
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya musanta rahotanni dake yawo cewa wai yace zai janye wa matashi yayi takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC.
Atiku ta bakin me magana da yawunsa, Paul Ibe yace wannan magana ba gaskiya bace.
Yace a hirar da yayi da BBC babu inda yace zai janyewa wani dan takara, yace abinda ya fada shine idan aka yi zaben fidda gwani kuma matashi yayi nasara a zaben zai goya masa baya.
Atiku yayi kira ga ‘yan Jarida su daina fassara labari ba yanda ya kamata ba.