Nijeriya Ta Yi Nasarar Haƙo Gangar Mai Milyan Daya Da Rabi A Karon Farko Cikin Shekaru Hudu
Najeriya ta yi nasarar cimma burinta na cike gibin da take samu wajen hako mai wanda Kungiyar ƙasashe masu albarkatun mai OPEC ta kayyade mata na haƙo ganga miliyan 1.5 a kowace rana.
Wannan shinekaron farko cikin shekaru hudu da Najeriya ta sami irin wannan gagarumar nasara tun bayan dawowar matsalar masu fasa bututun mai da gwamtocin baya suka fuskanta
Wasu alkaluman binciken Bloomberg sun nuna cewa yawan man da Najeriya ke haƙowa ya ƙaru da ganga 40,000 zuwa miliyan 1.51 a watan Disambar bara.
A baya dai ƙungiyar OPEC ta ware wa Najeriya damar haƙo ganga Milyan 1.8 a kowace rana, sai dai ƙungiyar ta rage wannan adadi zuwa milyan 1.5 sakamakon gazawar Najeriya na cike giɓin da take samu wajen haƙar man ta dalilin matsalolinta na cikin gida, hakan ya janyo wa kasar koma-baya a ba...








