Friday, February 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Gwamnatin jihar Sokoto ta fara biyan malaman firamare mafi ƙanƙantar albashi

Gwamnatin jihar Sokoto ta fara biyan malaman firamare mafi ƙanƙantar albashi

Duk Labarai
Makonni uku bayan wani rahoton da BBC ta yi game da ƙorafin da malaman makarantun firamaren jihar Sokoto suka yi na rashin biyansu sabon albashi mafi ƙanƙanta na naira 70,000, gwamnatin jihar ta biya su, har ma da yi musu ƙari. Malaman makarantun firamaren sun shaida wa BBC irin farin cikin da suka ji game da alƙawarin da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya cika, na biyansu sabon albashin kamar kowa tare da sauran ma’aikatan gwamnatin jihar da suka hada da na kananan hukumomi 23. Mai magana da yawun gwamnan jihar, Abubakar Bawa, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ta saurari ƙorafin da ma’aikatan suka yi ne, shi ya sa ta cika alƙawarin da ta ɗaukar musu tun da farko. A watan Yulin shekarar 2024 ne, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da ƙara albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan ƙasar dag...
Mutum huɗu sun mutu goma sun ji rauni a wata motar bas da ta ƙone a jihar Jigawa

Mutum huɗu sun mutu goma sun ji rauni a wata motar bas da ta ƙone a jihar Jigawa

Duk Labarai
Mutane huɗu sun ƙone ƙurmus wasu goma kuma sun ji raunuka yayin da wata mota ƙirar bas (Hummer) ta kama da wuta a garin Gwaram da ke jihar Jigawa. Lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 4 na yamma, a jiya Asabar a kusa da makarantar sakanadare ta haɗaka ta gwamnati ta 'yammata da ke garin na Gwaram (Government Girls Unity Secondary School ) Wata sanarwa da kakakin 'yansanda na jihar SP Lawan Adam ya fitar a yau Lahadi ta nuna cewa motar ta tashi ne daga ƙaramar hukumar Zaki ta jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke ƙaramar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa. Sanarwar ta ce, ''motar na ɗauke ne da fasinja 44, da suka haɗa da manya 25 da yara 19.'' Kakakin 'yansandan ya ce, wutar ta kama ne sakamakon katifa da aka ɗaure a bayan motar da ke kusa da salansa. Sanarwar ta ƙara da cewa ...
Minista ya yi barazanar barin APC idan ba a sauya shugabancinta na Kano ba

Minista ya yi barazanar barin APC idan ba a sauya shugabancinta na Kano ba

Duk Labarai
Minista a ma'aikatar gidaje, Yusuf Abdullahi Ata ya yi barazanar cewa shi da magoyansa za su iya ficewa daga jam'iyyar APC a Kano, matuƙar ba a canja shugabancin jam'iyyar a jihar ba. Ministan ya ce furucin jagoran jam'iyyar ne ya jawo faɗuwar jam'iyyar a zaɓen da ya gabata na 2023, kamar yadda ya bayyana a wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafofin sadarwa, wanda aka ce ya yi a taron masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumarsa ta Fage a jihar Kano. Ata ya ce, “muna faɗa wa kowa, idan aka mayar da irinsu, duk irinmu fita za mu yi." Ya ƙara da cewa, "mu an mana tarbiya, mun san waye malami, mun san waye babba. Saboda haka ba za mu sauka daga turbarmu ba. Idan suka dawo da shi, mu za mu fita, kuma na rantse da Allah sai jam'iyyar ta sake faɗi zaɓe," in ji shi. "Dole a canja, dole a nemo...
Zan iya sauka daga mulki idan hakan zai sa a samu zaman Lafiya>>Inji Shugaban kasar Ukraine

Zan iya sauka daga mulki idan hakan zai sa a samu zaman Lafiya>>Inji Shugaban kasar Ukraine

Duk Labarai
Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya haƙura da kujerar shugabancin ƙasar idan haka ne zai zama silar samar da zaman lafiya a ƙasarsa. Zelensky ya bayyana haka ne a daidai lokacin da aka cika shekara uku ana gwabza yaƙi tsakanin Ukraine da Rasha. "Idan kuna so in sauka daga mulki, zan amince. Amma ina so ƙasata ta shiga ƙungiyar Nato," in ji shi a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani taron manema labarai. Wannan jawabin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya kira shi da "mai kama-karyar mulki ba tare da zaɓe ba." "Maganarsa ba ta ɓata min tai ba," in ji Zelensky wanda aka zaɓa a watan Mayun shekarar 2029. Zelensky ya ƙara da cewa tabbatar da zaman lafiyae ƙasar ne a gaban shi, amma ba ya tunanin daɗewa a mulkin ƙasar...
Yanda na hadu da matata na musuluntar da ita>>Tsohon Shugaban kasa, IBB yayi bayani dalla-dalla

Yanda na hadu da matata na musuluntar da ita>>Tsohon Shugaban kasa, IBB yayi bayani dalla-dalla

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB ya bayar da labarin yanda ya hadu da matarsa Maryam a cikin littafin tarihin rayuwarsa. Babbangida yace asalin sunan matarsa shine Maria Okogwu kamin daga baya ta musulunta ta koma Maryam. yace sun dade suna abuta kamin ya aureta. Yace babban dalilin da yasa yayi aure shine an taba harbinsa a kirji aka kwantar dashi a gadon Asibiti a Legas, anan ne yayi tunanin cewa ya kamata ace yayi aure. Yace yana kan gadon Asibiti ya rika tunanin irin 'yan matan da yake dasu da kuma da wacece cikinsu ya kamata ace yayi rayuwa a matsayin matarsa? Yace anan tunanin Maryam ya fado masa, yace a lokacin tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon shima ya auri matarsa, Victoria inda abin ya kara karfafa masa gwiwa. Yace yan...
Yan Nigeria Basu iya Tattali Ba Amma N8,000 zata iya canza rayuwar matashi Wanda yasan meya keyi – Inji Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shattima

