Jihar Naija dake Arewa itace jiha mafi girman kasa a Najeriya.
Jihar na daya daga cikin jihohin Najeriya dake tsakiyar kasarnan.
Kuma tana da fadin kasa data kai 76,363 square kilometers.
Yawan jama'ar jihar sun kai 3,950,249.
Babban birni a jihar Naija shine Minna.
Sauran manyan birane a jihar sun hada da Bidda, Kontagora, da Suleja.
Jihar dake takewa Naija wajan girma ita Borno.
Sai jihar Taraba.
Sai Kaduna.
Wadda ke bin Kaduna itace Bauchi.
Sai kuma jihar Yobe.
Sai jihar Zamfara.
Daga nan kuma sai jihar Adamawa.
Me bin Adamawa itace jihar Kwara.
Sai Kuma jihar Kebbi.
Sannan sai jihar Benue.
Idan aka lura yawancin jihohin a Arewa suke.