Friday, December 5
Shadow

Ba gaskiya bane, Ban sha komai ba, Matukin jirgin saman Air Peace ya karyata binciken da yace ya sha miyagun Qayoyi da Giyya a lokacin da yake tuka mutane 103

Matukin jirgin saman air peeace ya musanta sakamakon da aka fitar wanda yace ya sha giya da miyagun kwayoyi a lokacin da jirgin saman da yake tukawa me dauke da mutane 103 yayi hadari.

Matukin a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV yace shi bai sha komai ba.

Yace sun san irin kudade masu yawa da suka kashe a makarantar horas da tukin jirgin sama, babu yadda za’a yi a rana daya su batawa kansu suna.

Yace Asibitin da aka kai jininsu aka yi gwajin hukumar jirgin sama bata amince da ingancinsa ba.

Jirgin dai yayi hadari ne ya sauka daga kan titinsa a filin jirgib sama na fatakwal duk da yake dai ba’a samu asarar rayuka ba

Karanta Wannan  Hoto: An kama janar din soja inda aka kulleshi a Abuja saboda karkatar da shinkafar tallafi da sayar da motocin aiki da janare na ofishinsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *