Majalisar Kula Da sarautun Gargajiya A Nijeriya Ta Nuna Damuwa Kan Gayyatar Da Aka Yi Wa Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II
Majalisar Kula Da Cibiyoyin Gargajiya A Nijeriya Ta Nuna Damuwa Kan Gayyatar Da Aka Yi Wa Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II
Ƙungiyar ta yi nuni da cewa tuni rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan lamarin, wanda hakan ya sa gayyatar ‘yan sandan bai zama dole ba.
Ƙungiyar a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun ko-odinetan ta na ƙasa Alhaji Yahaya Nda Musa, ta bayyana mamakin gayyatar da ‘yan sandan suka yi mai dauke da kwanan watan Afrilu 4, 2025, mai ɗauke da sa hannun kwamishinan ‘yan sanda Olajide Rufus Ibitoye, a madadin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da sashen leken asiri na rundunar.
“Muna da ra’ayin cewa wannan gayyata da babbar hukumar ‘yan sanda ta yi wa Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu cin mutunci ne ga cibiyarmu ta gargajiya, ...








