Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli bidiyo: Yanda Wata Nurse ta yankewa likita Azzakarinsa yayin da yayi yunkurin yi mata fyade

Kalli bidiyo: Yanda Wata Nurse ta yankewa likita Azzakarinsa yayin da yayi yunkurin yi mata fyade

Duk Labarai
Wata ma'aikaciyar Jinya,Nurse dake aiki a wani Asibiti dake Bihar me suna RBS Health Care Centre ta gamu da barazanar fyade. https://www.youtube.com/watch?v=hzBaAm1qLmM?si=0YtpIarh3h_63I4R Likitan Asibitin da take aiki da wasu 3 ne suka so yi mata fyade amma basu yi nasara ba. Likitan me suna Dr Sanjay Kumar da abokan aikinsa, Sunil Kumar Gupta da Awadhesh Kumar ne suka aha giya suka yi mankas. Suka kulle kofofin shiga Asibitin inda suka afka mata. Nan dai Allah ya bata sa'a ta kama azzakarin babban likitan ta yanke da wukar fida. Ta samu ta fita da gudu kamar yanda kafar Livemint ta ruwaito. Ta samu wani waje ta labe inda ta kira 'Yansanda suka zo suka kama likitocin. Likitan dai yana can yana karbar kulawa ta musamman inda ake ci gaba da bincike.
Matar shugaban kasa,Remi Tinubu ta kashe Naira Miliyan Dari bakwai wajan yawon zuwa kasashen Duniya a cikin watanni 3 kacal

Matar shugaban kasa,Remi Tinubu ta kashe Naira Miliyan Dari bakwai wajan yawon zuwa kasashen Duniya a cikin watanni 3 kacal

Duk Labarai
Matar Shugaban kasa,Remi Tinubu ta kashe Naira Miliyan 701 a zagayen da ta yi a kasashen Duniya guda 5. Ko da a shekarar 2023 sai da fadar shugaban kasa ta warewa ofishin matar shugaban kasar Naira Biliyan 1.5 dan saya mata motoci na Alfarma. An gano hakanne a kundin tattara bayanai na gwamnatin tarayya na yanar gizo. Bayan wannan kuma, Gwamnatin ta kashewa Matar shugaban kasar Naira Miliyan 314 wajan shirya taruka a cikin gida Najeriya.
Tinubu zai dawo Najeriya bayan ziyarar da ya kai kasashen China, UAE da Ingila

Tinubu zai dawo Najeriya bayan ziyarar da ya kai kasashen China, UAE da Ingila

labaran tinubu ayau
A yau,Lahadi ne shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu zai dawo gida Najeriya bayan ziyarar da ya kai kasashen China, UAE da Ingila. Ranar 29 ga watan Augusta ne shugaban ya bar Abuja zuwa Beijing inda ya dan tsahirta a Dubai, UAE. Ya isa Beijing ranar 1 ga watan Satumba. Ranar 2 ga watan Satumba ne dai shugaban ya fara ziyarar a aikace inda ya gana da shugaban kasar China Xi Jinping sannan aka masa fareti da harbin bindiga na ban girma. A taron, Najeriya da kasar China sun sakawa wasu yarjejeniyoyi guda 5 na ci gaban kasashen biyu hannu kamar yanda kakakin shugaban kasar, Bayo Onanuga ya bayyanar. Hakanan shugaban kasar na China Xi Jinping da matarsa, Peng Liyuan sun shiryawa shugaba Tinubu wata liyafar dare wadda aka nuna al'adun kasar Chinan. Daga nan Shugaba Tinubu ya tafi z...
Kalli Bidiyon Ambaliyar ruwan Maiduguri da aka dauka daga sama

Kalli Bidiyon Ambaliyar ruwan Maiduguri da aka dauka daga sama

Duk Labarai
Ambaliyar ruwan Maiduguri na daga cikin manyan abubuwan da suka tayar da hankalin Najeriya a makon da ya gabata. Wannan Bidiyo ne na yanda ambaliyar ruwan ta kasance wanda aka dauka daga sama. https://www.youtube.com/watch?v=X2SQOOEHmQg?si=Yipd2UO4zlFedN9s https://www.youtube.com/watch?v=F-KxNLEo-kY?si=8KQKXZIlyqMI_2vL Lamarin Ambaliyar ruwan ya jefa mutane cikin halin kaka nikayi
Tsadar rayuwa tasa yanzu da yawan ‘yan Najeriya basa iya sayen magunguna>>Kungiyar masu Hada magunguna ta Najeriya

