Monday, January 27
Shadow

Author: Bashir Ahmed

‘Yan Bindiga: Bani Da Ikon Tafiyar da Harkokin Tsaro A Zamfara – Gwamna Lawal

‘Yan Bindiga: Bani Da Ikon Tafiyar da Harkokin Tsaro A Zamfara – Gwamna Lawal

Jihar Zamfara, Tsaro
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya koka kan yadda ya kasa sarrafa gine-ginen tsaro a jihar. Lawal ya ce ba shi da iko a kan shugabannin hukumomin tsaro a jihar, yana mai jaddada cewa suna karbar umarni daga manyansu. Da yake jawabi yayin wani taron birnin tarayya na bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya karo na 25 a Abuja ranar Laraba, gwamnan ya yi tir da ayyukan ‘yan bindiga a jihar. A cewar Lawal: “Da sunan, ni ne babban jami’in tsaro na jihata amma idan ana maganar umarni da iko, ba ni da iko a kan duk wani jami’in tsaro na soja, ko ‘yan sanda ko na Civil Defence. “Suna karbar umarninsu daga manyansu ba daga gwamnoni ba. Ba mu da wannan iko, ina fata muna da, da ya kasance wani labari na daban. " Ya ce matsalar tsaro ba ta gyaru a jihar ba sakamakon katsalandan da ya b...
An Daure Wani Mutum A Gidan Yari Sakamakon Samun Sa Da Laifin Karbar Batirin Jirgin Kasa Na Sata

An Daure Wani Mutum A Gidan Yari Sakamakon Samun Sa Da Laifin Karbar Batirin Jirgin Kasa Na Sata

Duk Labarai
A ranar Alhamis ne wata kotun majistare da ke garin Kafanchan a jihar Kaduna, ta yanke wa wani matashi mai suna Chibuzo Emmanuel, dan shekara 40 da haihuwa, hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari, bisa samunsa da laifin karbar baturan jirgin kasa da silinda na sata. Hukumar NSCDC, ta gurfanar da Emmanuel tare da Adamu Danbaba mai shekaru 52 da laifin sata da kuma karbar dukiyar sata. Jami'i mai shigar da kara na NSCDC, Mista Marcus Audu, ya shaida wa kotun cewa hukumar kula da layin dogo ta Najeriya da ke yankin Arewa ta tsakiya, Kafanchan, ta shigar da kara a ofishin hukumar a ranar 13 ga watan Mayu. Audu ya bayyana cewa Danbaba ma’aikacin layin dogo ne ya saci batir din jirgin kasa guda biyu da silinda mai nauyin kilogiram 12 a ofishin sa ya sayar wa Emmanuel akan kudi N24,000...

Cin yaji ga mai ciki

Duk Labarai, Gwajin Ciki
Cin abinci me yaji ga mai ciki bashi da matsala sam ko kadan. Kuma ba zai cutar da dan cikinki ba. Saboda yanayin bakin me ciki, zaki so cin abu me yaji dan kwadayi, masana sun ce zaki iya ci ba tare da matsala ba. Mutane da yawa na da tunanin cewa, abinci me yaji yana da hadari ga mai ciki amma hakan ba gaskiya bane. Saidai a sani ko menene aka yishi ya wuce iyaka zai iya bayar da matsala. Hakanan kowace mace da irin jikinta, wata Yaji zai iya zamar mata matsala, wata kuma bata da matsala dashi. Dan haka kinfi kowa sanin kanki. Yaji zai iya sa zafin kirji ko kuma rashin narkewar abinci wanda duka basu da mummunar illa ga me ciki. Jin kwadayin cin abinci me yaji ba matsala bane ga mace me ciki, ga wasu amfanin da abincin me yaji zai yiwa mace me ciki kamar haka: Cin...

