Babban malamin addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami kenan a wadannan hotunan tare da malamai abokansa.
https://twitter.com/ProfIsaPantami/status/1799702225411043418?t=R6pngDgWCiYXtOoWkuIqDA&s=19
Sheikh Pantami ya wallafa hotunan a shafinsa na sada zumunta inda masoyansa da yawa suka yaba
Atiku, Kwankwaso: Dalilan Da Ya Sa Arewa Ba Za ta Iya Magana Da Murya Ɗaya Ba A 2027 – Buba Galadima.
DAGA: Abbas Yakubu Yaura
Wani jigo a jam’iyyar, NNPP, Buba Galadima ya ce ba zai taba yiwuwa ɗaukacin yankin Arewa su samu ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya a zaɓen 2027 ba.
A wata hira da jaridar Sun, tsohon sakataren rusasshiyar jam'iyyar CPC, ya bayyana cewa a tsarin dimokuradiyya irin na Najeriya, masu zaɓe na da ƴancin yin zaɓi daban-daban.
Da aka tambaye shi ko ƴan Arewa za su zaɓi Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, ko kuma takwaransa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, Galadima ya ce, “Ba ma cikin còci; Ba ma cikin másallaci. Me ya sa za mu yi magana da murya ɗaya?
“Dimokradiyya kenan."Idan ka haɗa mutane uku tare, kowa ya sami hanyar t...
Madugun Kwankwasiyya kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya zargi 'yan adawa a Kano da cin dunduniyar gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf har tsawon shekara guda.
Kwankwaso ya fadi haka ne a lokacin da gwamnatin Kano ta ayyana dokar ta-baci kan ilimi a jihar Kano a yau Asabar.
Ya ce, “Bari in fara da taya shi murnar wannan rana mai cike da tarihi, ranar da gwamna ke ayyana dokar ta-baci kan ilimi. Sanin kowa ne cewa gwamna yana aiki tun daga ranar da ya hau mulki a ko’ina a fadin jihar.
“Duk da cewa gwamnan ya na fuskantar kalubale tsawon shekara guda. Nan da nan bayan zaɓe, maƙiyan Jiha sun kai shi Kotu, zuwa Kotun Daukaka Kara zuwa Kotun Koli. Mun ga abin da ya faru duk da sun san cewa babu bukatar a je wata Kotu. Kowa ya san cewa ya ci zabensa...
Iya Yawan Yin "Mining" Ɗinka, Iya Talaucinka, Inji Naziru Sarkin Waƙa
Maganar Mawaƙin na cigaba da jawo cece-kuce da kuma zazzafar muhawara musamman a tsakanin matasa.
Ko me.za ku ce akan wannan magana ta Sarkin Waƙa?
Daga Abubakar Shehu Dokoki
TIRKASHI: Ya Saki Matarsa Saboda Ganyen Shayi, Bayan Tsawon Shakara Goma Suna Zaman Aure
Daga Mubarak Ibrahim Lawan
"Da Asubahi ta gaya wa mijin cewa ganyan shayi ya ƙare. Wajen ƙarfe shida na safe kuma ƙaninsa ya zo ya ɗauke shi suka tafi jana'izar wani abokin kasuwancinsu. Bayan ya dawo gida wajen ƙarfe 9 na safiyar, sai ya tarar yaransa ba su tafi makaranta ba. Ya tambayi dalili sai ta ce ai bai kawo ganyen shayin da za su yi karin kumallo ba. Daga nan fitina ta fara. A yinin ya sallame ta.
Lokacin da iyaye suka shiga maganar, sai ya ce ya gaji da zama da macen da ta ke kasa yi masa hidimar naira 100 duk da cewa shi ya na iya yi mata hidimar miliyan 5 domin, a shekarar bara ma ya kai ta Hajji, ya canja mata kujeru, kuma ya tabbatar cewa shi ya sama mata aikin da ta ke yi. Ya ƙa...
IDAN KUNNE YA JI.
Idan Har Kina Sha'awar Shigowa Harkar Fim Amma Ba Ki Shigo Ba Tukun, To Ki Rufawa Kanki Asiri Ki Je Ki Yi Aure Ya Fi Miki, Shawarar Hadiza Gabon Ga 'Yan Mata Masu Sha'awar Shiga Harkar Finafinan Hausa.
Daga Rariya.
Bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumuna na tsohon ministan sufuri a kasar Burkina Faso,Vincent Dabilgou inda aka ga mutane na zaneshi.
An masa hakane bisa zargin cewa ya saci makudan kidade a kasar.
https://twitter.com/PSAFLIVE/status/1799334263747465694?t=utEYAEYbq_Y905R_nO6sWA&s=19
Lamarin dai ya dauki hankula sosai inda da yawa suka rika cewa sun yi fatan a kasarsu ma za'a iya yin hakan
Tauraron Fina-finan Hausa, Adam A. Zango kenan a wadannan bidiyon da ya saki a shafinsa na sada zumunta inda aka ganshi suna shakatawa shi da iyalansa:
https://www.tiktok.com/@iam_adam_a_zango/video/7378231281156361478?_t=8n2RujFVFjB&_r=1
https://www.tiktok.com/@iam_adam_a_zango/video/7378231578486443269?_t=8n2S1sKTbdd&_r=1
Tun bayan fashewar Notcoins, matasa a Najeriya suka mayar da hankalai wajen yin mainin, domin tara maki ko 'points' a cikin manhajojin da suke amfani da su a wayoyinsu.
Daga lokacin ne kuma harkar kirifto ke ƙara samun karɓuwa a Najeriya, inda a kowace rana ake samun ƙaruwar ɓullar sabbin shafukan mainin da ke alƙawarta samar wa mutane kuɗi.
Masu amfani da shafukan ko manhajojin kan yi ta taɓa sikirin ɗin wayarsu domin samun wani maki da ake kira 'points', wanda za a iya canjawa zuwa kuɗi ''idan ta fashe''.
A yanzu akwai sabbin manhajojin waya da dama da ake amfani da su domin samun kuɗin.
Fitattu daga ciki sun haɗa da Notcoins da Tapswap da Hamstar Kombat da Poppo da sauransu.
Yayin da wasu mutane ke darawa saboda kuɗin da suka ce sun samu sakamakon fashewar Notcoins, wasu ...