Tsadar rayuwa tasa yanzu da yawan ‘yan Najeriya basa iya sayen magunguna>>Kungiyar masu Hada magunguna ta Najeriya

Duk Labarai
Kungiyar masu hada magunguna ta koka da cewa tsadar rayuwa tasa yanzu mutane da yawa basa iya sayen magunguna. Kungiyar ta alakanta hakan da tashin farashin magunguna da kayan hadasu da karyewar farashin dala da dogaro da shigo da kayan hada magunguna da shigo da magungunan daga kasashen waje. Kungiyar ta bayyana hakane a wajan wani taro da aka yi a A Legas na masu ruwa da tsaki a cikinta.
ALHAMDULILLAH: Sojojin Nijeriye Sun Aika Da Rikakken Dan Ta’àďďan Da Ya Addabi Jihar Katsina, Sani Wala Burki Zuwa Barzahu

ALHAMDULILLAH: Sojojin Nijeriye Sun Aika Da Rikakken Dan Ta’àďďan Da Ya Addabi Jihar Katsina, Sani Wala Burki Zuwa Barzahu

Duk Labarai
ALHAMDULILLAH: Sojojin Nijeriye Sun Aika Da Rikakken Dan Ta'àďďan Da Ya Addabi Jihar Katsina, Sani Wala Burki Zuwa Barzahu. Jami'an sojojin Nijeriya sun samu nasara haĺaķa Sani Wala Burki daya daga cikin manyan 'ýan ta'aďďan da suka addabi jihar katsina. Wala Burki ya gamu da ajalin sa ne a yau Asabar a wajen jami'an tsaro na haɗin guiwa a yayin wata arangama da suka yi. Wala Burki shine ya addabi ƙananan hukumomin Safana da Batsari dake jihar Katsina. Me za ku ce?
Hotuna: Wannan matashiyar ta samu tallafi daga mutane da yawa bayan da ambaliyar ruwa ta shafeta a jihar Borno

Hotuna: Wannan matashiyar ta samu tallafi daga mutane da yawa bayan da ambaliyar ruwa ta shafeta a jihar Borno

Duk Labarai
Wannan matashiyar daga jihar Borno ta samu tallafi daga mutane da yawa bayan da ambaliyar ruwa ta shafeta daga jihar Borno. A wani faifan bidiyonta daya watsu sosai a kafafen sada zumunta, an ga matashiyar tana kokawa da irin illar da ambaliyar ruwan ta musu. Hakan yawa mutane da yawa suka sha Alwashin tallafa mata inda tuni wasu suka bayyana cewa sun fara aika mata da tallafin kudi. Ambaliyar ruwan dai ta jefa mutane cikin halin rashin tabbas inda wasu dole suka bar gidajensu suka koma kodai wajan 'yan uwa ko suka shiga halin rayuwar rashin tabbas.
Ba Gaskiya Ba Ne Maganar Da Sheíkh Sani Yahaya Jingir Yayi, Saboda Bamu Wallafa Labarin Dake Cewa Tinubu Bai San An Ƙara Farashin Man Fetur Ba, Idan Kuwa Mun Wallafa Ya Bamu Hujja, Martanin Jaridar Daily Trust Ga Shiekh Jingir

Ba Gaskiya Ba Ne Maganar Da Sheíkh Sani Yahaya Jingir Yayi, Saboda Bamu Wallafa Labarin Dake Cewa Tinubu Bai San An Ƙara Farashin Man Fetur Ba, Idan Kuwa Mun Wallafa Ya Bamu Hujja, Martanin Jaridar Daily Trust Ga Shiekh Jingir

Duk Labarai
Ba Gaskiya Ba Ne Maganar Da Sheíkh Sani Yahaya Jingir Yayi, Saboda Bamu Wallafa Labarin Dake Cewa Tinubu Bai San An Ƙara Farashin Man Fetur Ba, Idan Kuwa Mun Wallafa Ya Bamu Hujja, Martanin Jaridar Daily Trust Ga Shiekh Jingir. A baya dai malam ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima basu sani ba aka kara kudin man fetur. Inda malamin yayi ikirarin cewa, jaridarta Daily Trust ce ta ruwaito hakan. Lamarin ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sadarwa. Inda da yawa suke ganin cewa bai kamata malamin yayi wannan magana ba. Me zaku ce ?