Yan Nigeria Basu iya Tattali Ba Amma N8,000 zata iya canza rayuwar matashi Wanda yasan meya keyi – Inji Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shattima

Duk Labarai
Yan Nigeria Basu iya Tattali Ba Amma N8,000 zata iya canza rayuwar matashi Wanda yasan meya keyi - Inji Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shattima DAGA Wakiliya ) Mataimakin shugaban ƙasa yace indai matashi zaiyi anfani dashi yadda ya dace, To Indai Allah yasamai arbarka cikin Shekara 1yr zai Tara abunda yafi karfi 100k. Misali: Akwai kananun sana'a kamar su sana'ar Shoe Shiner, Saida Data, Saida Katin Waya, Saida Touch Light dadai sauransu, Wanda a maneji 8k zata ishi mutum ya fara, Kuma Idan Allah yasama Abun Arbarka, A Shekara ba karamun kudi zai Tara ba, Kenan 8k ta canza rayuwarsa, Ya kuma barranta daga Rokon mutane, Balle kuma 8k din ba sau daya za'aba mutum ba. Akwai iyayenmu mata a Gida da suke Dan Saida daddawa, Magi, Gullisuwa, Tuwon Madara dadai sauran kayan makwalash...
‘Yan Najeriya, Ghana, China, da India ne suka bace aka rasa inda suke bayan da suka shiga kasar Canada da cewar sun je yin karatune

‘Yan Najeriya, Ghana, China, da India ne suka bace aka rasa inda suke bayan da suka shiga kasar Canada da cewar sun je yin karatune

Duk Labarai
Wani rahoto ya bayyana cewa akalla dalibai dubu 50 ne suka bace aka rasa inda suke bayan da suka shiga kasar Canada da sunan yin karatu. Daiban sun fito ne daga kasashen Duniya daban-daban wa da suka hada da kasar India da dalibai 19,582 suka shiga kasar ta Canada amma suka ki zuwa su yi rijistar fara karatu aka rasa inda suke, me biye mata itace kasar China dake da dalibai 4,279 da suma bayan shiga kasar Canada da sunan karatu suka bace, kasa ta uku itace Najeriya dake da dalibai 3,902 wanda suma sun shiga kasar Canada da sunan yin karatu amma sun bace, kasa ta gaba itace kasar Ghana itama dalibanta sun isa kasar Canada da sunan yin karatu amma suka bace. Daliban dai sun shiga kasar Canada ne a tsakanin watannin Maris zuwa Afrilu. Rahoton yace wasu daliban yaudararsu aka yi inda ...
A biyamu diyyar Tiriliyan 10 sannan a bamu hakuri, Inyamurai suka gayawa shugaba Tinubu game da maganar kazafin da aka musu na cewa sune suka shirya juyin mulki na farko amma IBB ya wankesu

A biyamu diyyar Tiriliyan 10 sannan a bamu hakuri, Inyamurai suka gayawa shugaba Tinubu game da maganar kazafin da aka musu na cewa sune suka shirya juyin mulki na farko amma IBB ya wankesu

Duk Labarai
Biyo bayan abinda Tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana na cewa, Juyin Mulkin da aka shrirya na shekarar 1966 ba na Inyamurai bane, Kungiyar kare muradin Inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta nemi a biyata diyyar asarar da aka mata. Kungiyar ta nemi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bata hakuri sannan a biyasu diyyar Naira Tiriliyan 10. Kungiyar tace lamarin ya jefa Al'ummar Inyamurai cikin wahala wanda ta kai ga yakin Biafra. Kungiyar tace an yi mata asara sosai inda aka kashe mata mutane miliyan 3 ciki hadda yara kanana da mata, kungiyar tace kuma har yanzu abin yana damun inyamurai. Kungiyar tace dan haka suna neman shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a madadin gwamnatin data gabata, musamman ta Yakubu Gowon da ya basu hakuri kan lamarin. Sun kara da...
An kama mutane 3 a jihar Naija saboda baiwa me ciki Naira Miliyan 30 dan ta yadda su cire cikinta me watanni 6 dan yin tsafi

An kama mutane 3 a jihar Naija saboda baiwa me ciki Naira Miliyan 30 dan ta yadda su cire cikinta me watanni 6 dan yin tsafi

Duk Labarai
Hukumar 'yansanda ta jihar Naija ta sanar da kama mutane 3 bisa zargin siyan ciki wata 6 dan yin amfani dashi wajan tsafi. Kakakin 'yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace wadanda ake zargin sun baiwa matar Naira Miliyan 30 dan ta yadda su cire cikin nata. Yace a ranar 17 ga watan Fabrairu ne suka kama mutanen masu sunan Martha Andrew, James Luka da Johnson John wadanda duka sun fito ne daga Minna. Yace an kamasu ne a yayin da suke kokarin daukar matar me ciki daga garin Rafin-Yashi zuwa ga wani mutum me suna Gbege, saidai mutumin tuni ya tsere. Yace an kama mutanen ne a wani Otal dake Minna kuma duka sun amsa laifukansu sannan a yanzu ana kan kokarin kama Gbege wanda ya tsere.