Friday, December 5
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kan mu ya daure, Bamu san wanne hukunci zamu yi amfani dashi ba>>Hukumar ‘yansandan jihar Kano bayan da aka aika mata hukunce-hukuncen kotu har 5 da suka shafi masarautar Kano, saidai ta bayyana abinda zata yi nan gaba

Kan mu ya daure, Bamu san wanne hukunci zamu yi amfani dashi ba>>Hukumar ‘yansandan jihar Kano bayan da aka aika mata hukunce-hukuncen kotu har 5 da suka shafi masarautar Kano, saidai ta bayyana abinda zata yi nan gaba

Kano, Siyasa
Hukumar 'yansandan jihar Kano ta bayyana tsaka mai wuya da take ciki kan hukunce-hukuncen kotu har guda biyar da aka yi kan masarautar Kano. Kwamishinan 'yansandan jihar, Mr Usaini Gumel ne ya bayyanawa manema labarai hakan inda yace sun tattara duka wadannan hukunce-hukuncen 5 sun aikewa da shugaban 'yansanda na kasa yayin da shi kuma ya aikawa da ministan shari'a. Yace suna jiran ministan shari'ar ya gaya musu da wane hukunci zasu yi amfani. Yace da zarar sun samu umarni daga ministan shari'ar, zasu zartas da hukuncin da doka ta amince dashi. Yayi kira kan kafafen yada labarai da su rika tantance labari kamin su yadashi.
An gano Maniyyata na sayarwa da Takari Uniform dinsu a kudi me tsada a kasar Saudiyya

An gano Maniyyata na sayarwa da Takari Uniform dinsu a kudi me tsada a kasar Saudiyya

Hajjin Bana
Hukumar alhazan Najeriya, NAHCON ta gargadi maniyyatan kasar kan sayar wa wadanda ke zaune a Saudiyya domin neman kudi da aka fi sani da 'takari' tufafin da hukumar ta dinka musu domin gudanar da ayyukan hajjin. Daraktan Da'awah na hukumar ta NAHCON reshen jihar Kebbi, Sheikh Aminu Hassan ne ya bayyana haka lokacin da yake yi wa maniyyatan jhar jawabi bayan isarsu kasa mai tsarki. Akwai zarge-zargen cewa takarin na sayen tufafin wasu maniyyatan musamman mata da kudi masu yawan gaske, tare da yin bad da bami domin shiga cikinsu da fakewa da aikin hajjin wajen aikata abubuwan da ba su dace ba. Sheikh Aminu Hassan ya ce sayar da tufafin babban laifi ne da zai iya janyo wa duk wanda ya aikata hukunci mai tsanani, don haka ne ya gargadi maniyyatan su kauce wa wannan mummunar dabi'a. ...
An soki Peter Obi saboda kiran ‘yan Bindigar Arewa ‘yan Ta’dda amma yaki kiran ‘yan IPOB da ‘yan ta’adda

An soki Peter Obi saboda kiran ‘yan Bindigar Arewa ‘yan Ta’dda amma yaki kiran ‘yan IPOB da ‘yan ta’adda

Siyasa
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya yi Allah wadai da harin da 'yan IPOB suka kai da ya kashe sojoji 5 a jihar Abia. A baya dai, an yi tsammanin ba zai yi magana akan lamarin ba saidai yazo yayi maganar. Amma kuma ya kaucewa kiran 'yan IPOB din da 'yan ta'adda. Tsohon hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan inda ya dauko wani tsohon sakon na Peter Obi wanda yayi magana akan wani hari da aka kai jihar Filato inda ya kira maharan da sunan 'yan ta'adda. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1796877604475040183?t=ynvg3_I3Mpo8KjuxyO6U9w&s=19 A zamanin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne dai aka ayyana kungiyar ta IPOB dake ikirarin kafa kasar Biafra da sunan kungiyar ta'ddanci.
An kama yaro dan shekaru 13, da dan shekaru 18 da wani me shekaru 45 da yin Fyade a jihar Gombe

An kama yaro dan shekaru 13, da dan shekaru 18 da wani me shekaru 45 da yin Fyade a jihar Gombe

Tsaro
Jami'an 'yansanda a jihar Gombe sun kama wani karamin yaro dan shekaru 13 saboda yiwa yarinya me shekaru 8 fyade. Ya aikata laifinne a karamar hukumar Akko dake jihar ta Gombe. Hakanan an kama wani Usman Husseini dan shekaru 18 da kuma wani Mohammed Yaya shi kuma dan shekaru 45 da duka ake zargi da yin fyade a jihar. Kakakin 'yansandan jihar, ASP Buhari Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace yaron ya ja yarinyar zuwa wata hanya da ba kowa inda acanne ya zakke mata. Shi kuma Mohammed Yahya yawa yarinya me shekaru 10 fyadene a lokuta daban-daban inda wani lokacin yake bata Naira 100 wani lokacin kuma ya bata Naira 50. Shima ya fito ne daga Tumu karamar hukumar Akko. Yace ana bincike akan lamuran kuma za'a gurfanar da wadanda ake zargi a Kotu.
YANZU-YANZU: Babiana Ta Fitar Da Takardar Saki Ukkun Da Mìjinta Yayi Mata

