSC daga shekara ɗaya zuwa shekara biyu. Mista Alausa ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wa babban daraktan hukumar, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ziyara a ofishinsa ranar Juma'a. Haka kuma ministan ya buƙaci a faɗaɗa tare da inganta shirin koya wa masu yi wa ƙasa hidima sana'o'i. Minista ya kuma yaba wa ayyukan hukumar NYSC, musamman wajen tantance tare da gano matasan da suka je sansanonin NYSC da takardun kammala karatu na bogi. Ya kuma ce ma'aikatarsa za ta ci gaba da aiki tare da da hukumar wajen inganta harkokin ilimi a faɗin ƙasar. Mista Alausa ya kuma yi kira da a riƙa tura masu yi wa ƙasa hidima domin koyarwa a makarantun ƙauyuka da karkara, domin cike giɓin malaman da ...