Yadda mai ciki zata kwanta

Gwajin Ciki
Masana sun yi amannar cewa, da zaran ciki ya fara girma, an fi son mace ta kwanta a bangaren jikinta na hagu tare da lankwasa gwiwowin kafarta. Wannan tsarin kwanciya a cewarsu shine mafi jin dadi sannan zai taimakawa gudanar jini a jikin uwar da danta. Hakanan a cewar masanan, wannan salon kwanciyar yana hana kumburar kafar me ciki. Masana kiwon lafiya sunce kwanciyar ruf da ciki bata da illa idan ciki be girma ba amma idan ya girma a daina yinta. Masana sun ce kwanciya a gefen dama yana da illa amma kuma me ciki zata iya kwanciya a gefen dama na dan gajeren lokaci. Hakanan masana sun yi gargadin kada a kwanta rigingine, watau akan baya musamman idan ciki yayi nisa. Kwanciya akan baya na hana jini gudana yanda ya kamata a jikin me ciki da kuma dan dake cikinta. Hakana...
Hotuna: An kama wadannan malaman makarantar mata bayan da suka yi yunkurin yin taron dangi suwa dalibinsu fya-de

Hotuna: An kama wadannan malaman makarantar mata bayan da suka yi yunkurin yin taron dangi suwa dalibinsu fya-de

Abin Mamaki
Wasu malaman makaranta a kasar Amurka sun yi ritaya bayan da aka kamasu suna yunkurin yin taron dangi dan yiwa dalibinsu fyade. Malaman mata sunansu Alexsia Saldaris da kuma Jennifer Larson dake koyarwa a makarantar Joseph Craig High School dake garin Janesville dake jihar Wisconsin. An gano cewa, daya daga cikin malaman har ta aikewa da dalibin hotonta na batsa. Bayan da aka tunkareta da maganar, ta amsa cewa lallai ta aikawa da dalibin hotunan batsa. Hakanan sun kuma nemi dalibin ko zai sako musu karin wani dalibi ya zo su yi lalatar tare dashi. Yanzu haka dai hukumar 'yansanda ta garin Janesville tana bincike kan lamarin.
‘Ana samun ƙaruwar bautar da ƙananan yara a Najeriya’

‘Ana samun ƙaruwar bautar da ƙananan yara a Najeriya’

Abin Mamaki
Wasu alƙaluman hukumomin kare haƙƙin dan adam a duniya sun nuna cewa ana samun ƙaruwar cin zarafin ƙananan yara a wasu ƙasashen duniya musamman na Afrika, ta hanyar bautar da su, ko sanya su aikin wahala. Bayanai sun nuna cewa akwai yara fiye da miliyan 87 a duniya da ke aikin karfi ko aikatau, kuma sun fi yawa ne a arewaci da kuma yammacin Afrika. Arewacin Najeriya na daga cikin wuraren da wannan matsalar ke karuwa a cikin ƴan shekarun nan. Bincike ya gano cewa matsalolin cin zarafin da yara kanana ke fuskanta na dakushe musu rayuwa, da janyo musu tsangwama a cikin al'uma da sauran su. Kungiyar ba da agajin ta Save the Children ta ce tana bakin kokarinta wajen ganin an magance matsalolin, da tabbatar ganin an tallafawa wadanda suka samu kan su cikin irin wannan halin domin ing...

Ya ake gane cikin namiji

Gwajin Ciki
A yayin da kika dauki ciki zaki ta samun mutane suna miki magana da bayyana ra'ayoyinsu akan cewa, namiji ne kike dauke dashi ko mace. Akwai dai maganganu na al'ada da camfe-camfe wanda a wannan rubutu zamu muku bayani dalla-dalla yanda lamarin yace a ilimance. A ilimin likitanci, sun ce da zarar maniyyi ya shiga mahaifane ake tantance cewa namiji ne mace zata haifa ko mace. Hakanan sunce kuma kalar ido, kalar gashi, da sauransu duk daga shigar maniyyi da kwan mace mahaifa duka ake tantancesu. Al'aurar abinda ke cikinki zata fara bayyana ne a yayin da kika kai sati 11 da daukar ciki. Saidai duk da haka, ko da gwaji aka yi a wannan lokacin ba za'a iya tantance namiji ne zaki haifa ko mace ba. Maganganun da basu da inganci da ake amfani dasu wajan cewa kin dauki cikin mace ko ...
Ji wata murya da aka ce ta Sarki Sanusi ce tana cewa zasu sauke Gwamna Abba Gida-Gida, “Gara Ganduje ya dawo”