YANZU-YANZU: Babiana Ta Fitar Da Takardar Saki Ukkun Da Mìjinta Yayi Mata

Auratayya, Nishadi
DAGA Shafin Dokin Karfe TV Jarumar Tik-Tok Hafsat Waziri, wadda aka fi sani da Babiana ta bayyana cewa mijinta ya sake ta saki uku dan haka, yanzu haka ba ta da aure kuma ta ga cewa bai kamata ta yi ta ɓoye-ɓoyen sakin da mijinta yayi mata ba gara ta fito ta shaidawa Duniya halin da take ciki. Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu takardar shaidar sakin wadda Babiana Waziri ta aiko mata inda a ciki aka bayyana cewa "Ni Muhammad Izzudden Eze na saki matata saki uku". An rubuta takardar ranar 11 ga watan 4 na shekarar 2024, kamar yadda kuke gani. Babiana ta kuma bayyana cewa "Na shiga bala'in rayuwa a dalilin aurensa da nayi, har asibitin mahaukata an kai ni a dalilin aure kuma har yanzu ban gama farfaɗowa ba". In ji ta. Daga nan ta ƙara da cewa "Mijina ba ya biya mun buƙatuna na rayuwa...
YANZU – YANZU: Matashin Malami mai da’awah, Mufti Yaks ya rasú

YANZU – YANZU: Matashin Malami mai da’awah, Mufti Yaks ya rasú

Ilimi
INNÁ LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UÑ YANZU - YANZU: Matashin Malami mai da’awah, Mufti Yaks ya rasú. Allah Ya yi wa matashin malamin nan Abdullateef Aliyu Maitaki, wanda aka fi sani da Mufti Yaks rásúwâ. Sheikh Isa Ali Pantami ne ya wallafa labarin rasúwar ta matashin malamin, wanda ya ke kwaikwayòn shararren malamin nan Mufti Menk, a shafinsa na Facèbook a yau Asabar da safe. Pantami, wanda ya baiyana kaɗuwar sa da rasúwar matashin malamin, wañda ya ke gabatar da wa’azuzzukañ sa da turanci ta kafafen sada zumunta, ya ce za a yi jana’izar sa da ƙarfe 10 na safe a layin Justice Maiyaki, Dutsén Kura Gwari, Minna, Jihar Neja. Marigayi Mufty Yaks sananne ne wajén da’awah (kira zuwa ga Musúlunci) a ciki da wajén Nájeriya. Mu na fatan Allah Ya karbi dukkanin aiyukansa na alk...
An bayyana sunayen sojojin da Kungiyar IPOB ta kashe

An bayyana sunayen sojojin da Kungiyar IPOB ta kashe

Tsaro
Hukumar Sojojin Najeriya ta bayyana sunayen sojoji 5 da ake zargin 'yan Kungiyar IPOB sun kashe. An kashe sojojinne a ranar Laraba a Obikabia dake jihar Abia. sunayen sojojin sune: • Sergeant Charles Ugochukwu (94NA/38/1467)• Sergeant Bala Abraham (03NA/53/1028)• Corporal Gideon Egwe(10NA/65/7085)• Corporal Ikpeama Ikechukwu (13NA/70/5483)• Corporal Augustine Emmanuel (13NA/70/6663) Hukumar sojojin Najeriya dai ta sha Alwashin daukar mataki me tsauri dan rama kisan sojojin nata.
‘Ɗaliban Najeriya sama da miliyan tara ne suka nemi bashin karatu’

‘Ɗaliban Najeriya sama da miliyan tara ne suka nemi bashin karatu’

Tsaro
Asusun bayar da bashin karatu na Najeriya (NELFUND) ya ce sama da ɗalibai miliyan 9.5 ne suka kai ziyara ofishinta dangane da bashin karatu da za a bai wa dalibai tun bayan buɗe shafin da za a cike takardar neman bashin karatun a ranar Juma’ar da ta gabata. Sama da ɗalibai 6,000 ne suka cike takardan neman bashin. Yayin da yake yi wa manema labarai karin haske a taron da aka shirya wa ɗaliban da suka cike takardan neman bashin a ranar Alhamis, shugaban asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce sama da kashi 90 cikin 100 na manyan makarantun gwamnatin tarayya sun mika bayanan dalibansu da cibiyoyi kusan biyar da suka rage. Ya kuma bayyana cewa nan da makwanni uku za a bude shafin neman bashin ga daliban da ke manyan makarantu na gwamnati domin su samu su iya cike takardun neman bashin karat...