Alamomin ciwon ulcer
Menene cutar Ulcer?
Cutar ulcer ko gyambon ciki, kamar yanda aka fi saninta da Hausa, ciwone dake samuwa a cikin dan adam ko kuma a cikin hanjinsa.
Allah ya halicci wata kariya a cikin dan Adam. Kariyarce idan ta samu matsala, sai wasu sinadarai da jikin mutum ke samarwa na sarrafa abinci su ji mada ciwo a ciki ko a hancinsa.
Ana iya maganin cutar ulcer cikin sauki. Amma idan aka barta ba tare da kulawa ba, tanawa mutum illa sosai.
Abubuwan dake kawo cutar ulcer
Abubuwan dake kawo cutar ulcer sun hada da:
Cutar da Bakateriya ke sawa.
Yawan shan magungunan Aspirin, ibuprofen, da naproxen.
A likitance, abinci baya saka ulcer.
Alamomin ciwon Ulcer
Alamar ciwon ulcer ya danganta da tsananin ciwon. Mafi shaharar alamar ciwon ulcer itace jin zafi a tsakanin kirji ...