Ji wata murya da aka ce ta Sarki Sanusi ce tana cewa zasu sauke Gwamna Abba Gida-Gida, “Gara Ganduje ya dawo”

Kano
Wata murya data bayyana a kafafen sada zumunta wadda ake cewa ta me martaba sarkin Kano ce, Muhammad Sanusi II ta rika cewa ba'a musu abinda suke so ba. Sannan kuma zasu yi amfani da karfin jama'a su sauke Gwamna Abba Gida-Gida, an ji muryar na cewa, gara Ganduje ya dawo. Saidai babu wata kafa ko majiya me zaman kanta data tabbatar da cewa, wannan muryar ta sarki Muhammad Sanusi II ne. https://twitter.com/Engr_Alkasimfge/status/1800821908126249077?t=7lPi1Tm7EWRvndIKrHfiVw&s=19 Wannan murya tana iya yiyuwa kwaikwayon muryar sarkin aka yi, kamar yanda wasu ke zargi, ko kumama an yi amfani da fasahar zamani ta AI Voice wajan yinta. A Kano dai har yanzu akwai Sarki Muhammad Sanusi II wanda shine Gwamnatin jihar ta nada a matsayin sarki, sannan akwai Me marba Aminu Ado Baye...

Yadda ake gane cikin tagwaye

Gwajin Ciki
Babbar hanyar da ake gane cikin tagwaye shine ta yin gwaji. Saidai akwai alamomi na al'ada wanda ake amfani dasu wajan gane cikin tagwaye bisa yanda aka saba gani a wajen masu haihuwarsu: Wadannan alamu na cikin gwaye sune kamar haka: Wadannan alamomi da zaku karanta sukan farune a kwanakin farko-farko na daukar ciki. Za'a ji motsin ciki da wuri. Za'a ji motsin ciki a bangarori daban-daban na cikin. Cikin zai yi girma fiye da yanda aka saba gani a sauran cikkunan da ake dauka. Nauyin jikin me cikin zai karu sosai. A wajan gwaji, na'ura zata nuna zuciyoyi biyu na bugawa. Wadannan sune alamomin dake nuna mace na dauke da Tagwaye, saidai kamar yanda muka fada a farko, babbar hanyar gane Tagwaue itace a yi gwaji. Mace zata iya rika jin wadannan alamomi a jikinta i...
“Kylian Mbappe ya ce gasar Euro ta fi gasar cin kofin duniya wahala? Ya kuma ce kungiyoyin Kudancin Amurka ba sa fafata gasar da takai ta Turai, wajen darajar abin da suke bugawa

“Kylian Mbappe ya ce gasar Euro ta fi gasar cin kofin duniya wahala? Ya kuma ce kungiyoyin Kudancin Amurka ba sa fafata gasar da takai ta Turai, wajen darajar abin da suke bugawa

Kylian Mbappe
"Kylian Mbappe ya ce gasar Euro ta fi gasar cin kofin duniya wahala? Ya kuma ce kungiyoyin Kudancin Amurka ba sa fafata gasar da takai ta Turai, wajen darajar abin da suke bugawa. Leo Messi "Kofin Euro yana da matukar muhimmanci, amma babu kasar Argentina, wadda ta taba zama zakarar duniya sau uku, da kasar Brazil mai rike da kofin duniya sau biyar, Uruguay, wadda ta taba zama zakara a duniya sau biyu. Gasar da ta zama mafi wuya. "A gasar cin kofin duniya, kungiyoyin kasashen duniya wadanda suka fi kyau sune a cikin gasar, dukkanin zakarun duniya suna cikin gasar. Shi ya sa burin kowanne dan wasa shine son zama zakaran duniya." (arevalo_martin) ● Fagen Wasanni