Sheikh Kabiru Gombe Ya Tara Wa Marayu Zunzurutun Kuɗi Har Naira Miliyan 67.
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Sheikh Muhammad Kabir Gombe, Ya Tara Wa Marayu Zunzurutun Kuɗi Har Naira Miliyan 67 Inda Ya Ke Karatun Tafsirin Al-Quran Maigirma, Cikin Wannan Watan Azumin Ramadana A Masallacin Helkwatar Ƙungiyar Izala Dake Unguwar Utako, Birnin Tarayya, Abuja, Cewar Shugaban Ƙungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau
Daga Jamilu Dabawa
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIN RAJI'UN:
Mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina ta rasu.
Allah ya yima Hajiya Safara'u rasuwa yanzu, da asubahin yau lahadi 23/3/2025, mahaifiyar mai girma Gwamnan Malam Dikko Umar Radda PhD CON. Allah ya gafarta mata yasa Aljanna fiddausi ce ce makomar ta. Idan ajalinmu yazo Allah yasa mu cika da imani.
Mun samu rahoton rasuwar mahaifiyar Gwamnan daga daya daga cikin jikokin marigayiyar.
Rahotanni sun bayyana cewa, Dalibai daga jami'ar Harvard ta kasar Amurka wadda kusan itace ta daya a Duniya kuma shuwagabannin kasar Amurkar da yawa irin su Obama can suka yi karatu sun zo matatar man fetur ta Dangote sanin makamar aiki.
An ga daliban ana kewayawa dasu inda suke shiga lungu da sako na matatar dan ganin yanda take aiki.
Rahotanni sun bayyana cewa, Darajar Naira ta yi rugu-rugu a kasuwar Chanji.
A wani bincike na tsanaki da aka yi, an gano cewa, Nairar ta fadi a tsakanin 14 zuwa 21 na watan Maris na shekarar 2025.
Sannan a kowane sati tana rasa darajar Akalla Naira 18.96.
A ranar Juma'ar data gabata, an kulle kasuwar Chanji Naira na da farashin N1,536.89.
Wannan a kasuwar Gwamnati kenan.
Saidai a kasuwar bayan fage, an kulle kasuwar Naira na da farashin N1,580 akan kowace dala.
Wannan bayanai duka an samosu ne daga bayanan canjin kudi daga rubun ajiyar bayanai na babban bankin Najeriya, CBN.
Wannan wasu masu garkuwa da mutanene da suka harbi wani mutum a kafa.
Lamarin ya baiwa mutane takaici inda akai ta Allah wadai dasu.
Kalli bidiyon anan
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa babu wata haɗakar ‘yan siyasa da za ta iya sauke Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
Matsayar Shekarau na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, suka soki matsayar Gwamnatin Tarayya game da rikicin siyasa a Jihar Ribas a wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja.
A wata sanarwa da Dr. Sule Yau ya fitar a madadin Shekarau, ya jaddada cewa, sabanin abin da wasu ke hasashe, wannan haɗaka kawai wata tarayya ce ta masu niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa, ku...
Sarki Alhaji Aminu ado Bayero Na 15 ya sanar da Hawan Sallah a bikin sallah mai zuwa kamar dai Yadda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi Lamido Na ll ya sanar shima
Me zaku ce?
Rahotanni sun bayyana cewa an kama dansanda da soja bisa zargin satar batura mallakin hukumar kula da jirgin kasa na Najeriya.
Dansandan da aka kama me suna Akowe Joel na da mukamin Inspector.
Daga cikin wadanda aka kama hadda jami'in hukumar dake kula da jiragen kasa na Najeriya.
Hukumar 'yansandan ta tabbatar da hakan.
Babbar Kotun tarayya dake Lokoja ta amince a shiryawa sanata Natasha Akpoti kiranye.
Kotun tace mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti suna da 'yancin yi mata kiranye kamar yanda kundin tsarin mulki ya basu dama.
Kotun tace mutanen mazabar zasu iya ci gaba da gudanar da zaben kiranyen da suke shiryawa Sanata Natasha Akpoti amma su bi doka da oda wajan yin hakan.
Kotun ta bayyana hakane bayan da a ranar Alhamis tace a dakata da maganar yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye.