YANZU-YANZU: El-Rufai da Peter Obi Sun Tattauna a Gefen Taron Cambridge Africa Together a Birtaniya.
An hango tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, na tattaunawa da ɗan takarar Shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, a gefen taron shekara-shekara karo na 11 na Cambridge Africa Together Conference (ATC), wanda ke gudana a Jami’ar Cambridge, ƙasar Birtaniya.
Taron, wanda ke ɗaya daga cikin manyan taruka da ke haɗa shugabanni, masana da matasa daga sassa daban-daban na nahiyar Afirka da duniya, ya kasance dandali na musayar ra’ayoyi, tattaunawa kan ci gaban Afirka, shugabanci da sabbin dabaru na magance matsalolin da ke fuskantar nahiyar.
El-Rufai da Peter Obi, wadanda dukkansu sanannu ne a harkar siyasar Najeriya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen ...
Gwamnoni da sarakunan Arewa sun yabawa ƙoƙarin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na kawo ƙarshen matsalar tsaro da samar da ayyukan raya ƙasa a Arewa.
Shugabannin sun bayyana haka ne a jawabin bayan taron da suka gabatar yau Asabar a fadar gwamnatin jihar Kaduna.
Jami'ar kimiyya da Fasaha ta Aiko Ɗangote ta karrama sanata Rabi'u Kwankwaso da digirin girmamawa.
Rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso shi ne wanda ya assasa wannan jami'ar tun a zamanin da yake gwamnan jihar Kano, daga shekarar 1999 zuwa 2003.
HOTO-: Saifullahi Hassan
Gwamnonin arewa da kuma sarakunan gargajiya na gudanar da taro a Kaduna, domin tattaunawa kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi yankin.
Taron wanda ke gudana a gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, zai kuma tattauna kan matsalar talauci da yaran da ba su zuwa makaranta da kuma sauran al'amura da suke damun yankin.
Gwamnonin jihohin Zamfara da Kebbi da Gombe da Neja da kuma Zamfara na cikin waɗanda ke halartar taron.
A ɓangaren sarakunan gargajiya kuma akwai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III da Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli da Etsu na Nupe da Sarkin Zamfara da Sarkin Bauchi da Sarkin Ilorin da Sarkin Keffi da sauransu.
Haziƙin Matashi Ya Kammala Digirinsa Da Sakamako Mafi Kyau A Bangaren Kimiyya A Jami'ar Aliko Dangote Dake Wudil
Muhammad Abubakar Ɗan Haya kenan dalibin da ya zama gwarzo a bangon karatu na shekarar 21/22, inda ya fita da sakamako mafi daraja a fannin kimiyya (Engineering) jami'ar Aliko Dangote dake Wudil.
Abubakar ɗan Haya, ya fito daga ƙaramar hukumar Birnin-Kudu dake jihar Jigawa.
Daga Abubakar Shehu Dokoki
Hukumar alhazan Najeriya ta ce ya zuwa ranar misalin ƙarfe 8:02 ta yi jigilar maniyyata 2,006 zuwa ƙasa mai tsarki.
Hukumar ta bayyana a shafinta na X cewa jirgin MaxAir ya tashi daga birnin Bauchi zuwa Madina, inda ya kwashi maniyyata 384 da kuma jami'i guda ɗaya.
Wannan dai shi ne cikamakin jirgi na biyar da suka yi jigilar maniyyatan daga ranar da aka ƙaddamar da jigilar wato ranar Juma'a.
Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya soki ƴan siyasar da ke sauya sheƙa bayan sun gama cin moriyar jam'iyyar, abin da ya bayyana da babban kuskure a siyasance.
Sanata Kwankwaso wanda ya bayyana hakan a Kano lokacin da yake karɓar wasu ƴan siyasar da suka sauya sheƙa zuwa NNPP daga ƙaramar hukumar Takai, a gidansa da ke Miller road a birnin Kano.
A baya-bayan nan ne dai raɗe-raɗi suka yi ta yawo cewa Kwankwason zai koma jam'iyya mai mulki ta APC.
Rabi'u Kwankwaso ya ƙara jaddada irin juriya da haɗin kai da ke tafiyar Kwankwasiyya duk kuwa da cewa an ta ƙoƙarin ganin an kawar da hankalin mabiya.