Thursday, December 25
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Buhari Bai Taba Son Tinubu A Matsayin Shugaban Ƙasa Ba, Bai Taba Amincewa Da Osinbajo Ba – Sule Lamido

Buhari Bai Taba Son Tinubu A Matsayin Shugaban Ƙasa Ba, Bai Taba Amincewa Da Osinbajo Ba – Sule Lamido

Duk Labarai
Daga: Abbas Yakubu Yaura Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba son shugaba Bola Tinubu ya gaje shi ba a matsayin shugaban kasa. Lamido ya kuma ce Buhari bai taba amincewa da tsohon mataimakinsa Yemi Osinbajo ya gaje shi ba, ya kara da cewa tsohon shugaban kasar yana son tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan ne ya gaje shi. Lamido ya ci gaba da cewa, babu wanda ya isa ya zama shugaban kasa saboda Tinubu mutum ne jajirtacce kuma mai son kansa. Da yake magana da jaridar Tribune, Lamido ya ce: “Kafin taron, shi (Tinubu) yana Abeokuta, jihar Ogun, inda ya yi takama da cewa lokaci ya yi da zai mulki Najeriya. Shi kuwa Buhari saboda butulci yana kallo. Bai taba son Tinubu ba. Akwai wanda yake so. “Bai ma aminta da nas...