Tabbas zaku iya rage kiba cikin sati daya amma abu mafi kyawu shine a shimfida tsari na rage kiba na lokaci me tsawo da yafi sati daya, kalla wata daya, biyu ko uku.
Dalili kuwa shine likitoci sun ce rage kiba a sati daya na iya zamarwa mutum matsala musamman idan yana da wasu manyan ciwuka irin su hawan jini, ciwon suga, ciwon zuciya da sauransu.
Sannan rage kiba a sati daya zai zama ba kitse bane kadai mutum zai rage hadda ruwan jiki da yawan naman jikin mutum wanda hakan ba zai dade ba mutum zai iya komawa yana da kiba.
Amma idan aka bi abun a hakanli, za'a fi samun sakamako me gamsarwa.
Saidai duk da haka,ga masu so, ga yanda za'a iya rage kiba cikin sati daya.
A daina cin abincin da aka sarrafa a kamfani, irin su cakulan, kifin gwangwani, waken gwangwani, yegot, Yoghurt...