Thursday, January 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Wannan ai Shedanne, mutane suka rika cewa yayin da aka ga wannan matashi ana sallah shi kuma yana daukar hoto

Wannan ai Shedanne, mutane suka rika cewa yayin da aka ga wannan matashi ana sallah shi kuma yana daukar hoto

Duk Labarai
Wannan hoton ya dauki hankula sosai a shafukan sada zumunta inda aka ga wani matashi yana daukar hoto yayin da ake Sallar Idi. https://twitter.com/ibrahimtashboi/status/1802439160084759037?t=F6_AUnKPRIIrE9PpVca8Aw&s=19 https://twitter.com/EmesDos1/status/1802417436966174863?t=OPElzhGrtqNv7JhtzFBY9A&s=19 https://twitter.com/Abbakr_Abbaty/status/1802376022802702542?t=LVT3XMoZKbhlpN7KJPeI5Q&s=19 https://twitter.com/jiddah_mk/status/1802402291959373960?t=0fx1YU9ewy-FK_it8Mat9w&s=19 https://twitter.com/ummer_zeee/status/1802375684930589145?t=k1LWW10JPU0euYreEMjOqg&s=19 Hoton ya nuna maza da mata a yamutse a waje daya ana Sallah sannan wasu na cewa ma ba'a daidaita sahu ba. Hoton ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta.
“Mataimakin Gwamna A Najeriya Kamar Ba Ka Da Aiki Ne” — Tsohon Mataimakin Gwamna

“Mataimakin Gwamna A Najeriya Kamar Ba Ka Da Aiki Ne” — Tsohon Mataimakin Gwamna

Siyasa
Yanzu haka dai wani tsohon ministan lantarki kuma tsohon mataimakin gwamna a jihar Yobe, ya ce babban sirrin zama mataimakin gwamna da gwamnan kansa shi ne yin gaskiya da riƙon amana da kuma biyayya. Injiniya Abubakar D. Aliyu ya ce duk da yake tsarin mulkin Najeriya ne ya tanadi muƙamin mataimakin gwamna, amma kuma bai tanadar masa wani taƙamaiman aiki ba, don haka “in dai kana so ka yi, ka zauna kawai. Abin da gwamna ya ce ka yi, ka yi. In ya ce kar ka yi, ka bari”. A cewarsa: “Ba zancen kai Mataimakin gwamna (ne ba), ai tare muka je mu kai kamfen, ai tare muka je! Ai gwamnatin, tsarin mulki ne yake ajiye ta, to kai kuma tsarin mulki ba abin da ya ba ka”. Tsohon Ministan ya Bayyana hakan ne a jerin hirarrakin da BBC ta yi da wasu jiga-jigan ‘yan siyasar Najeriya albarkacin cikar...
Kalli Bidiyon yanda aka kulle Gidan Dabo

Kalli Bidiyon yanda aka kulle Gidan Dabo

Kano
Rahotanni sun bayyana cewa wai an kulle gidan Dabo. Wani bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta ne ke wannan ikirari. https://twitter.com/Musaddiqww/status/1802438326735225133?t=uX0ExUbfDMFQ4drut1mL-g&s=19 Bidiyon ya nun kofar fadar sarkin Kano a Kulle. Lamarin dai ya jawo cece-kuce.
Bidiyo: Yadda Kanawa suka yiwa Gwamna Abba Kabir ihun bamayi a hanyarsa ta zuwa sallar Idi

Bidiyo: Yadda Kanawa suka yiwa Gwamna Abba Kabir ihun bamayi a hanyarsa ta zuwa sallar Idi

Kano
Rahotanni da bidiyo sun yo ta yawo kan Yadda Kanawa suka yiwa Gwamna Abba Kabir ihun bamayi a hanyarsa ta zuwa sallar Idi. Lamarin bai zo da mamaki ba ganin lamuran da suka faru a jihar ta Kano daga Chanja sarki wanda baiwa masu son Aminu Ado Bayero dadi ba zuwa rusau. https://twitter.com/Ahmad_Gogel/status/1802299626822811767?t=CZUUWUSeyPciG5gkc4w_VQ&s=19 An yi rusau din shaguna da yawa ana kwanaki 4 kamin Sallah a IBB wanda har ya jawo Wasu 'yan kasuwar suka yi zanga-zanga. Wannan dai ka iya zamarwa gwamnatin Abba Kabir Yusuf kalubale.
Ƴan bindiga sun sace mutane masu yawa ranar sallah a ƙauyen Dudun Doki na ƙaramar hukumar Gwadabawa ta jihar Sokoto

Ƴan bindiga sun sace mutane masu yawa ranar sallah a ƙauyen Dudun Doki na ƙaramar hukumar Gwadabawa ta jihar Sokoto

Sokoto, Tsaro
ANA BIKIN SALLAH YAN BINDIGA SUN TAFKA MUMMUNAN BARNA A SOKOTO. Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun kai hari wani kauye a jihar Sokoto, inda suka kashe kuma suka sace mutane da dama da sanyin safiyar Lahadi Maharan sun farmaki kauyen Dudun Doki a karamar hukumar Gwadabawa ta jihar, suka kashe mutane sama da goma, kamar yadda aka ruwaito An ruwaito cewa, har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan lamarin ba. Allah ta'ala yakawo mana zaman lafiya alfarmar Al-qur'ani.
Ya kamata a wayar da kan Mutane: Irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya na damuna>>Shugaba Buhari

Ya kamata a wayar da kan Mutane: Irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya na damuna>>Shugaba Buhari

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, irin yanda yawan mutane ke karuwa a Najeriya lamarin na damunshi. Ya bayar da shawarar cewa, ya kamata a wayar da kawunan mutane game da hakan. Shugaban ya bayyana hakane bayan kammala sallar Idi a jiya, Lahadi. Ya kuma bayyana farin cikinsa kan yanda mutane da yawa suka rungumi harkar Noma. Shugaban yace nasarar kasa ta dogara ne akan zamun shuwagabanni masu nasara akai-akai.