Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 8 a Maiduguri da jikkata wasu da dama
Rahotanni daga jihar Borno na cewa harin Bom ya kashe akalla mutane 8 da jikkata mutane da dama.
Harin wanda na kunar bakin wakene mahara 4 ne suka kaishi kuma rahoto yace dukansu sun mutu.
Hukumar 'yansandan jihar ta tabbatar da mutane 8 ne suka mutu inda wasu 15 suka jikkata.
Kakakin 'yansandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso ya bayyana cewa lamarin ya farune da misalin karfe 3:40 na safiyar yau,Rabar, 29 ga watan Yuni.
Rahoton yace wata mata dake goye da yaro ta tayar da bom din a tashar motar Mararraba dake T. Junction dake garin Gwoza.
Matar da dan da take goye dashi da wasu 6 sun mutu.
A bangaren jaridar Premium times kuwa, tace mata 4 ne suka tayar da bamabamai a bangarori daban-daban na jihar wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutanen da ba'a kai ga tantance yawansu ba c...