Ana warkewa daga ciwon hanta
Ana warkewa daga mafi yawan cutar hanta da aka saba da ita a tsakanin al'umma saidai akwai kalar wadda ba' warkewa daga ita saidai ai ta kokarin shan magani.
Yawanci ba'a cika ganin alamun cutar hanta ba, fara maganin cutar da wuri na da matukar amfani saboda idan hantar ta riga ta tabu, magani bai cika yin tasiri ba.
Akwai matakai 3 na ciwon hanta kamar haka:
Hepatitis: Wannan shine matakin farko da hanta ke fara kumbura saboda wata cuta data sameta ko kuma ta kasa yakar wata cuta data shigeta. Daga wannan matakine cutar ke tsallakawa zuwa matakin Fibrosis.
Fibrosis: A wannan matakine hanta zata fara tsotsewa tana kankancewa, jini zai daina zuwarwa hantar, sannan kuma iska ma zai daina zuwar mata yanda ya kamata kuma zata rasa sauran sinadarai masu amfani. A wannan matakine h...