Tuesday, January 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalaman soyayya

Kalaman Soyayya
Ga jerin kalaman soyayya masu dadi da kwantar da hankulan masoya. Kece numfashina Kaine numfashina Idan banji muryarka ba bana iya bacci. Idan ban ji muryarki ba bana iya bacci. Idan ina tare dake ji nake kawai na sukurkurce, kamar bani ba saboda tsabar shauki. Idan ina tare da kai, ji nake kawai na sukurkurce, kamar bani ba, saboda tsabar shauki. Kina burgeni fiye da yanda kike tunani. Kana burgeni fiye da yanda kake tunani. Idan muna tare sai inji kamar mu biyune kawai a duniyar. Idan ina tare da kai sai inji kamar mu biyu ne kawai a Duniyar. Idan ina tare dake ina mantawa da matsalolin rayuwata. Idan ina tare da kai ina mantawa da matsalolin rayuwata. Ban gajiya da jin kanshin turaren ki. Ban gajiya da jin kanshin turarenka Kallon gidanku ka...

Yadda ake kamuwa da ciwon hanta

Ciwon hanta
Ana kamuwa da ciwon hantane ta hanyar abinda ake cewa Virus, saidai wasu kalolin abinci, irin su giya, shan maganin gargajiya, da shan hadin gambizar magungunan asibiti ba tare da umarnin likita ba suma suna kawo cutar hanta. Shan abubuwan zaki na leda ko na roba wanda aka sarrafa suma suna iya haifar da cutar hanta. Hakanan yawan cin soyayyen abinci shima na iya haifar da cutar hanta. Hakanan wasu ana haihuwarsu da cutar ta hanta. Wannan virus na cutar hanta na yaduwa ne ta hanyar maniyyi, ruwa, abinci marar kyau, yin ma'amala ta kusa da wanda ya kamu ko ta hanyar jini. Saidai ita wannan cuta idan bata yi tsanani ba ana iya warkewa. Kuma akwai hanyoyi da ake bi wanda idan Allah ake inganta lafiyar hantar. Allah ya karemu da lafiya. Amin.

Rigakafin ciwon hanta

Ciwon hanta
Hanta na da matukar muhimmanci a jikin mutum wadda ke taimakawa gudanarwar jiki sosai dan haka yana da kyau mutum ya kula da lafiyarta. Akwai hanyoyi da yawa da mutum zai yi amfani dasu dan kula da hantarsa ta yanda in Allah ya yarda, ba zata kamu da ciwo ba. Hanyoyin sune: Motsa Jiki: Motsa jiki na da matukar muhimmanci wajan sa hantar mutum ta kasance cikin lafiya da aiki yanda ya kamata. Ka a sha ko a daina shan Giya: Shan giya na taimakawa wajan lalata hantar mutum, dan haka idan ana sha sai a daina, idan kuma ba'a sha, sai a kiyaye kada a sha. A kiyayi shan magungunan gargajiya: Yawan shan magungunan gargajiya barkatai, yana iya kaiwa ga mutum ya sha abinda zai illata hantarsa, dan haka a daina sha zai fi ko a kiyaye. Shan Coffee: Masana sun ce shan Coffee yana taima...
Tapswap sun ɗage Ranar da za ta fashe, za su sake sanya Lokaci

Tapswap sun ɗage Ranar da za ta fashe, za su sake sanya Lokaci

Duk Labarai
Tapswap sun ɗage Ranar da za ta fashe, za su sake sanya Lokaci. Shahararriyar Manhajar haƙo sulalla ta Tapswap ta hanyar TON Blockchain ta ce ta jinkirta ranar bajakolin kasafin sulalla ga masu amfani da shi zuwa wani lokaci da ba su sanar ba, yayin da ma'aikantan su ke kokarin neman karin hanyoyin da za su inganta shi domin amfanar mutane da yawa. Shugaban sashen sadarwa na Tapswap John Robbin ne ya bayyana hakan a dandalin sadarwarsa na X ranar Laraba. Dandalin wanda ke buƙatar masu amfani da shi da su rika danna alamar da ke tsakiyar manhajar Tapswap a Telegram don hakar sulalla a kwanan nan ya samu karbuwa a tsakanin 'yan Najeriya inda suke duƙufa wajen latsa fuskar wayarsu don neman kudi, kuma ya tara mutane sama da Miliyan 50 tun bayan da aka kaddamar da shi a ranar 15 g...
Nnamdi Kanu na duba yiwuwar yin sulhu da gwamnatin Najeriya

Nnamdi Kanu na duba yiwuwar yin sulhu da gwamnatin Najeriya

Siyasa
Lauyoyin jagoran ƙungiyar Ipob mai rajin kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu sun bayyana cewa akwai yiwuwar su tuntuɓi gwamnati domin neman sasanci a wajen kotu game da shari'ar da ake yi masa. Ana tuhumar Nnamdi Kanu ne da laifukan da suka jiɓanci ta'addanci a matsayinsa na jagoran ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biafra ta Ipob. Ƙungiyar na ƙoƙarin ganin yankin kudu maso gabashin Najeriya ya ɓalle ne tare da kafa ƙasa mai zaman kanta. Tuntuni gwamnatin Najeriya ta ayyana ƙungiyar a matsayin ta ƴan ta'adda. Aloy Ajimakor, wanda shi ne jagoran lauyoyin da ke kare Kanu, ya shaida wa kotu cewa kundin tsarin mulkin Najeriya da dokar da ta kafa Babbar kotun tarayya sun bayar da damar sasantawa a wajen kotu kan duk wani rikici tsakanin mutum da mutum ko kuma wani mutum da gwamnati. Sai ...

Allah Sarki: Ji yanda auren wata mata ya mutu saboda kissar kishiya

Abin Mamaki, Auratayya
Wata baiwa Allah da labarinta ke cike da ban tausai ta bayyana yanda aurenta ya mutu saboda kissar Kishiya. Ta bayyana hakane a zauren yanar gizo na Arewa up. Ga dai yanda labarin yake kamar yanda ta badashi: Ta fara shimfida kamar haka: "yadda aure na ya mutu assalamualaikum warahmatullah wabarakatuh yadda aure na na biyu ya mutu a silar kissar kishiya a gaskiya maza idan kunsan Baku Isa da matanku na gida ba kudaina yinkurin Kara aure sbd ku kanku Baku Isa kuce ba bare Kuma mu da aka aura" Ta ci gaba da bayar da labarin kamar haka: "wallahi na fada Miki bansan me ya faru ba Kinga an kaini gidansa ranar Friday to Kuma Daman gaskiya kamar Yana tsoron matar tasa to kwana na uku muka fara rabon kwana to yaje yayi mata kwana 2 ya dawo yayimun kwana 2 ya koma gidanta to wa...