Muna yin bakin ƙoƙarinmu kan matsalar tsaro – Gwamnatin Sokoto
Bayan an shafe kwanaki ana sukar yadda gwamnatin jihar Sokoto ke tafiyar da sha’anin tsaro, musamman bayan garkuwa da kuma kashe Sarkin Gobir na Gatawa, a yanzu hukumomin jihar sun bayyana cewa suna iyakar ƙoƙarinsu kan matsalar.
A makon da ya gabata ne ƴan bindiga suka kashe Sarkin Gobir, Muhammad Isa Bawa, bayan yin garkuwa da shi na sama da mako uku, lamarin da ya janyo wa hukumomi kakkausar suka.
Wasu dai a Najeriya na zargin hukumomi da gaza yin abin da ya kamata wajen kawar da matsalar tsaro a faɗin ƙasar.
Ƴan fashin daji na kai hare-hare a jihohin arewa maso yammacin ƙasar, yayin da har yanzu ake fuskantar hare-hare nan-da-can na ƙungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas.
Hukumomin Najeriya dai sun ce suna bakin ƙoƙarinsu wajen magance matsalar.
Sai dai kisan da a...