Babbar Hanyar da masana suka ce ana iya magance damuwa da ita shine motsa ciki.
Motsa ciki na da matukar tasiri sosai wajan magance matsalar damuwa, ko da kuwa tafiyace ta mintina 30 ko 5 ma ta isa a kullun.
Daina shan giya, masana sunce shan giya yana saka mutum damuwa sosai kuma yana hana yin bacci me kyau.
Samun bacci me kyau na da marukar Tasiri wajan maganin matsalar damuwa.
Daina Shan Taba: Masana sun bayyana cewa yawanci damuwace ke sa mutane su rika shan taba amma kuma duk da haka tabar bata maganin damuwa sai ma kara saka mutum cikin damuwar, dan haka daina shan taba zai taimakawa me fama da matsalar damuwa.
Samun Isashshen Bacci na taimakawa wajan magamce matsalar damuwa.
Hakanan cin abinci me gina jiki ma na taimakawa sosai wajan magance matsalar damuwa.
Yan...