Tsohon Daraktan Ayyuka na Kudi a Babban Bankin Najeriya (CBN), Ahmed Bello Umar, ya shaida wa babbar kotun Abuja da ke Maitama cewa ba a bi umarnin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na sake fasalin Naira ba.
Ya bayyana cewa takardar kudin Naira da aka sake gyarawa a karkashin tsohon Gwamna Godwin Emefiele sun sha bamban da bayanan da tsohon shugaban kasar ya amince da su.
Daga: Abbas Yakubu Yaura