Friday, December 5
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Akwai yiyuwar a yi fama da wahalar man fetur yayin da kungiyar NUPENG ke shirin bin kungiyar kwadago itama ta yi yajin aiki

Akwai yiyuwar a yi fama da wahalar man fetur yayin da kungiyar NUPENG ke shirin bin kungiyar kwadago itama ta yi yajin aiki

Siyasa
Kungiyar ma'aikatan man fetur ta NUPENG ta umarci membobinta da su shiga yajin aikin sai mama ta gani wanda za'a fara a gobe Litinin. Sakataren Kungiyar, Mr Afolabi Olawale ne ya bayyana haka inda yace kungiyar tasu zata bi umarnin yajin aikin. Kungiyoyin NLC da TUC dai sun bayyana aniyar shiga yajin aiki a gobe litinin wanda sai abinda hali yayi kan neman gwamnati ta kara mafi karancin Albashi. Wannan mataki na NUPENG dai zai iya jefa da yawa daga cikin 'yan Najeriya cikin matsalar wahalar man fetur.

Idan aka biya ma’aikata mafi karancin Albashin da suke nema na Naira N494,000 sauran mutanen Najeriya zasu shiga wahala>>Ministan Yada Labarai

Siyasa
Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana damuwa kan bukatar kungiyar NLC ta a biyasu mafi karancin Albashi na Naira N494,000. Ministan yace idan aka biya wannan mafi karancin Albashin da kungiyar NLC take nema, za'a rika kashe Naira N9.5 trillion wajan biyan Albashi. Ya kara da cewa kuma hakan zai jefa rayuwar sauran 'yan Najeriya miliyan 200 cikin wahala. A zama na karshe dai da aka yi tsakanin kungiyar ta Kwadago da Gwamnati an tsaya ne akan gwamnati zata biya Naira Dubu 60 a matsayin mafi karancin Albashi wanda kungiyar Kwadagon tace bata yadda ba. Hakan yasa kungiyar tace tunda dai ba'a cimma matsaya tsakaninta da gwamnati ba, zata shiga yajin aikin sai mama ta gani daga ranar Litinin dinnan me zuwa.
Hukumar Wutar lantarki ta Abuja zata yankewa hedikwatar Sojoji dana ‘yansanda wuta saboda bashi

Hukumar Wutar lantarki ta Abuja zata yankewa hedikwatar Sojoji dana ‘yansanda wuta saboda bashi

Siyasa
Hukumar wutar lantarki ta Abuja ta bayyana cewa, zata yankewa manyan ma'aikatu da yawa wuta saboda bashin kudin wutar da ake binsu. Ta bayyana cewa, daga cikin hukumin da ake bin bashin akwai hukumar sojojin, dana 'yansanda da ma'aikatar mata ta tarayya, da jihar Kogi, da ma'aikatar Ilimi, da ma'aikatar masana'antu. Hukumar tace ba wata ma'aikata da zata dagawa kafa zata yanke mata wuta. Hakan na kunshene a cikin sanarwar da hukumar wutar ta fitar.

YANZU-YANZU: Real Madrid Ta Ci Kofin Zakarun Turai Karo Na 15 Bayan Ta Yi Nasara Kan Dortmoumd Da Ci 2-0

Kwallon Kafa
Kungiyar Real Madrid ta lashe kofi na 15 bayan da ta doke Borussia Dortmund da ci 2-0 a wasan karshe da suka buga a filin wasa na Wembley. Dani Carvajal da Vinicius Jr ne suka ci kwallayen 2. Tsohon dan wasan Real Madrid din kuma kocinta, Zinedine Zidane ne ya kai kofin filin: Kungiyar Borussia Dortmund ta gayyaci Jurgen Klupp ya kalli wasansu. Shine dai ya kaisu wasan karshe na gasar da suka buga a shekarar 2013. Mahaifi da mahaifiyar Jude Bellingham da dan uwansa sun je kallon wasan. https://twitter.com/footballontnt/status/1796957357852832007?t=AfUBdCBVKdBJiz6B_0kChQ&s=19 Hakana mawakin Amurka Jay Z ma ya je kallon wasan: https://twitter.com/ChampionsLeague/status/1796973390743351387?t=l4Xncg675YAq4gnq5hRRRg&s=19 An samu wani da yayi kutse a ...
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya yi niyyar ɗaukar sojoji milyan ɗaya da ƴan sanda milyan ɗaya da a ce ya zama shugaban Najeriya a zaɓen 2023

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya yi niyyar ɗaukar sojoji milyan ɗaya da ƴan sanda milyan ɗaya da a ce ya zama shugaban Najeriya a zaɓen 2023

Kano, Rabiu Musa Kwankwaso
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ya yi niyyar ɗaukar sojoji milyan ɗaya da ƴan sanda milyan ɗaya da a ce ya zama shugaban Najeriya a zaɓen 2023 Ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar NNPP a zaɓén na 2023 da ya gabata, Engr Rabi'u Musa Kwankwaso ya furta hakan a hirarsa da BBC Hausa, ya ce wannan matakin zai inganta harkokin tsaron Najeriya da ya tabarbare a wasu sassan ƙasar. Wane fata zaku yi masa?
Mugunta ko cin Amana? Ji yanda shugaban wani kauye a jihar Katsina ya karbi cin hancin Naira dubu dari bakwai(700,000) ya amince aka kaiwa mutanen kauyensa hari har aka kash-she 30

Mugunta ko cin Amana? Ji yanda shugaban wani kauye a jihar Katsina ya karbi cin hancin Naira dubu dari bakwai(700,000) ya amince aka kaiwa mutanen kauyensa hari har aka kash-she 30

Katsina, Tsaro
Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Umar Dikko Radda ya bayyana yanda wani shugaban kauye ya karbi Naira dubu dari bakwai ya amince aka kai hari akan kauyenshi wanda yayi sanadiyyar kisan mutane 30. Gwamnan yace an samu hakanne a Guga dake Bakori. Ya kara da cewa ba zasu kyale ko wanene aka samu da hannu a harkar 'yan Bindigar ba. Saboda rayuwar mutanen jihar tafi ta mutum daya ko wanene shi.