Monday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Gyaran nono a sati daya

Nono
Gyaran nono a sati daya nada wahala amma akwai dabarun da ake bi wajan ganin nono ya gyaru ya ciko ya bada sha'awa. Babbar hanyar da masana kiwon lafiya sukace na kara kumburo nono tasa ya ciko yayi kyau itace ta hanyar motsa jiki. Yin motsa jiki akai-akai, musamman bankarewa da zama a turo kirji da kuma yiwa nonuwan tausa duk yana sanya nono ya ciko yayi kyau sosai. Akwai abubuwan da idan ana cinsu suna taimakawa nono ya kara girma sosai. Misali Kifi, Man Zaitun da Madara. Hakanan masana sunce hanya daya da mace zata iya samun girman nono a dare daya amma tana da hadari itace ta hanyar yin tiyata ko Surgery a takaice.

Maganin matsi ciki da waje

Magunguna
Akwai magungunan matsi kala-kala na mata, wasu ana yi dan maganin sanyi, wasu kuma dan gaban mace ya matse. Idan maganin matsewar gaba ne watau Farji, Akwai hanyar gargajiya da ake amfani da ita. Wannan hanya itace ta amfani da ruwan sanyi, musamman kamin a sadu da me gida. Ana zama a cikin ruwan sanyi ne na dan lokaci kamin saduwa, hakan wata hanyar al'adace da ake magance matsalar budewar gaba. Akwai kuma hanyar matsi da Karo wadda itama ta gargajiyace amma a likitance bata ingabta ba. Ana kuma yin matsi da kanunfari wanda shima hanya ce ta gargajiya wadda a likitance bata inganta ba. Ana kuma yin matsi da Tafarnuwa, ita tafarnuwa an tabbatar tana maganin sanyi amma itama masana ilimin kiwon lafiya sun yi gargadin kada a sakata a cikin farji. Hakanan ana yin matsi da...

Amfanin aloe vera a gaban mace

Aloe Vera
Aloe Vera na da amfani daban-daban a jikin dan Adam Musamman mata. Daya daga cikin amfanin sa a jikin mace shine yana maganin kaikayin gaba. Macen dake fama da kaikayin gaba, tana iya amfani da man Aloe Vera, ko ruwansa, a samu wanda ba hadi a shafa a farji,da yardar Allah za'a samu sauki. Hakanan me fama da fitar farin ruwa a gabanta,itama tana iya amfani da Aloe Vera dan magance wannan matsala. Akwai wani bincike da aka yi dan gano ko Aloe Vera na maganin fitar farin ruwa a gaban mace? An ware mata 9 aka basu Aloe Vera suka rika amfani dashi kuma dukansu sun bayyana cewa sun samu Sauki. Hakanan a wani bincike da aka yi, An gano cewa idan aka hada Aloe Vera da Gurji(Cucumber) suna sawa gaban mace yayi haske.
Atiku ya caccaki manufofin Tinubu kan ƙayyade shekarun shiga jami’a

Atiku ya caccaki manufofin Tinubu kan ƙayyade shekarun shiga jami’a

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga manufar ma’aikatar ilimi ta tarayya na kayyade shekarun shiga jami’o’i, inda ya bayyana hakan a matsayin wani baƙon abu da zai janyo komabaya ga harkar ilimi a Najeriya A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana manufar a matsayin "zai haifar da naƙasu ga hakar ilimi" inda ya ce hakan ya saɓa wa ƙa'idojin tsarin ƙasar ta hanyar shiga ayyukan gwamnatocin jihohi. Atiku ya yi nuni da cewa ilimi na cikin abubuwan da ke cikin ƙundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bai wa ƙananan hukumomin ƙasar karfi wajen tafiyar da harkokinsa. Ya yi allah-wadai da matakin da gwamnati ta ɗauka na kafa manufofin ilimi ba kamar yadda doka ta tanada ba inda ya bayyana cewa hakan ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasa...
Zanga-zanga: An saki Turawan da ake zargi da hannu a ɗaga tutar Rasha a Najeriya

Zanga-zanga: An saki Turawan da ake zargi da hannu a ɗaga tutar Rasha a Najeriya

Duk Labarai
An saki ɗalibai da malamai ƴan asalin ƙasar Poland da aka kama a lokacin da aka yi zanga-zangar tsadar rayuwa, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Poland ya bayyana a ranar Laraba. Mutum bakwan sun shiga hannu ne a Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, "bisa zargin su da hannu a ɗaga tutocin Rasha da ma ita kanta zanga-zangar," kamar yadda jami'an tsaron Najeriya suka bayyana. Sai dai hukumomi a ƙasar Poland sun ce waɗanda aka kama ɗin ɗalibai ne na Jami'ar Warsaw da malaminsu, waɗanda "tsautsayi ya kai su inda bai dace ba." Ministan Harkokin Wajen Poland, Radoslaw Sikorski ya ce yanzu an sako ɗaliban. "Ina tabbatar da cewa an sako mutanenmu ɗin nan, yanzu haka sun koma Kano sun ci gaba da karatunsu," kamar yadda Sikorski ya wallafa wani bidiyo a shafi X. Ya ƙara da...
‘Ya kamata a ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a Najeriya’

‘Ya kamata a ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a Najeriya’

Duk Labarai
Cibiyar tattarawa da yaɗa bayanai kan rikice-rikice (CCC) ta yi gargaɗin cewa garkuwa da mutane na ƙaruwa a Najeriya, inda ta yi kira ga Gwamnatin Tarayyarv ƙasar da ta ayyana dokar ta-ɓaci domin magance matsalar. Shugaban CCC, Manjo Janar Chris Olukolade, mai ritaya, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa matsalolin za su iya ta'azzara idan ba a yi abin da ya dace ba, wanda hakan zai ƙara jefa rayuwar al'umma cikin matsala da ƙara taɓarɓarar da matsalar tsaro. Sanarwar ta ƙara da cewa garkuwa da mutane ta rikiɗe zuwa wata babbar harka ta kasuwanci, inda ƙungiyoyin ta'addanci ke amfani da lamarin domin samun kuɗin shiga. "Sace mutum da aka yi na kwana-nan shi ne sace basarake a Masarautar Sokoto, da sace ɗaliban jami'a masu karatun kiwon lafiya guda 20, waɗanda aka sako daga ...