Sunday, February 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Masarautar Kano: Yajin aiki ya hana sauraron ƙarar Aminu Ado

Masarautar Kano: Yajin aiki ya hana sauraron ƙarar Aminu Ado

Kano
A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta fara a yau ya kawo cikas wajen zaman sauraron ƙarar da Alhaji Aminu Babba Danagundi ya shigar yana ƙalubalantar rushe masarautun jihar. Gwamna Abba Kabir ya soke masarautu biyar - ciki har da sababbi da aka ƙirƙiro a 2019 - bayan sauye-sauyen da Majalisar Dokokin Kano ta yi wa dokar masarautun jihar a watan Mayu, wanda hakan ya ba shi damar sauke Sarki Aminu Ado Bayero, kuma ya naɗa Muhammadu Sanusi II. Sai dai bayan ɗaukar matakin ne Aminu Ado Bayero ya koma garin kuma ya sauka a gidan sarki na Nassarawa saboda umarnin kotu da ya ce a dakatar da rushe masarautun har sai ta gama sauraron ƙarar. "Da zarar an janye yajin aiki kotu za ta ba mu sabuwar ranar sauraron ƙarar, umarnin da kotu ta bayar yana nan daram...
Jam’iyyar Labour ta ce yajin aiki zai ƙara wa ƴan Najeriya wahala ne kawai

Jam’iyyar Labour ta ce yajin aiki zai ƙara wa ƴan Najeriya wahala ne kawai

Siyasa
Jam'iyyar Labour ta yi kira ga ƙungiyoyin ƴan ƙwadago a Najeriya da su sake tattaunawa da gwamnati a kan maganar sabon albashi mafi ƙanƙanta maimakon shiga yajin aiki. Jam'iyyar ta ce a halin da Najeriya take ciki yajin aiki ba shi da amfani hasali ma zai iya ƙara wa ƴan ƙasar wahalhalun da suke ciki ne. Babban sakataren yaɗa labaran jam'iyyar Obiora Ifoh ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN). Ya ce tuni daman ƴan Najeriya na fama da katutun matsaloli, a don haka babu buƙatar yin abin da zai ƙara waɗannan wahalhalu. '' Ina ganin neman Naira 494 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ba abu ne mai yuwuwa ba. Abu ne da ba zai ɗore ba saboda hakan na nufin cewa Najeriya za ta ɗauki duk kuɗin da take da shi ta riƙa biyan ma'aikata,'' in ji ...
Maniyyata 737 sun tashi daga Najeriya ranar Litinin duk da yajin aiki

Maniyyata 737 sun tashi daga Najeriya ranar Litinin duk da yajin aiki

Hajjin Bana
Maniyyata Hajjin bana daga Najeriya na ci gaba da tashi zuwa ƙasa mai tsarki duk da yajin aikin 'yan ƙwadago da ya haddasa tsaiko a filayen jirgin ƙasar. Hukumar Alhazai ta Ƙasa National Hajj Commission of Nigeria (Nahcon) ta ce aƙalla maniyyata 737 ne suka tashi a yau Litinin daga jihohin Kwara da Sokoto. Nahcon ta ce jirgin Air Peace ne ya fara tashi a yau daga birnin Ilorin na jihar Kwara da mutum 311 da misalin ƙarfe 9:52 na safe. Sai kuma wani jirgin Flynas da ya sake tashi da mutum 426 daga jihar Sokoto. Alƙaluman da hukumar ta wallafa sun nuna cewa zuwa yanzu jimillar maniyyata 38,249 aka kwashe zuwa Saudiyya don gudanar da babbar ibadar ta addinin Musulunci.
Shugabannin ƙwadago da na gwamnati na tattaunawa

Shugabannin ƙwadago da na gwamnati na tattaunawa

Siyasa
Wakilan ƙungiyar ƙwadago ta NLC da TUC na can na ci gaba da tattaunawa da wakilan gwamnati a ofishin sakataren gwamnati da ke Abuja. Wannan dai na zuwa ne bayan kwashe sa'o'i da dama gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago suna yajin aiki a Najeriyar, inda asibitoci da makarantu da sauran ma'aikatu suka kasance a rufe. Gwamnatin shugaba Tinubu ta nemi 'yan ƙungiyar da su janye yajin aikin su koma bakin tattaunawa. Wannan tattaunawar ita ce zangon farko kafin wadda za a yi a ranar Talata.

Ba za mu shiga yajin aiki ba – Ƙungiyar likitoci Kano

Kano
Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa reshen jihar Kano, (NMA), ta ce likitocin da ke aiki a asibitocin Kano za su ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ke gudanarwa. Sakataren ƙungiyar reshen jihar Kano, Dr Abdurrahman Ali, ya shaida wa jaridar Daily Trust ranar Litinin cewa " mu ƙwararru ne saboda haka ba a ƙarƙashin ƙungiyar ƙwadago muke kuma saboda haka ba za mu shiga yajin aiki ba". Ya ƙara da cewa “dukkannin likitoci da sauran ma'aikatan lafiya za su ci gaba da kasancewa a wuraren aikinsu. Bai zama lallai a cimma hakan ɗari bisa ɗari ba amma dai ba za mu shiga yajin aikn ba. E akwai yiwuwar ka je ka ga ma'aikacin da zai fito da fayil ɗinka ba ya nan amma kuma mambobinmu za su kasance a wuraren aikinsu.”
Gwamnatin Najeriya ta roƙi ‘yan ƙwadago su janye yajin aiki

Gwamnatin Najeriya ta roƙi ‘yan ƙwadago su janye yajin aiki

Siyasa
Gwamnatin Najeriya ta roƙi haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC da ta 'yan kasuwa TUC da su janye yajin aikin da suka fara a yau Litinin. Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya nemi 'yan ƙwadagon su koma kan teburin tattaunawa, kuma bayanai sun nuna cewa yanzu haka ma 'yan ƙwadagon na tattaunawa da wakilan gwamnatin a Abuja. "Wannan roƙo ne muke yi cikin sanyin murya ga ƙungiyoyin ƙwadago da su dawo teburin tattaunawa da gwamnatin Najeriya da na jihohi ƙarƙashin jagorancin kwamatin lalubo mafi ƙarancin albashi," in ji ministan yayin wani taron manema labarai. A matsayinmu na gwamnati, muna muradin a cimma matsaya cikin lumana kuma za mu yi duk mai yiwuwa wajen cimma hakan. Jiya shugabannin majalisa sun gana da 'yan ƙwadago, yau mu ma mun sake gayyatar su don cigaba da tattaunawar."...

Kalli Bidiyo yanda NLC ta kulle gidan rarraba lantarki na Kaduna(KEDCO)

Siyasa
Kungiyar Kwadago ta NUEE dake karkashin NLC ta kulle gidan rarraba wutar lantarki na Kaduna, watau KEDCO. Ta kulle gidan wutar ne a yau, Litinin dan tabbatar da yajin aikin da suke kan neman karin mafi karancin Albashi. Kalli Bidiyon a kasa: https://twitter.com/channelstv/status/1797610368522740126?t=Bb2fuE322DgypwK9UrwOew&s=19 In compliance with the nationwide strike, the National Union of Electricity Employees(NUEE) has also shut down operations at the Kaduna Electricity Distribution Company (KAEDCO). The union officials on Monday morning locked the premises of KAEDCO Headquarters in Kaduna.