
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba ya tunanin tsayawa takara a zaɓen ƙasar na shekara ta 2027 ba.
Ya ce dawowarsa harkar siyasa kwanan nan “ba don neman muƙami ba ne, sai don tallafa wa shugabanci nagari a dukkan matakai”.
El-Rufai ya yi wannan bayani ne yayin wani taron siyasa a jihar Kaduna ranar Laraba.
“Asalin shirina bayan barin gwamna a 2023 shi ne na huta daga siyasa, amma abubuwan da suka faru kwanan nan ne suka tilasta min dawowa, ba don kaina ba, amma domin na bayar da goyon baya,” in ji El-Rufai.
El-Rufa’i ya ce “ni dai ba zan sake yin gwamna ba, ba na so na je senate (Majalisar Dattijai), ba na wata takara”.
Ya kuma yi kakkausar suka ga gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu, inda ya ce ta gaza.
Nasir El-Rufa’i na cikin manyan ƴan siyasar Najeriya da suka yanke shawarar kafa hadakar ƴan adawa domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar a zaɓen ƙasar na 2027.
Tsohon gwamnan na daga cikin wadanda suka mara wa APC baya a zaɓen 2023 da ya gabata, lokacin da shugaba Bola Tinubu ya yi nasara, sai dai ɗan siyasar ya raba gari da jam’iyyar watanni bayan hawan Tinubu kan mulki, inda ya koma jam’iyyar SDP.
Daga baya kuma ya bayyana cewa zai kasance cikin jam’iyyar ADC wadda a yanzu haka ƴan adawar ke amfani da ita a matsayin lemarsu