DARASIN RAYUWA: Har Zuwa Yamma Ana Hira Da Shi Cikin Koshin Lafiya, Amma Daga Bisani Allah Ya Karbi Ransa A Wannan Ranar.
Allah Ya gafarta maka Turaki.
Daga Bello Abubakar Babaji
Hedkwatar tsaro (DHQ) tace jami’anta sun kashe ƴan ta’adda guda 1,166 tare da tsare wasu 1,096 acikin kwana 29 a faɗin Nijeriya.
Daraktan watsa labarai na ofishin, Manjo-Janar Edward Buba ya faɗi hakan a Abuja, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai kan ayyukan jami’an tsaro, a ranar Alhamis.
Ya ce, jami’an sun yi nasarar ceto mutane 721 da aka yi garkuwa da su.
Sannan, sun kuma ƙwato makamai 391 da wasu nau’ukan bindigu da kayan yaƙi da adadinsu ya kai 15,234 acikin wata guda.
Ya ƙara da cewa, sun yi nasarar kamo manyan ƴan ta’addan da kwamandodinsu a yayin gudanar da ayyukansu cikin watan.
Waɗanda aka kama a yankin Arewa-maso-Gabas sun haɗa da; Munir Arika, Sani Dilla (aka Ɗan Hausawan Jibilarram), Ameer Modu, Ɗan Fulani Fari Fari, Bakour...
Jarumar mai suna Sadiya Abdulƙadir wacce aka fi sani da (Sareena) sabuwar Jaruma ce duk da cewa ta ɗan kwana biyu a masana'antar ta Kannywood ana damawa da ita a fagen shirya fina-finan Hausa wadda ƴar asalin Jihar Bauchi ce ƙaramar hukumar Azare.
Fim na farko da ta fara yi tun bayan shigowarta masana'antar fim ne mai dogon zango mai suna (Aliya) wanda ake haska shi a (Youtube Channel) na Ali Jita, wato (Ali Jita Multimedia).
Yanzu haka dai Jarumar ta faso gada-gadan da zafinta domin cigaba da aikinta na faɗakarwa cikin fina-finan Hausa domin inganta tarbiyyar al'umma.
Photo Credit: Dk Photography
Wane fata zaku yi mata ?
An kama wadannan mutanen da zargin yiwa karuwai 3 fashi da makami.
Lamarin ya farune a titin Adeniran Ogunsanya dake Bode Thomas a Surulere ta jihar Legas.
Ranar 23 ga watan Augusta ne dai wanda ake zargin suka dauki karuwan 3 da niyyar zasu je su yi lalata dasu. Ko da suka shiga wani wuri sai suka tsayar da motarsu suka kwace musu wayoyi da kudade.
Karuwan dai sun kai kara wajan 'Yansanda inda suka ce sun gane fuskokin wanda suka musu satar.
Kuma an kamasu.
Kakakin 'yansandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarun.
Mafi yawanci budurwa tana tasowa ne da nonuwanta a tsaye. Amma wsu dalilai sukan sa nonuwan su kwanta.
Saidai budurwa ta sani cewa, idan tana da karancin shekaru, misali, daga 10 zuwa 15 nonuwanta basu gama girma ba, dan haka kada ta damu kanta da tsayuwar nonuwa ko karin girmansu.
Ta dakata tukuna har sai jikinta ya kammala girma, nonuwan sun kammala fitowa gaba daya.
Mafi yawan lokuta Nonuwan mace suna gama girma ne idan ta kai shekaru 18, saidai wasu matan nonuwansu na kara fitowa waje su kara girma har zuwa su kai shekaru 20 zuwa 25.
dan haka idan mace tana tsakanin shekaru 10 zuwa 20 ko 25 kada ta yi gaggawar nemanaganin kara girman nono, ta jira tukuna ta ga nonuwan nata su gama girma.
Kuma a sani mafi yawanci mata suna gadon girman nono ne a wajen iyayensu, idan mahai...
Kungiyar 'yan uwa musulmi da aka fi sani da shi'a aun koka kan cirewa matansu Hijabi da 'yansanda suka yi a Abuja.
Kungiyar tace wannan cin zarafine da kuma batanci ga addinin musulunci.
Wakiliyar mata ta kungiyar 'yan uwa musulmi, Maryam Sani ta bayyana a wata sanarwa data fitar cewa zasu yadawa duniya wannan lamari a gani.
https://www.tiktok.com/@asmat.muhd/video/7408970047680498950?_t=8pKCn6Pj8sg&_r=1
Kuma zasu kai maganar kotu.
Bidiyo dai ya bayyana a kafafen sada zumunta inda aka ga 'yansanda na cirewa matan 'yan shi'ar Hijabi ta karfin tsiya.
Wani magidanci dan shekaru 32 ya kashe kansa a garin Kemta dake Abeokuta jihar Ogun.
Lamarin ya farune da misalin karfe 10 na daren ranar Laraba kamar yanda kakakin 'yansandan jihar, Omolola Odutola ya tabbatar.
Matar mamacin ce ta iskeshi a rataye ba rai.
'Yansanda sun so su yi bincike amma iyalan mamacin suka kwace gawar suka ce zasu binne saidai hukumar 'yansandan tace tana bibiyar lamarin.
Dole Ne Mu Magance Matsalar Rashin Abinci Mai Gina Jiki, Inji Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi kira wajen kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Kungiyar Tarayyar Turai domin yaki da Matsalar karancin Abinci mai gina jiki da sauran kalubalen jin kai a kasar.
Kashim Shettima ya furta hakan ne a yayin da yake karbar bakuncin tawagar jakadan EU mai barin gado Samuela Isopi a wata ziyarar bankwana da ya kai fadar shugaban kasa.
Mataimakin ya kuma yaba da irin gudunmawar da kungiyar ta EU ke bai wa Najeriya Musamman a fannin Ayyukan jin kai da kasuwanci.Shettima ya yaba da ayyukan Isopi a Najeriya, ciki har da rawar da ta taka wajen karfafa huldar EU da Najeriya, wajen samar da zaman lafiya da tsaro.
A nata bangaren ita ma Isopi ta yi tsokaci k...
Mun samu labarin rasuwar yara biyu wadda iftila'in Gini ya faɗo musu a Anguwar Git Git dake Yarimaram ward Potiskum. Tare da raunata mutum ɗaya.
Tunidai shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Yobe, Dr. Mohammed Goje ya bada umarnin a yi gaggawa kai su Babban asibiti tare da biyan kuɗin magungunan da aka rubuta musu.
Yanzu haka Uwar tana kwance a Babban Asibitin Kwararru dake garin Potiskum domin cigaba da jinya. Inda aka garzaya da yaran biyu zuwa gida domin yi musu jana'iza.
Muna roƙon Allah ya karɓi shahadarsu baki ɗaya.Mahaifiyar tasu kuma Allah ya bata lafiya tare da haƙurin jure wannan Babban rashi.
JAN HANKALI
Wanann shekarar mun samu al'umma da dama wadda gine gine ya faɗo akansu tare da asarar rayuka da dama.
Dan Allah duk wadda gininsa ya nuna alama yayi h...