“Ba na yin TikTok” — Natasha ta karyata bidiyon da aka nuna ta na rawar waƙar Rarara ta ‘Omo Ologo’

Natasha Akpoti-Uduaghan, sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, ta nesanta kanta da wani faifen bidiyo da ya karade shafin TikTok wanda ke nuna ta a cikin wani yanayi na raha ta na rawar wata waka da Rarara ya yi wa Shugaba Bola Tinubu mai taken Komo Ologo.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X , sanatar ta bayyana cewa ba ta da wani shafi a TikTok.
“Ba ni da shafin TikTok,” in ji sanatar.
“Akwai wasu shafukan bogi da dama da ke amfani da sunana a X (Twitter), Instagram, Facebook da TikTok. Wasu daga cikinsu sun tara mabiya masu yawa.”
Ta ce bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta an yi shi ne ta amfani da wani tsohon bidiyo daga shekarar 2023 tare da nufin yaudara.
Natasha ta yi bayanin cewa an yi amfani da wata bidiyo da ta yi rawa a 2023, aka haɗa wannan faifen da ya karade shafukan sada zumunta.