Saturday, January 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Babu ranar daina Zàngà-zàngà sai Tinubu ya biya mana bukatunmu>>Inji Wanda suka shirya zanga-zangar tsadar rayuwa

Duk Labarai
A yayin da kamin fara zàngà-zàngà wanda suka shiryata suka ce an shiryata ne na tsawon kwanaki 10. A yau bayan da aka fara zàngà-zàngàr sun ce ba zasu daina ba har sai shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya biya musu bukatunsu. Hakan na zuwane yayin da kusan kowane sako da lungu na Najeriya ya dauki harama akan yin zanga-zangar.

Da Duminsa: ‘Yansanda a jihar Naija sun yi harbi dan hana masu zàngà-zàngà tare babbar hanya

Duk Labarai
Rahotanni sun ce 'yansanda sun yi harbi a iska a Tunga dake babbar birnin Jihar Naija watau Minna dan hana masu zanga-zanga tare babbar hanya. Da farko dai 'yansandan sun fara watsawa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa ne saidai daga baya masu zanga-zangar sun sake taruwa a waje daya. Rahoton yace jami'an tsaro da suka hada da sojoji, 'yansanda da sauransu sun cire duwatsu akan titi da matsa suka sa.

Yayin da aka fara zàngà-zàngà, farashin kayan abinci ya sake tashi

Duk Labarai
A yayin da aka fara zàngà-zàngà akan yunwa a yau, farashin kayan abinci ya sake tashi a kasuwannin Najeriya. Hakan ya farune yayin da mutane ke ta rububin ahuga kasuwa dan sayen kayan abinci saboda rashin sanin me zai je ya dawo game da maganar zanga-zangar. Gwamnatin tarayya dai ta yi iya bakin kokarinta dan ganin ba'a yi zanga-zangar ba amma abun ya ci tura inda tuni an fara zanga-zangar a jihohi da yawa na kasar nan.
Hotuna: Matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta girbe shukar data yi a gonarta dake fadar shugaban kasa

Hotuna: Matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta girbe shukar data yi a gonarta dake fadar shugaban kasa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta nuna yabanyar data girbe daga gonarta dake fadar shugaban kasa.
An samu banbancin ra’ayi: Yayin da Kwankwaso yace masu zàngà-zàngà su bari sai lokacin zabe su canja wanda basu so, Abba Gida-Gida yace yana goyon bayan zàngà-zàngàr kuma ma zai iya shiga a yi dashi

An samu banbancin ra’ayi: Yayin da Kwankwaso yace masu zàngà-zàngà su bari sai lokacin zabe su canja wanda basu so, Abba Gida-Gida yace yana goyon bayan zàngà-zàngàr kuma ma zai iya shiga a yi dashi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Gwamnatin jihar Kano, a karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta sanar da goyon bayan masu zanga-zangar kan tsadar rayuwa. Gwamnan da kansa ne ya bayyana hakan a wajan wani taro na masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar Laraba a Kano. Gwamnan yace muddin za'a yi zàngà-zàngàr cikin tsari ba tashin hankali zai karbi masu zanga-zangar a fadar gwamnati. Yace idam suna so ma zai shiga shima a yi dashi. Gwamnan yace kundin tsarin Mulkin Najeriya ya bayar da damar yin zanga-zangar. Saidai wannan ra'ayi nasa ya sh...
Dan kunar bakin wake da ya tayar da Bàm ya kàshe mutane 19 a jihar Borno

Dan kunar bakin wake da ya tayar da Bàm ya kàshe mutane 19 a jihar Borno

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Borno na cewa, akalla mitane 19 ne suka mutu,wasu da dama suka jikkata bayan harin bam da dan kunar bakin wake yakai akan kauyen Kawuri dake karamar hukumar Konduga ta jihar. Hakan na zuwane kasa da kwana daya bayan da bam ya tashi da wata mota ya kashe wani akawu dake aiki da karamar hukumar Damboa. Hakanan a baya ma bamabamai na kunar bakin wake sun tashi a karamar hukumar Gwoza inda mutane akalla 30 suka mutu wasu 100 suka jikkata. Jami'an tsaro sun fitar da sanarwar kiyaye kowane irin taron mutane a yanayin da ake ciki.
Da Duminsa: Babbar Kotu a Abuja ta Haramta Zàngà-zàngà

Da Duminsa: Babbar Kotu a Abuja ta Haramta Zàngà-zàngà

Duk Labarai
Wata babbar kotu dake babban birnin tarayya, Abuja ta haramta yin zanga-zanga. Kotun tace ba'a amince wani dan zanga-zanga ya hau kan titin babban birnin tarayya Abuja ba da sunan zai yi Zàngà-zàngà. Ministan Abuja, Nyesome Wike ne ya gabatar da wannan korafi a gaban kotun. A baya dai masu zanga-zangar sun nemi a basu filin Eagle Square dan amfani dashi wajan gudanar da gangaminsu amma hukumomi suka kiya. A yanzu masu zanga-zangar sun bayyana cewa ko an yadda ko ba'a yarda ba zasu yi amfani da filin.
Ana harbi ko aka kàshe mutum daya zamu ajiye duk wasu bukatu zamu koma neman sai Tinubu ya sauka daga mulki>>Inji Masu Zàngà-zàngà

Ana harbi ko aka kàshe mutum daya zamu ajiye duk wasu bukatu zamu koma neman sai Tinubu ya sauka daga mulki>>Inji Masu Zàngà-zàngà

Tsaro
Matasa masu shirin fita Zàngà-zàngàr tsadar rayuwa sun gargadi hukumomi kan cewa kada a sake a harbi ko a kashe ko da mutum daya a cikinsu. Sunce muddin aka yi hakan, to lallai zasu ajiye duk wasu bukatunsu su koma neman sai Bola Ahmad Tinubu ya sauka daga mulki. Daya daga cikin wakilan kungiyar, Damilare Adenola ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar. Ya kara da cewa ba zasu bari jinin 'yan uwansu ya zuba a banza ba.