Monday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Masoya Aminu Ado Bayero sun yi Sallar Rokon Allah ya dawo dashi kan sarautar Kano

Masoya Aminu Ado Bayero sun yi Sallar Rokon Allah ya dawo dashi kan sarautar Kano

Duk Labarai, Kano
Masoya tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero sun yi Sallah inda suka roki Allah ya dawo dashi kan sarautar Kano. Ranar Alhamis ne dai majalisar Kano ta soke dokar data kirkiro masarautu 4 a Kano sannan ta sauke Aminu Ado Bayero inda aka dawo da tsohon Sarki, Muhammad Sanusi II kan karagar Sarautar. Saidai Aminu Ado ya koma Kano inda ya je gidan Nasarawa ya kafa fadarsa acan, kuma masoyansa sun mai maraba. An ga masoyan Tsohon sarkin da yawa suna Sallah inda suke rokon Allah ya dawo dashi kan karagar sarautar Kano.
Bidiyo Da Duminsa: Zanga-zanga ta barke a Kano inda ake kone-konen Tayoyi

Bidiyo Da Duminsa: Zanga-zanga ta barke a Kano inda ake kone-konen Tayoyi

Duk Labarai, Kano
Zanga-zanga ta barke a Kano kan rikicin sarautar da ya faru a jihar. An ga wasu matasa dauke da kwalaye inda suke ihun basa so. An kuma ga an kunnawa taya wuta a karkashin wata fastar Abba da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. https://twitter.com/daily_trust/status/1794756398351356238?t=lWt28qaBdF9DMh57LPzSgw&s=19 Daily Trust ta wallafa bidiyon wanda ya nuna abinda ke faruwa. A wani bidiyon kuma an ga matasan na kabbara: Jaridar dai tace matasan dake zanga-zanga suna neman a sake dawo da Sarki, Aminu Ado Bayero ne kan karagar Mulkin Kano: https://twitter.com/daily_trust/status/1794760364070187113?t=-yPmQeNl8DbliJ5gkTzO7Q&s=19 Lamari dai ya kazancene bayan da Aminu Ado Bayero ya dawo Kano kuma ya sauka a gidan sarki dake Nasarawa.
Karanta Jadawalin Daraktoci 14 da CBN suka kora daga aiki

Karanta Jadawalin Daraktoci 14 da CBN suka kora daga aiki

Duk Labarai
Wadannan Daraktocine da babban bankin Najeriya, CBN ya kora daga aiki su 14. A kwanannan ne dai aka samu rahoton cewa, CBN din ta kori ma'aikata 200 da suka hada da manya da kanana. Clement Oluranti Buari, Director, Strategy Management Dr Blaise Ijebor, Director, Risk Management Lydia Ifeanyichukwu Alfa, Director, Internal Audit Jimoh Musa Itopa, Director, Capacity Development Muhammad Abba, Director, Human Resources Rabiu Musa, Director, Finance Dr Mahmud Hassan, Director, Trade & Exchange Dr Ozoemena S. Nnaji, Director, Statistics Dr Omolara Duke, Director, Financial Markets Chibuike D. Nwaegerue, Director, Other Financial Institutions Supervision Chibuzo A. Efobi, Director, Payments System Management Haruna Bala Mustafa, Director, Financial Pol...
Ba zan daina fadi ba, Peter Obi ne ya lashe zaben shekarar 2023>>Inji Datti Ahmad

Ba zan daina fadi ba, Peter Obi ne ya lashe zaben shekarar 2023>>Inji Datti Ahmad

Duk Labarai, Siyasa
Mataimakin Peter Obi a takarar shugabancin Najeriya da suka yi a shekarar 2023, Datti Baba Ahmad ya bayyana cewa ba zai daina fada ba cewa, Peter Obi ne ya lashe zaben shekarar 2023. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. Yace a lokacin da ake aikawa da sakamakon zabe ga hukumar INEC an kulle dadamalin yanar gizo da ake aikewa da sakon. Yace aka koma karbar sakon da hannu inda aka juya lamura. Ya kuma kara da cewa jam'iyyarsu a yanzu ta fi jam'iyyar CPC a zaben 2013/2014 karfi nesa ba kusa ba. Ya kara da cewa, tattalin arzikin Najeriya sai kara durkushewa yake, sannan kuma akwai cin hanci da rashawa sosai.
Hotuna: Jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja yayi Hadari

Hotuna: Jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja yayi Hadari

Abuja, Duk Labarai, Kaduna
Jirgin kasan dake zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna yayi hadari a yau, Lahadi. Jirgin yayi hadarin ne a daidai Jere. Jirgin ya tashi ne daga Kaduna zuwa Abuja da misalin karfe 8:05 na safiyar ranar Lahadi. Kuma ya sauka daga kan titinsa a daidai garin Jere. Jami'an tsaron sojoji dana 'yansanda sun je wajan da hadarin ya faru. Hukumar NIBS ta sanar da cewa tana sane da faruwar lamarin kuma ta tura jami'anta zuwa wajan.