Amfanin lemon tsami a gashi
Lemun tsami yana da amfani mai yawa ga gashi.
Ga wasu daga cikin amfaninsa:
Kawar da Amosanin Kai: Lemun tsami na dauke da sinadarin anti-fungal da anti-bacterial wanda yake taimakawa wajen kawar da Dandruff/Amosani da sauran cututtukan fatar kai.
Inganta Tsawon Gashi: Ruwan lemon tsami na taimakawa wajen kara yawan jini a fata, wanda zai iya bunkasa saurin tsawon gashi.
Kare Gashi Daga Faduwa: Sinadarin Vitamin C dake cikin lemon tsami yana taimakawa wajen karfafa gashi da kuma hana faduwar gashi.
Inganta Sheki da Lafiyar Gashi: Acid din citric dake cikin lemon tsami yana taimakawa wajen cire datti da mai daga gashi, yana barin gashi mai tsabta da kuma sheki.
Rage Yawan Mai a Gashi: Idan kina da gashi me yawan fitar da maski, lemon tsami na taimakawa wajen rage yawan m...