Wednesday, October 9
Shadow

Gwamnatin Tarayya Ta Tara Naira Bilyan 60 Daga Cire Tallafin Taki, Inji Hukumar NSIA

Daga Bello Abubakar Babaji

A ranar Litinin ne Hukumar kula da harkokin Zuba hannun-jari ta Ƙasa, NSIA ta sanar da cewa gwamnatin tarayya ta tara Naira biliyan 60 a ɓangaren cire tallafin taki a ƙarƙashin shirin taki na shugaban ƙasa (PFI) cikin shekaru takwas.

Hukumar, wadda tayi nazari kan ayyukan PFI, ta ce hakan wani yunƙuri ne bunƙasa masana’antar takin Nijeriya inda aka samar da masarrafa guda 84 a shiyyoyi shida na Nijeriya.

Ci gaban ya kuma tara Dala miliyan 200 daga hada-hadar cinikayyar ƙasashen wajen wanda hakan ya taimaka wajen samar da ayyuka 100,000.

Hakan nan, shirin PFI ya jagoranci raba buhunan taki mai inganci miliyan 90 ga manoma a Nijeriya.

Karanta Wannan  Tinubu ya bai wa jihohi naira biliyan 108bn kan ambaliya da zaizayar ƙasa - Shettima

Darakta Manaja na NSIA, Aminu Umar Sadiq ya yi ƙarin haske game da nasarorin da aka samu ta hanyar shirin waɗanda suka haɗa da rage adadin tallafi da gwamnati ke biya da kuma farfaɗo da martabar masana’antar taki na gida.

Ya ce, duk da ƙalubalen annobar COVID-19 da yaƙi tsakanin Rasha da Ukraniya, PFI ya yi nasarar ɗorewa wajen raba taki a Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, duk da ƙalubalen sauye-sauyen cinikayyar ƙasashen waje kan shigo da sinadarai, ya na mai tabbatar da cewa NSIA ta na aiki tuƙuru da abokanan hulɗa wajen cigaba da taimaka wa harkar noma a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *