Thursday, March 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ashe shima Godswill Akpabio ya taba sukar Bukola Saraki bayan da ya canja mai kujerar zama kamar yanda a yanzu fadanshi da Sanata Natasha Akpoti ya samo Asali ne daga canja mata kujera

Ashe shima Godswill Akpabio ya taba sukar Bukola Saraki bayan da ya canja mai kujerar zama kamar yanda a yanzu fadanshi da Sanata Natasha Akpoti ya samo Asali ne daga canja mata kujera

Duk Labarai
Rahotanni na tuna baya sun nuna cewa a lokacin tsohon kakakin majalisar Dattijai, Bukola Saraki, sun samu tirka-tirka da kakakin majalisa na yanzu, Sanata Godswill Akpabio kan maganar canja masa kujera. A wancan lokacin, Sanata Godswill Akpabio ya nemi yayi magana da lasifikar dake kujerar sanata Ali Ndume amma Sanata Bukola Saraki ya hanashi inda yace ya koma kan wata kujera da ya canja masa wadda lasifikarta na aiki. Saidai hakan ya jawo cece-kuce a majalisar inda a wancan lokacin aka zargi Bukola Saraki da aikata rashin Adalci. A wannan karin ma, abinda ya jawo cece-kuce tsakanin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti shine canja mata kujerar zama da kuma canja mata kwamiti.
Ka daina batawa Mahaifin mu suna>>’Ya’yan Abacha suka gargadi IBB

Ka daina batawa Mahaifin mu suna>>’Ya’yan Abacha suka gargadi IBB

Duk Labarai
'ya'yan Marigayi Janar Sani Abacha sun gargadi tsohon shugaban kasar, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB cewa ya daina batawa mahaifinsu suna. Sanarwar wadda daya daga cikin 'ya'yan Sani Abachan, Muhammad Abacha ya fitar tace IBB ya zargi cewa Abacha da cewa shine yayi sanadiyyar soke zaben zaben Abiola. Saidai sanarwar tace wannan ikirari na IBB ba gaskiya bane, duk da yake cewa, Abacha babba ne a gwamnatin IBB din amma IBB din shine shugaban kasa. A karshe dai sun gargadi IBB din da ya daina batawa babbansu suna.
Na yi aiki da mata kyawawa masu yawa babu wadda ta taba cewa na nemeta sai Sanata Natasha Akpoti, dadin abin ba ni kadai ta taba kalawa sharri ba>>Sanata Godswill Akpabio

Na yi aiki da mata kyawawa masu yawa babu wadda ta taba cewa na nemeta sai Sanata Natasha Akpoti, dadin abin ba ni kadai ta taba kalawa sharri ba>>Sanata Godswill Akpabio

Duk Labarai
Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa, Akwai mata da yawa kyawawa da yayi aiki dasu amma babu wadda ta taba zarginsa da neman yin lalata da ita sai Sanata Natasha Akpoti. Ya bayyana hakane a wajan taron ranar mata ta Duniya. Sanata Akpabio yace zargin da Sanata Natasha Akpoti ta yi masa ya girgiza Majalisar inda yace abin ya basu mamaki. Yace amma dadin abin bashi kadai ne ta taba yiwa irin wannan sharri ba da kuma ta kasa kawo shaida. Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ma ya zargi Sanata Natasha Akpoti da cewa shima ta taba kala masa sharrin yin lalata da ita amma daga baya aka gano karyane.
Karya ake mana, bamu ce muna goyon bayan Peter Obi da El-Rufai su yi takarar shugaban kasa a shekarar 2027 ba>>Inji Gwamnonin PDP

Karya ake mana, bamu ce muna goyon bayan Peter Obi da El-Rufai su yi takarar shugaban kasa a shekarar 2027 ba>>Inji Gwamnonin PDP

Duk Labarai
Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun musanta jita-jitar da ke cewa wasu daga cikinsu Guda biyar na Goyon bayan tikitin El-Rufai/Obi a zaɓen 2027. Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Darakta Janar na ƙungiyar, Dakta Emmanuel Agbo, ya fitar a madadinsa a yau Asabar. Ya ce, “Wajibi ne a gare mu a matsayin ƙungiyar Gwamnonin PDP, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, mu fito mu karyata, kuma mu yi Allah-wadai da wadannan jita-jita marasa tushe da wasu ‘yan siyasa masu son zuciya ke yayatawa. Su ne dai ba za su iya jure irin kokarin da muke yi don nuna gazawarsu a shugabanci ba, wanda ya jefa ‘yan Najeriya cikin fatara da tsananin wahala.” “A saboda haka, ƙungiyar gwamnonin PDP ba ta d...
Tinubu da mukarrabansa sun kashe Naira Biliyan 1.9 wajan tafiye-Tafiye zuwa kasar Faransa

Tinubu da mukarrabansa sun kashe Naira Biliyan 1.9 wajan tafiye-Tafiye zuwa kasar Faransa

Duk Labarai
Manyan ma'aikatun Gwamnati da suka hada da fadar shugaban kasa sun kashe Naira Biliyan 1.9 wajan tafiye-Tafiye da horas wa a kasar Faransa. Hakan ya farune a tsakanin Watan May 2023 zuwa September na 2024. Wasu kungiyoyi masu zaman kansu da ke saka idanu kan yanda ake kashe kudin Gwamnati GovSpend ne suka gudanar da wannan bincike. Kudin dai an kashesu ne akan kudin jirgi, dana Otal, dana abinci dana horaswa da sauransu. Rahoton yace yawancin kudin an kashesu ne a wajan ayyukan horaswa.
Doyin Okupe ya hango mutuwarsa tun kamin ta zo, yana sane da cewa ya kusa mutuwa dan ya gaya mana>>Inji Daya daga cikin yaransa

Doyin Okupe ya hango mutuwarsa tun kamin ta zo, yana sane da cewa ya kusa mutuwa dan ya gaya mana>>Inji Daya daga cikin yaransa

Duk Labarai
Daya daga cikn yaran tsohon hadimin shugaban kasa da ya mutu, watau Doyin Okupe ya bayyana cewa, Yasan zai mutu an ya hango mutuwar tasa. Mutumin me suna Jack ya bayyana Doyin Okupe a matsayin uba kuma haziki sannan jajirtaccen mutum. Yace dukan alamu sun nuna cewa ya hango mutuwarsa dan kuwa a shekarar data gabata ya tara na kusa dashi ya shirya musu liyafar cin abincin dare inda yace itace ta karshe.
Labari Me Dadi: Najeriya ta samu kudin shiga da suka kai Naira Tiriliyan 13.78 daga sayar da Danyen man

Labari Me Dadi: Najeriya ta samu kudin shiga da suka kai Naira Tiriliyan 13.78 daga sayar da Danyen man

Duk Labarai
Hukumar kididdiga ta kasa, NBS tace Najeriya ta samu kudin ahiga da suka kai Naira Tiriliyan 13.78 daga sayar da danyen man fetur a watanni 3 na karshen shekarar 2024 data gabata. A sanarwar da suka fitar sun ce Najeriya ta kuma samu kudin shiga daga harkokin da ba na man fetur ba da suka kai Naira Tiriliyan 2.8 da kuma Naira Tiriliyan 6.2. !Hakanan hukumar tace har yanzu dai abinda Najeriya ta fi fitarwa dan sayarwa da samun kudin shiga daga kasashen Duniya danyen man fetur ne wanda ke wakiltar kaso 68.87 cikin 100 na kudin shigar gwamnatin.
Duk da an rage farashin Man Fetur, mu ba zamu iya rage farashin daukar mutane ba>>Kungiyar Masu motocin haya

Duk da an rage farashin Man Fetur, mu ba zamu iya rage farashin daukar mutane ba>>Kungiyar Masu motocin haya

Duk Labarai
Kungiyar masu sana'ar tuka motocin haya, (NURTW) ta bayyana cewa, rage farashin Man fetur ba zai sa su rage farashin da suke daukar fasinja ba. Sakataren Kungiyar na jihar Kano, Yushu’a Haruna ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da jaridar Leadership. Ya bayyana cewa, duk da yake an rage farashin man fetur amma ba shi kadai ne suke kashe kudi wajan amfani da mitar ba, yace farashin taya ya karu hakanan farashin motar kanta ba sauka yayi ba. Dan haka yace ba zasu rafe farashin daukar mutane ba. Hakanan Takwaransa na kungiyar NARTO, Ado Inuwa Yakasai shima ya tabbatar da wannan magana inda yace tabbas an rage farashin man fetur amma na sauran kayan mota bai ragu ba. Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur din daga 860 zuwa 825.
Kalli: Sanata Shehu Sani ya sha raddi a wajan Kiristoci inda suka rika tambayarshi kana Azumi kuwa bayan da yayi comment a kasan wani bidiyon da ake nuna tsìràìcì mata Tsìràra suna rawa

Kalli: Sanata Shehu Sani ya sha raddi a wajan Kiristoci inda suka rika tambayarshi kana Azumi kuwa bayan da yayi comment a kasan wani bidiyon da ake nuna tsìràìcì mata Tsìràra suna rawa

Duk Labarai
Sanata shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai a shekarar 2015 zuwa 2019 ya sha raddi a kafar X. An wallafa wani Bidiyo ne inda aka nuna mata tsirara daga su sai dan kamfai a wani shagon Aski da aka ce a Najeriya yake auna rawa. Da yake bayyana ra'ayinsa akan bidiyon, sanata Shehu Sani yace ka zo Najeriya zaka ga abubuwan ban mamaki. Saidai da yawa sun yi mamakin ganin comment dinsa a kasan Bidiyon ganin cewa bidiyon na dauke da tsiraici. Da yawa sun rika tambayar anya Sanata Shehu Sani na Azumin kuwa? Kalli Bidiyon anan: